Mine

1.9K 223 36
                                    

https://my.w.tt/VtYbk6o8Ecb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣3️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

"Wannan kuma matsalarka ce, itama Adeemah zanci zarafin ta, idan na shiga cikin gidan, wallahi idan baka fita hanyar kanwata ba, zan baka mamaki banza kawai wanda kazamtar shi bai tsaya a iya shi ba."

    Nan Mahir ya sille shi sannan ya bar gurin, duk da ya razana amma dan kar ya nuna cewa ya razana sai ya bi Mahir da harara.  Shi kuwa Mahir da ya shiga cikin gidan sai ya rasa me zai mata ya huce bakin cikin da ya gani dan haka ba tare da cewa kome ba, ya riko hannun da ya gani akan cinyar Nazzir.

     Murdewa yayi baya, sai da ta sake fitsari a jikinta.
"Na kuma ganin ki a cikin gidan su Nazzir ki kuma na ganki da shi sai na ɓalle hannunki mara mutunci kawai."

Cillata yayi ta fadi, kallon Ummi yayi cikin baƙin ciki ya juya zai fita cikin tsawa yace mata.
"Kar na dawo baki gyara gidan ba! Daga yau ita zata cigaba da aikin gidan ta tunda tasan daura hannunta akan cinyar namiji."

               Kallon shi Ummi da Hajiya suka yi, sannan suka ce.
"Da haka ba gwara idan tana da wanda yake sonta ya fito ai mata aure ba,"
        "Ita tasani gata nan dai." Ya fadi haka, bayan ya bar falon. Tsabar tashin hankali, a ranar kasa barci yayi, yana hango Abinda aka soyiwa Noorh da wanda Nazzir yayiwa Deemah, gani yake da zaran ya bar kasar Nazzir zai samu damar lalata mishi tarbiyyar kanwar shi.

      Dan haka, washi gari hana Haroon aiki yayi, ya nufi gidan Ummi ya karya sannan ya turawa haroon sakon yayi mishi abinci sai fita da shi.
Kallon juna suka Mahir da Ummi,
"Hmm! Sai kumbiya kumbiya kake min meye nufinka?"
      "Hmm! Ke bani wayar ki, da laptop din ki."

    Babu musu ta dauko kome ta bashi, sannan ya kalli Ummi yace mata.
"Hmm ina son zanyi tafiya!"
"Ina zaka?"
"Canada!"
"Allah ya tsare kuma a kiyayye tab'a yar wasu domin kar haka ya faru akan na ka"

     "Insha Allah" ya faɗa a takaice,
   Mikewa yayi ya bar gidan ya nufi gidan shi ya dauki abincin ta, tunda ya isa cikin asibitin yaga yadda mutane suke bin shi da ido, ya fahimci akwai matsala. Yana nufar hanyar da zai kai shi ya samu anata kiciniyar kaita d'akin ta, taki sai dambe suke da nurses, yana isa gurin ya mikawa wata nurse basket din abincin yazo ya rikota, d'ago kai tayi sannan ta fashe da kuka tare da fadawa kirjin shi, lumshe idanun shi yayi tare da rufa hannun shi a bayanta.
"Don Allah Sir idan mun daureta karka kunceta."
Dakin ya nufa da ita, yana shiga ya rufe kofar ya ajiye ta a bakin gadon. Juyawa yayi ya bude kofar ya karbi abincin sannan yazo ya ajiye shi daukar brush da maclean yayi ya saka mata, sannan ya riko hannunta suka shiga ban daki, karshe dai ta shanye maclean din.

        Brush kuwa karya shi tayi zata taune ya matse bakinta sai da ya fitar, sannan ya koma ya dauko wani ya kuma, lakata mata dakyar ya wanke mata baki da idanunta suka fito, zama yayi da ita ya zuba mata.
      A hankali yake ci yana hura mata iska, tare da bata a bakinta tana ci hankalinta yana kan kofar dakin da take ganin wucewar mutane ta kasa, can sai ta rufe idanunta, sai da ya lura da haka ya mai da ita tana kallon kofar shi yana zaune a inda take.

        Yasan bata cewa bata san koshi ba, dan haka ya shiga bata dai dai tare da kai hannun shi cikin ta, jin ya d'an taso ya ajiye abincin ai kuwa ta fara ihu, haka ya bata tayi mugun koshi, sannan ya dauke abincin.

         Kwanciya tayi a kafar shi, yana shafa kanta, a hankali yana wasa da gashin kanta,  sannun sannu yaji ya kama barci, gyara mata kwanciya yayi sannan ya kuma gyara mata gashin kanta, yana kallon yadda take b'ata fuska, tana numfashi dai-dai kamar wacce ta dauki kaya.

             ••• idan akwai abinda yake ɗaukar hankalin shi, toh surar Jikinta ne, tana da zubin halittar da yake son matar shi da ita, tana da cikar kamala a fiskarta, kallon shedar sallar goshinta yayi, yayi tare da sake murmushin jin dadi, duk yadda aka yi ma'abociyar ibada ce.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now