Babi na Hamsin da Daya.

1K 129 1
                                    

Sanye take cikin full covered swimming body suit wanda ake kira da burkini,  kalar baki ta saka, kanta kuma rufe yake da hular kayan. Zaune take gaban private swimming pool in da ke suit in su. Jiya suka iso Maldives, don haka ba abinda suka tsinana illa baccin gajiya, yau ma dai hakan take domin basuda niyar fita. Yanzu ma gajiya da yin bacci ne yasata fito wa wajan swimming pool ta baro Omar a daki. Kafafunta ta sanya cikin ruwan Wanda ba laifi yana da dan dumi domin ko garin ba wai sanyi ake  ba, yatsun kafarta take Wasa da su a cikin ruwan tana jin kamar ta shiga ciki tayi swimming amma kuma sai dai ba wai iyawa tayi ba.

Ta dade a haka tana kallon horizon in dake daukan ido, da yanda kallar garin yayi lokacin da ranar take faduwa, such a pictureque view ta fada a zuciyar ta silently tana yi wa Allah kirari da yabo. Bata san ma har rana ta fada ba sai ta taji Omar na kiranta. Juyawa tayi ta ganshi tsaye sanye yake cikin grey sweat pants yayi pearing da wata black tshirt.

" me kike a nan ke dai kin san baki iya swimming ba " ya fada with concern etched on his face.

Dan murmushi take tareda cire kafafunta daga cikin ruwa. "don ban iya swimming ba, ba yana nufi ina tsoron ruwa bane". Ta bashi amsa.

Dan jin jina kanshi yayi, tareda gesturing mata da hannunshi ta je wajan shi. Takawa take a hankali domin ta barin swimming pool in akwai santsi kartaje a garin tafiya santsi ya kwashe ta ta fada ciki. Tana isa inda yake ya saka hannun shi around waist inta tareda janyo ta jikinshi.

" I have missed you, shine kike fita kika barni ni kadai " fada yana me dan sausautar muryarshi da ko da da mutane ba Wanda za su jishi ila ita dake Kusa da shi.

" hmm " ta furta domin ta rasa amsar da zata bashi, domin tsareta yayi da wa'enan mayun idon nashi Wanda ita ta ma kasa kallo sai maida kallonta tayi kan kirjinshi inda hannunta ke resting a kai.

" kinsan me " ya kara mata whispering a kune, Wanda take jin dumin numfashin shi a ta wuyanta ya sa mata goose bumps, duka kananan gashin da ke jikinta sai da suka tashi.

Still bakinshi na gefan kunen ta ya karasa furta abinda da yayi niya duk da ba wai ta ma yi wani kwakwaran motsi da zai nuna tana jinshi bane amma kuma ya san tana jin nashi.

" zaki iya tuna lokacin da nace ina so ki ban babies "

Wannan zancen dayayi yasa ta kai iduninta kan shi taga ashe shima idon nashi na kanta. Bude bakin ta tayi duk da taji lebanta na mata nauyi amma haka ta furta kalaman da ke cikin bakinta.  

" ba na ce ma in ana siyansu zan siyar ma ba ".

Kallonta yayi na yan sakoni yana juya maganan ta a kwakwalwarshi, wai sarcasm take fada mishi ko kuma ita tsakaninta da Allah take magana don shi fa ba wai yana gane mood in magananta bane, in ma bakar maganace ba gane wa zai yi ba.

Dora hannunshi yayi akan kumatunta yana using thumb in shi yana caressing smooth cheek inta.

" ba na siya nake so ba, ki nake so ki ba ni "  ya fada, yayi dan shiru na wucen gadi kafin ya sa hannun shi ya shafi shafafan cikinta.   

" ina so ya zauna anan ne " ya karasa bayanin nashi. Wani dum taji na yan sakoni, kafin kuma taji wani kunya ya lullube ta, wato shi dai wanan baro baro yake son mata, daman tun farko da yayi maganar ba wai bata gane bane kawai dai so tayi ta kau da zancan.

