Babi na talatin da daya.

1K 121 7
                                    

Club Quilox.

Zaune su Salim suke akan wata laulausar sofa suna mai jiran isowar su Sid. Tawajen VIP suke, kuma ma a wani secluded waje, domin sai da suka zabi best place da zasuyi business din na su, don kar a sa musu ido. Tare suke da yaran su guda uku, domin in ma su Sid za su kawo musu wargi su gama da su.

Shi Salim ba wai yasan Sid bane, daman Ameer ne ya hada shi da su, shima dai Ameer in bawani saninshi yayi ba Kawai dai sun hadu ne a wani club, yaga sunyi amfani da kwayoyin da su Salim suke safarar. Shikuma ganin haka sai ya ga ai opportunity ne ya zo musu dan zasu sami wasu customers in kuma ma ai daga ganin su yasan kudi ya zauna so baza a samu matsala da suba.

Aikam a haka su Sid Wanda asalin sunansa Sidi suka jawo hankalin Ameer, daman it was their plan all along, sun rigada sun samai tarko kuma ya fada. Daman ba kai tsaye zasu far musu ba even though suna da enough evidence to put them behind bars forever, amma kuma akwai tight security a tareda su, suna so sai sunyi loosing guard in su down a little bit, ba zato ba tsamani sai su far musu.

Daman su suna da ogan NDLEA, dana ICPC duk Omar na da contact da su, kuma da su aka hada wannan plan in. Shi Omar so yake a kama har da Babayo da dan kwalisa, bai son kawai aka ma Salim domin in aka bar su Babayo ba abinda za su cimma donma killa a saki Salim ko kuma ma su koma wani garin da wannan aikin ta'asar da sukeyi. Ace ma da Kawai a safaran kwayoyin suka tsaya, amma suna da charges na rape, human trafficking, money laundering da murder.

" wai ya haryanzu basu iso ba ". Salim ya tambaye Ameer yana mai kai glass in ruwan da ya siya cikin bakinshi.

Juyi Ameer yake yana mai duba wajen ko zai gansu, domin basu dade da yin waya da su ba kuma sun ce mishi suna hanya.

" suna hanya ka basu nan da five minutes zaka gansu " ya ba abokin nashi amsa.

Aikam haka suka kara jira, ba su fi mintuna uku bama sai ga Sid tareda partnern shi Uncle B. Sanye suke cikin bakake expensive looking suit, hannun Uncle B ( shine Sam)  rike da wata bakar brief case wace kudine a cikin ta. Tafiya suke na takama da isa. Fuskar nan tasu a murtuke, yoo daman gasu sojojin sun iya hade fuska sai abin ma ya zo musu a saukake.

Issa sukayi inda su Salim suke, Sid ne ya dan saki fuskar shi tareda da kai hannun shi su gaisa da Ameer, kafin ya juya akalar kallon shi ga Salim Wanda shima ya bawa hannu tareda introducing kanshi da Sam.

" hello I'm Sid, and this is my partner Uncle B"  ya nuna Sam.

Tipping kanshi Uncle B yayi low as a greeting batareda ya ce komai ba. Nodding Salim yayi shi ma tuni ya aminta da su Sid sabida kwata kwata basu ma bar wani hole in da zai bashi daman dago su ba, sabida daman sun san yana da kwakwalwa, kuma dai in ba ayi amfani da irintasa tunanin ba toh tuni asirin su zai tonu.

Zama sukayi suka fara cinikanya. Shi dai Uncle B a zaune yake baya ce wa komai, illa shan giyan da Ameer ya mishi Offering. Shi Sid bai karba ba domin ba wai yana sha bane. Kallon Uncle B, Salim yake yana son gano wani abu amma kwata kwata instinct in shi basu bashi komai ba, shi yana mamakin yanda tunda Uncle B ya zauna ko ah bai ce musu ba.

" wannan bai magana ne " Salim yayi amfanin da habar shi yanuna Uncle B.

Jin tambayar da yayine ya tsayar da maganar Sid. Juya kallon shi yayi zuwa Uncle B kafin yace.

