The Family

1.5K 171 23
                                    


https://www.wattpad.com/1011360729?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=mMrIqcxdapq%2FSE7USZjGsb%2FFB1MBG%2Fu4vRbhIbJT5ilQsppeHl47%2FrAaYr311ST49cjr6g20uEIISILnMabOLa4cfYyXh4JH%2F5zPAmCw7u06ldoVSzISbMMN%2FFR4QX8x

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣8️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

        Cikin tsananin tausayi ya kalli Driven, ya shiga gaban motar driven zai magana ya mishi wani irin kallo, dole yayi shiru ya dawo gefen shi, da gudu ya nufi Dr Abdullahi keluarga Memorial hospital.  Kamar zai tashi sama, jin yadda take kananun magana tana kuma tab'a shirmen, Allah kadai ya kai su Asibiti.

                        Allah ya kai su asibitin cikin ikon shi, yana shiga ko parking me kyau bai yi ba, driven ya rigashi fita, tare da kiran a kawo abin daukar mara lafiya.

   Sanin waye yake maganar yasa duk kusan nurse din asibitin suka shiga gaggawan kawo gadon, sabida sanin darajar driven a gurin masu asibitin, duk wanda yake aiki da Familyn Dr Abdullahi keluarga toh ko a cikin gari ne haka zaka samu yana da daraja, sakamakon familyn sun kasance mutane masu zuciyar zinari, masu taimakon na kasa dasu.

      Basu dauki duniya da fadi ba, shi yasa duk wani gwamnati idan aka kafa shi toh sai ya janyo daya daga cikin gidan yayi tafiya da shi.

         Dan haka driven ma ganin ake mishi kamar jinin gidan ne shima, da sauri suka fito da gadon, lokacin yafito da ita a hannun shi yana tafiya irinta asalin jarumai,  kwantar da ita yayi yana kallon Dr Habib.

        "Faruq!"
"Please! Bana son damuwa!" Zurawa gadon da Noorh ido yayi, cikin damuwa da jin wani irin motsi da ran shi yake, wani irin yaja, tare da jin zuciyar shi yana bugawa da sauri da sauri, dauke kai yayi daga kallonta.

     "Ka kira min Ita!"
Wani juya ido Habib yayi sannan yace.
"Wacce kenan?"
Zaro idanu Faruq yayi cikin takaici, sannan ya dauke kan shi tare da juyawa ya bar gurin, yana jin dariyar mugunta da Habib yake Mishi,

Ya fahimci Naaz yake nufi, dake takan shigo asibitin aikin gaggawa.

    Kiranta yayi tare da gaya mata, tazo ana nimanta, sannan ya koma kan Noorh da ake duba,

    Nufar Office din Dr Raliyah yayi,.Yayar shi ce, yana shiga ya gansu tsaye da mijinta suna soyewa ya juyo da sauri, dariya tayi sannan tace.
"Ruq! Ka shigo yanzun Baby zai koma gida"
Buge mata hannu Mijin yayi shima likita ne,.yace mata.
"Liyah! Yau zanje duba Nanah da da daren nan ciwon kafa na damunta."
"Kace mata ta rage shan coffee."
Jan kumatunta  yayi sannan ya sumbaci goshin ta, ya fita.
Gaisawa suka yi da Faruq, sannan ya shigo Office din ta.
"Liyah!"
"Ruq!"
"Liyah!"
"Ruq!"
"I found my heart!"
"Kamar ya?"
"Wallahi daga ganinta nake jin bugun zuciyata ya nunku!"
"Kai Ruq!"
Tayi maganar tana zaro ido, zama yayi tare da mika kafar shi saman table din ta.
"Raliyah, Wallahi ita nake so! Zan iya rushe wancan tsohuwar al'adar auren zumuntan nan domin yarinyar tayi min!"

"Faruq kai da aka maka baiko da Naaz!"
Kamar wani shine zama da ita ya mike kamar zai buge ta,
"Ba zan yi auren zumunta ba! Nace miki Yanzun na tsinci abinda Zuciyata ta jima tana nima Ni bana son Naaz yarinyar bata min ba, dan haka karki dame ni da wata naaz"

     Sake baki tayi sake tana kallon shi.
"Amma kasan Nana da Dadah sun gama magana, yanzun ka bijiro da wata shirme, sannan ita wacce kake so yar uban waye!"
Dafe goshin sa yayi tare da lumshe idanun shi, sannan yace.
"Bugeta muka yi."
"Ruq! Dama daga muje na ganta."
Ta fito a fusace, a bakin kofar suka gamu da Naaz da idanunta yayi jajjur, cikin fushi ta juya fuuuuu.
"Wallahi kika bar asibitin nan baki duba min mara lafiya na ba, sai na baki mamaki a dare nan."
Cak ta tsaya, sannan ta juya tana kallon shi, cikin wani irin takaici.
"Kai waye? Ce maka aka yi ina son wannan yanayin naka ne?

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now