Ganin batada abinda zata fada ma, sai ta dan lumshe idonun ta still tana jin yanda yake kallonta, kafin wasu dan sakoni ta bude shi tareda ba shi amsarta.

" toh Allah ya kawo masu albarka ". Wani murmushi yayi Wanda shi kadai yasan ma'anar shi, jin kiran Sallah maghrib da wayarshi tafarayi yasa ya sake ta domin su je suyi sallah. Bayan su idar da maghrib ne ya kira room service domin su kawo musu abinci, ba a wani dau lokacin ba suka kawo mishi, aikam Afra tace domin dama bata ci abincin rana ba domin duk gajiya ma bata barta ta ci ba, sai da suka cika cikinsu kafin su kira a zo a dauke, ita Afra ta shiga bathroom domin tayi wanka tareda daura alwala domin lokacin isha yayi, bayan ta fito ne Omar ya shiga.

Tada sallah tayi ta fara gabatar da nafila kafin ta yi na Isha sai kuma ta zo ta hada da shaf'i wal witr, shi ma haka Omar in yayi tana shirin tashi daga abin sallah Omar yayi magana.

" karki tashi, yakamata muyi sallah Nafila na godewa Allah ko "

Bata kawo komai a maganar shi ba don haka sai ta bishi ya jasu sallah domin tana ganin kamar rama nafila da ya kamata suyi tun ranar auran su ne sukeyi yana. Suna idar yayi yayi musu addu'o'i kafin ya dafan kanta yayi mata addua. Nan ma dai ba wai ta kawo komai bane domin zuwa tayi ta canza kayanta zuwa na barci, wata silk Riga da ta tsaya mata iya waist in ta da wani kajeran wando da ya kusan kai knee in ta. Sai da ta feshu jikinta da turaren kafin ta cire abinda ta kama gashinta da shi domin gashin nata ya sa iska. Fitowa tayi daga cikin bathroom ta ganshi zaune a kan gado yana me latsa wayar shi.

Sanye yake cikin wani dogon wando na kayan bacci shi ma silk ne kuma dai daga gani ma duk company dayane da na jikinta domin color in su daya, amma shi kuma ba saka rigan ba, kawai dai yanda ya saba kwana ba Riga a jikin nashi hakan yau ma yake. Jin motsin kulle kofarta ne ya sashi kai hankalinsa kanta gani yayi ta tafi barin da take kwanciya, sai da ta karkade gadon kafin ta kwanta akai tana me shirin bacci.

" ya maganar mu " jin maganar shi ce ta sata fasa kwanciyar da zata, tana me kallonshi da mamaki, itafa har ga Allah ta wani manta da wata magana da sukayi, sabida ita maganar dazu ba wai ta sata a cikin ranta bane domin a wajan da ya gama surutunshi a wajan ita ma ta yarda maganganun nashi.

" wace maganar kenan " ta tambaye shi.

Kallonta yayi domin gano gaskiyar ta ganin da gaske take batasan abinda yake nufi ba ya sa shi tasowa daga inda yake ya tako har zuwa inda take zaune, zama shima yayi a Kusa da ita, ya yan juya tareda jawota jikinshi. Bayanta yana mai jone da kirjin shi. Abun kamar Wasa taji ya fara mata wasu abubuwa tun tana dauka karamin abu ne taji ya fara wuce gona da irin, tuni ta fara kuka tana me ne man kwace kanta daga wajan shi, amma cikin lalima da kwantar da kai har sai da Omar ya sami abinda ya ke neman a daran rana. Aikam tasha addu'o'i daga wajan mijinata, ya shimata albarka ba adadi, kamar yanda tajiyar da shi a daran ranar haka shima yayi wa kanshi alkawarin zama nata na har abada, wannan alkawarin ba wai furtashi yayi ba, A'a a cikin zuciyarshi ne ya daukawar wa kanshi hakan. Asuba ta gari....

______________________________________
Seems like yau Omar in mu ya angonce, ahhhh at last.

Okay vote, comment and share..

Not edited.

 AFRA Where stories live. Discover now