" yana yi amma ba kasafai yake bari aji muryar shi ba, an taba cutarshi ta hanyar amfani da muryarshi aka mishi sharri. Shi yasa yanzu hardly kaji yayi magana ".

Da kallon tausayi Salim yabi Uncle B  da. Sai yanzu ne kuma ya lura da behind hard look in Uncle B, scars ne that would be hard to reopen sabida yayi storing insu far away yanda nothing would trigger those scars. In bai yi magana ba ai ba zai tuno da pain in ba.

Komawa dai sukayi suna tattauna wa kafin daga kashe dai suka siya kwayan, daukan daya daga ciki cocaine in dake cikin leda Uncle B yayi, bude wa yayi ya zuba farar hodan a kan hannun shi, kai wa yayi Kusa da fuskar shi for closer inspection, by mistake hancin shi ya shako powder ai kam da sauri yayi watsi da ita tareda da girgiza kanshi domin jin shi yayi wani doom, kafin kuma ya jishi awani high, gani yake ma kamar weight in shi ba zai dauke shi ba.

Dariya su Salim suka fara ganin reaction in shi. Shi dai Uncle B sai da ya dan dawo daidai kafin yayi Nodding wa partnern shi. Brief case in da suka shigo dashi, Sid ya mika musu tareda da tashi daga kujeran, shi kuma Uncle B yana mai kulle jakan da kwayoyin suke ciki.

" it was nice doing business with you, now I'll take my leave but be rest assured I'm coming back for more " Sid yafada da wani smirk akan fuskar shi.

They sure are coming for more Uncle B ya ambata a zuciyarshi. Kara basu hannun Sid yayi kafin su fita daga club in with a proud smile on their faces. Wannan kenan.

****
Su Salim kuwa suna ganin fitar su Sid suma suka fita daga club in. Motar da suka zo da ita suka hau tareda da fara driving zuwa hotel in dasukayi lodging a ciki.

" Alhaji yanzu muka gama counting kudin, komai ya cika " Salim ya fada yana mai zaman dirshan akan gadon dakin hotel in. Gefan shi kuma wata mace ce wace baza ta wuce shekaru sha tara zuwa ashirin ba. Sanye take da wata lingerie baka, wacce tayi sticking to her kamar second skin. Box braid ne akanta, wanda ta bazashi a bayanta.

Fuskarta fayau ba makeup, amma ba laifin kyakyawa ce, baka ce irin bakinnan mai shining, lips inta kuma pink ne wanda yakara fito da tsantsar kyaunta. Jingine take da headrest tana jiran ya gama waya su cigaba da holewarsu.

Banji mai akace ba sai dai ji nayi Salim yace.
" full payment sukayi ".

Kara magana na dayan barin yayi kafin Salim yayi nodding kanshi tareda cewa .

" In Shaa Allah, gobe da asuba zamu shigo ".

Haka dai suka dauki hour daya yana magana da mutumin kafin kuma suyi Sallama ya kashe kiran. Aikam kamar jira ake ya gama wayar, domin ko yana nema ajiye ta ya ji wani kira, dubawan da zaiyi yaga matarshi ce Salima ke kira, tsaki yayi tareda ajiye wayar. Amma kuma yana tsinkewa wani kiran ya shigo, tsaki ya saki, ya dauki wayar tareda fita daga cikin dakin, ita kuma yarinyar na kallon shi tana mamakin halin Salim, ta duba wayan ta san kuma wa yace ke kiran amma jibi yanda yake yi, kamar bashine yayi ta roko lokacin da yarinyar nan ta falasa shi a lokacin dinner bikinshi ba, amma yanzu ita ce  abin wulakantawa. Shiyasa bariki ma tafi dadi ta fada a zuciyar ta. Tabe bakinta tayi tana mai kauda tunanin ma aranta as she awaits for his return . Wannan kenan.

************************************
Toh fa mun fa shigo cikin labarin, yanzu za a fara game in.

Vote, comment and share.

Not edited

 AFRA Where stories live. Discover now