Injured

1.9K 178 22
                                    


https://my.w.tt/RJDRFmzqxcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣0️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

      Noorh kina ja mana zagi 🤨🙄🤣 Yacin 🙈
Sakon godiya gare ku, Team Tasleem da Noorh! Ko nace Team Mahir da Nazzir.

*
"Idan kika tafi can babu matsalar kome?" Ya tambaye ta,
"Eh babu abinda zai faru!"
"Are you sure?"
"Hmm!"
Yana tambayarta tare da fita da gudu a cikin dajin, gudun awa biyu da rabi ya fito dashi bakin hanyar da ya ajiye motar shi, yana fitowa, ya isa tare da ciro key din da yake aljuhun wandon shi ta ciki, yana bude motar ya samu wayar shi tana haske, duba kiran yayi 75 miss call. Kashe wayar yayi dan yaga har da wasu Number da bai sani ba.
Kallon Noorh tayi tana lumshe idanun ta,  sake baƙin ta yawu na zuba wani irin ɗaukewa numfashi yayi, tabbas mahaukacin kare ne ya cije ta, dan ga alamar ya nuna, domin kwayar cutar ta har tabi jininta.

            Rufe motar yayi da karfi ta bude idanunta, tare da wani gurnani, tana kokarin neman hanyar da zata fito ta cije shi. Bude mata kofar yayi, ta fito da gudu. Kafin ta gama fitowa ya matse mata kafarta, ihu tayi me hade da haushin kare, sake bude kofar yayi ta fito da gudu, bude hannu yayi, ta shiga jikinshi tana kokarin cizon shi, dokin wuyar ta ya tab'a ta koma jikin shi ta kwanta, alamar ta suma.   Sakata yayi cikin motar sannan ta daure hannunta tam, tare da jan siririn hancinta yana faɗin.
"Zombia!"
Shigar motar yayi tare da bashi wuta, bai tsaya ba sai Estate din shi, ya shiga cikin gidan ya hada kome tare da ɗaukar motar shi, ya mai da ita ciki, sannan ya koma dakin shi ya dauko wata wayar shi ya kira Ummin shi ya shaida mata yana hanyar zuwa.

       Bayan nan ya kira likitan su na family ya gaya mishi, tare da cewa yana tare da mara lafiya, yana tunanin cutar haukar kare ne ya same ta sakamakon cizon kare, yana gamawa ya kira Captain Nuhu ya gaya mishi a fara shiri gashi nan zuwa.

        Yana gamawa ya kira wali, cikin gaggawa ya tura sakon, sanarwar ya sami Noorh, amma yanzun haka tana hanyar komawarta Jos gidan marayu, sannan ya nufi airport, cikin minti talatin da biyu, ya isa tare da Wali, mika mishi key din motar mutumin yayi da kudi masu yawa, ya bashi akan ya bawa driven, sannan ya kuma rike shima, idan akwai matsala ya kira shi. Zai koma Lagos akan lokaci ne.

       Daukar Noorh yayi wali kuma ya dauki kayan su, ya bi bayan su, zuwa cikin privet jet din shi. Ya saka musu kayan sannan yayi musu  sallama, shi kuma ya gyara zaman kayan, sannan ya zauna yana kallon yadda take kwance, kafarta yayi green, fuskarta a kumbure, a hankali ya kwantar da kanshi bayan ya makala belt, yana sauke ajiyar zuciya. Dan yasan tayi musu nisa, kuma zai yi wuyar su same ta.

        Karfe takwas na safe, suka sauka a babbar tashar jirgin sama na lagos, motar asibiti ya fara cin karo dashi, ita aka kasa a cikin motar suka tafi da ita, shi kuma motar gidan su, da suka zo daukar shi ya shiga, suka wuce gida kiran Likitan yayi tare da zabga mishi kashedin kar ya kuskura ya bari Ummi ta sani, domin zasu iya mishi caa.

    Tunda ya isa gidan, Ummi da kanta ta gyara mishi dakin shi, dan tasan shi da shegen kyamkyami, bayan ya gama wanka ya shirya cikin wata farar shadda, a hankali yake saukowa hannun shi daya cikin aljuhun wandon shi, dake rigar haf jamfa ne, kwantaccen sajen shi ya karawa amintacciyar fuskarshi kyau. Yana zaune akan table juya abincin yake, tare da sunkuyar da kanshi kan Abincin.
"Wasu yan bindiga da dad'i sun farmaki motar da suke zargin A'isha Omar Jimeta take ciki, bayan sun bankawa motar wuta, hakan ya faru ne sakamakon sake sanarwan da matashin Attajirin nan MAHIR Hamoud Boualem, mamallakin sharararren kamfanin Hamoud Boualem Company. Wanda ya sake sanarwar Noorh tana hanyarta ta zuwa garin Jos."
"Shbah off the tv!"
Ba musu ta kashe, sannan suka kafe shi da idanu, cin abincin shi yake a tsanake, amma abina yake jira kenan, tabbas yanzun ya kuma yarda da tsarin shi, nacewa Noorh tana hanyar Jos, da ashe ya barta ta tafi toh tabbas da itace zaa kona.  Bai kuma bin takan su ba, dan yasan ana bibiyar shi amma bai kai yadda yake tsammani ba.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now