Farko .

6.4K 324 12
                                    

GARIN KADUNA.

Acikin wani ƙaton hall da zai ɗauki mutane ɗari biyu, hall in ya sha kayan kwalliya na golden and black wacce glamhall decoration ne tai decorating, hall in cike yake maƙil da mutane kowa a wajen are in their best attires.

Ba amaryar ba, ba enmatan ta ba, ba kuma guests in ba. Na raɓu a gefe guda in na kallon yanda ake gudanar da sha'anin da na gane ashe dinner ce. Ankai awa biyu da rabi ana annashuwa da raha, sai kawai naji hall duk anyi shiru.

Abin mamaki ne ace hall din da ake dinner shine yayi tsit haka, banyi ƙasa a gwaiwa ba sai da na ɗaga idanuna don inga abin da ke faruwa, ananne idanuna suka gano min wata mace yar kimanin shekara ashirin zuwa ashirin da ɗaya, ita ba doguwa ba ita ba gajera ba za mu iya kiran ta da tsaka- tsaki, ta sha adon doguwar riga kalar ja, wadda ta fito da tsarin kyaun jikin ta mai kama da shape in coca cola bottle, watau figure eight kenan a turance.

Farace amma ba farin nan da yawa ba, farin ta mai kyau ne irin farin yan ethopia, tana dauke da manya- manyan idanuwa masu kama da na mage, da ɗan siririn hanci madaidaici, saikum leɓen ta wanda ya sha nude lipstick mai shigen kama da na bratz. Tana da yalwan gashin gira da yayi kamar tana gyarashi dan tsabar curving din da yayi.

Taku take ɗaya bayan ɗaya kamar wadda aka ce a runway take, da haka take takunan nata mai daukar hankalin mutane har ta isa wajen host in, magana tayi mishi wanda ni kaina ban ji mai tace ba, tare da miƙa mishi wani baƙin ƙaramin device a hunninshi, kawai sai gani nayi ya sakar mata mc din a hannunta.

Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta buga akan speakern dan ta ga ko yana aiki. Illai kuwa sai ta ji ƙaran bugun da tayi. Murmushi ta ƙara sakar wa mutanen da duk ita suke kallo, da mamaki a idanuwansu, kafin ta buɗe baki tafara magana kamar haka.

" Assalamu alaikum " sai ta ɗan dakata kaɗan don su amsa mata, ba laifi wasu sun amsa mata wasu kuma sunyi ƙum da bakin su.

" dama na zo ne don na nuna farinciki na game da taya abokin mu, kaninmu da yayen mu Salim murna " tace yayin da take kallon angon wanda tun tahowarta stage yake warwara ido kamar baƙin munafuki, gashi yanda zufa yake ta keto masa, zaka zata ba ac a wajen.

Kau da idanunshi yayi kafin su hadu da nata. " amma kuma abin da ya sosa min rai game da wannan abin shine ni nafi chanchanta da a kira in zo in bada tarihin wanan bawan Allah. " ta ƙara dan dakatawa yayin da ta runsunar da kanta kamar mai wani tunani, sai kuma ta k'ara daga kanta ta kalle mutanen da duk suke yi mata kallon mahaukaciya wadda batasan abin da take ba.

Budar bakin ta ne sai tace. " duk da dai an kira abokin ango yayi nasa bayanin barin in ɗan baku tak'aitaccen nawa ".

" amarya Salima " tace tana kallon amaryar da tace kwalliya a cikin doguwar riga kalar ja itama, sai dai na amaryar bai kai na wannan budurwar kyau da tsaruwa ba, dan inbaka san wacce amaryar ba sai kazata itace.

Salima wacce tun da yarinyar tafara magana ta ke ta faman bankamata harara, taja wani ɗan tsaki game da sake sakarmata wani hararan.

Afra , yarinyar da ta ke kan stage in ta murmusa kafin tace ." ina taya ki murnar auran munafukin namiji, azzalume wanda bai san darajar mutane ba, ina kuma ƙara tayaki murnar samun daƙiƙin na namiji wanda ban da wata shakka ƙarshen sa bazai yi kyau ba, kuma ki kasa kunan ki kiji mijinko mayaudari ne, me bin mata ne kuma zan iya rantse miki fasiƙi ne "

Ta idda maganar yayin da kowa yake sallallami, mutanen da suke jinjin maganar da wa'inda suke ƙaryata ta duk suka cika hall in da surutu, wasu ma har tsine mata suke yi, itako ko ajikin ta, sai laulausar murmushi take sakar musu yayin da tunani kala kalar suka cika mata kwakwalwa.

 AFRA Where stories live. Discover now