Babi na Talatin da Tara

958 126 6
                                    

Sai dariya su Sam suketa turka a cikin mota domin ko acting level in su was superb. Su ba ma abinda ya basu mamaki kamar yanda Omar yayi acting as if da gasken haka abin yake.
Shima Omar abin ya dan bashi dariya, amma yarinyar ta ba shi tausayi, kwata kwata bata fi si'ar su Abida ba amma rayuwarta take a haka, addu'ar shiriya yayi mata domin yasan shi kadai take nema.

" Sir yanzu wajan warehouse in zamu  ko " Sidi ya tambaya.

Kallon side mirror Omar yayi yaga masu machine in nan dai suna trailing in su. Maida kallonshi yayi ta windshield  tareda cewa.

" muje ware house in, nasan ai yanzu su Abdul suna wurin ".

Abdul yana daga cikin masu aiki a ICPC daman tuntuni sukayi planning wannan abun domin ma ICPC ne sukayi renting wajan da sunan da Omar yayi amfani dashi wa Zeena, a zuman warehouse in nashi ne. Duk wannan na cikin strategy in su.

Jin jina kanshi Sidi yayi kafin ya karya wheel in motar zuwa inda warehouse in yake. Tafiya ce mai dan nisa amma duk da haka masu machine in nan na trailing in su. Suna zuwa suka ga anyi rubutu a jikin warehouse da ja tareda saka raided by ICPC. fita sukayi daga motar, suka je gaban wajan, akwai yan mutane amma ba da waya ba yawancin su ma masu uniform ne amma kuma sukayi shigar farar hula suna jira a wajan. Masu machine in ma suna karasowa wajen abin mamaki ko kuma ince tsautsayi instead of su wuce sai suka tsaya aikam daman kamar jira ake suna sauka wasu daga cikin police men in nan suka zagaye su. Ko kamin su suyi wani yunkuri an riga da an samusu ankwai a hannu.

" you are under arrest by the dss, you have the right to remain silent because what you say will be used against you in the court of law " daya daga cikin yan sandan ya fada musu.

" mai kuma mukayi zakuyi arresting in mu " daya daga cikin masu machine in ya tambaya amma basu sami amsa da suke ne ma ba, sun dai lura da Omar Wanda zeena ta ba su aikin trailing in whereabout in su, suna tsaye amma kuma su ba a kamasu ba, toh mai hakan ke nufi kenan, setting in su up sukayi kenan. So Zeena was right all along da ta ce bata yarda da su ba.

Kiciniyar kwace kansu suka fara yi amma inaa an rigada an sa musu ankwa. Tuni wata mota kirar Hilux ta zo aka tasa keyarsu sai cikin motar. Duk abinda ke faruwa a kan idonun su Omar, wani murmushi Omar ya saki yana mai kallonsu ido cikin ido har aka wuce dasu bai bin motar da kallo ba.  Juyar da hankalinshi yayi kan kofar warehouse da take abude yanzu.

Abdul ne ya fito Sanye cikin wani bakin wando, da bakar riga, yaranshine kuma ke trailing behind him. Gaisawa sukayi da Omar.

" ya aiki, hope kun samu all the evidence that we need ko " Abdul ya tambaya.

" Yeah, jibi ma nake son zuwa Abuja wajan Alhaji Gana " Omar ya amsa mishi.

" well it was nice doing this business with you . "

" likewise, amma ina neman wata alfarma, in kun kama Salim, da sauran accomplice in shi, ku dan barmin su a wajan mu for a week haka, in ba matsala  ".

Dan shiru Abdul yayi kafin ya jin jina kanshi.

" toh ba matsala amma a dawo mana da su in one piece please"  dariya suka dan, Omar na mai amsa mishi da In Shaa Allah, kafin kowa yayi hanyar shi.

******
Suna isa military mess da ke rabah road, already ma su Faruq na jiranshi tareda su Ozo da Fadil a wajan don haka sai ya fita daga motar,  shiga cikin wajan yayi domin daman akwai dakuna a ciki dan haka canza kayan shi yayi kafin ya fito, ya samesu suna jiran shi, su Sam already sun rigada sun tafi gida.

Ba wa fadil key na motar yayi tareda wasu kudade masu yawa.

" gashi wannan ka ba malam Iro kace gobe goben nan nakeso ya koma garinsu, sannin kuma motar nan ka kai wa Hamisu, car dealern nan kace ni na turoka ". Nodding Fadil yayi ya karbi key da kudin.

 AFRA Onde as histórias ganham vida. Descobre agora