Babi na talatin.

1K 125 1
                                    

Tsaye take gaban floor length mirrorn dake makale da jikin bangon dakinta. Sanye take cikin wani black high  waist pants da ya matse daga cikin ta har zuwa cinyoyinta kafin ya bude, sai wata nude loose lacy crop top mai dan siririn hannu, pairing in shi tayi da black lacy full length jacket with slim sleeves, jacket in abude yake ta gaba don haka ana ganin kayan ciki amma kuma a suturce take domin ko ya boye shape in ta. Ta yane kanta da wani nude veil.

Heavy smooky makeup tayi Wanda ya kara fito da manyan idanunta, tareda da glossy lip stick colour brown. Highlight inta is blinding cause ko daga nesa mutum yake yana iya gani. Kafarta sanye take da wani nude coloured valentino stiletto heel, tayi pairing in shi kuma da jakar chanel shima kalar nude in.

Tayi kyau ainun, ga kuma jikinta yana fitar da wani sihirtaccen kamshi amma sai ka matso dab da itama mutum yake jinshi. Wayarta ta dauka, kirar iphone 11 pro max. Tafara daukan vogue worthy pictures. Hakalinta kwata kwata ya tafi wurin daukan pictures, domin ko bata yi tsamani ba sai ji tayi an rugume ta tabaya.

A dan tsorace ta dago idonta taga ashe Omar ne, ita abin ya bata mamaki ma tayanda ya shigo bata ma ji shi ba. Kallonshi tayi taga ya canza zuwa wasu Italian made two pieces suit kalan baki, sosai kayan ya amshe shi domin ya zauna a kan kirar shi wacce ke kamada na yan ball kokuma dai masu yin gym. Kamshin turaren shine na tom ford ya mamaye hancin ta. Intace bata son kamshin turaransa tayi karya domin turaren ya hadu ne irin sosai in nan.

" it's rude to stare you know " ya fada tareda hura mata iska a ido.

Kifta idonta tayi tana mai jin kunyar kamata dayayi tana kallonshi, amma kuma in her defense it was a harmless  scrutiny.

" I wasn't staring at you, I was scrutinizing you inga ko akwai inda zaka gyara. " tace mishi tana mai dan daure fuskar ta.

Dan murmushi yayi tareda daga giranshi daya yace.

" Allah ko, toh babu abin gyara ko matar Omar " ya fara juyawa a hankali domin taga full shigar ta shi.

Basarar da zancen nashi tayi tareda cewa.

" let's take picture "

Komawa yayi tareda sakale hannu akan waist inta, ita kuma ta dan yi leaning a jikinshi kadan, kafin tafara dauka su pictures, bayan mirror picture in kuma ta koma daukan selfies, daga selfies ne kuma taba shi yafara daukan pictures in ta. Har sai da ya fara gajiya da daukan pictures kafin ta karbi wayanta baya.

Fita sukayi daga cikin gidan tana mai duba pictures in da ya dauka da Wanda ta dauke su, pictures in ba karya sunyi kyau sosai. Turawa Abida tayi picturen ta Wanda take ita daya da Wanda ta dauka da Omar, domin ta ma Abida alqawarin tura mata pictures in suyi. Dazu sukayi waya lokacin tana shiryawa shine take ce ma Abida zasu fita, shine fa sai da Abida ta sata yin alqawarin daukar picture tareda Omar kuma ta turo mata.

Itama ganin mirror pic in nasu yayi kyau sai ta saka a what's app status tareda caption in out and about, a Instagram inta kuma, daman private ce, kuma sai wanda ta sani take accepting don haka nan ma sai da ta saka picture tareda da caption in outing with mijin. Tareda saka heart heart a gaban caption in nata.

Aikam kamar jira suke tasaka ta fara samun likes, da comments. Daman tunda tayi aure batayi musu posting ba, aikam daga masu cewa awwwn da hoton heart agaba, sai masu yi musu addu'a, sai kuma masu cewa sunyi kyau tare da dai sauransu.

" good evening ma'am ". Gaisuwan da tajine ta gefanta ya bata daman dauke kanta daga screen in wayanta. Sam ta gani tareda Sidi wa'enda daman taredasu suka taho.

" evening how are you"  tace musu tana mai musu murmushi.

" we are fine ma'am " suka amsa suma da murmushin a fuskar su. Bude mata kofar baya Sam yayi ta shiga kafin ya rufe, ita duk a zaton ta ma Omar na motan amma sai taga ita kadai ce aciki. Toh ina ya shiga shine tunanin da ke ranta.

 AFRA Where stories live. Discover now