babi na biyar

1.3K 136 3
                                    

Qarar ringing tone din wayar tane ya fargar da ita daga tunanin da ta lulla. Dogon numfashi ta sauke kafin ta janyo wayar dake a jikin carji akan vanity table in dake dakin ta. Kai idanun ta tayi izuwa ga screen in phone din. Sunan da ta ganin ne yasa tayi saurin dauka tare da karata a kunnen ta na dama.

" hello " tace fuskarta dauke da dan karamin murmushi.

Amsawa akayi a d'ayan bangaren. Magana suka fara yi na dan mintina kafan ta kashe wayar. Ajiya wayan ta tayi, ta tashe daga kan stool in sai bathroom. Alwala ta d'ora ta zo ta shimfida prayer mat, tayi nafila raka'a biyu na neman sa'a akan abinda tasa a gaba. Ta yi addu'oi ba adadi kafin ta tashi ta shiga closet in ta domin ta shirya.

******
wani katon Gida ne wanda ya amsa sunan sa gida, mai b'angare daban daban. Flat houses ne a gefe kowane ciki da parlour da kuma kitchen ne aciki. Sai kuma wani guda daya da shine suka sa a tsakiya wanda yake gidan sama ne. Qaran kida ne kawai ka tashi a harabar wadda ta sanadiya speakers in da a ka aje ne a cikin wani shelter wanda ya k'awatu iya k'awatuwa.

Flowers ne irin su roses da lilies shuke a wajen tareda grass carpet da ke kwacen a k'asan wadda ka nuni da jijiyoyin ta sunkama k'asa kuma tana samun kyakkyawar kulawa daga gardner.

Ko ina cikin gidan in mutum ya waiga zaiga yammatane da samari. Kowace kala a kwaita kuwa, daga bak'a zuwa fara, zuwa gajeriya zuwa mai tsaho. Kowaccen su tana cikin shiga wacce Babu tsari, duk al awaransu a wajen.

Babban gate in da zai sada mutum zuwa gidan ne aka bud'e, turo kofar tayi tana sako kafarta d'ayan bayan d'aya, tana taunar cingum. Sanye take da bakin kaya, doguwa riga ce ta abaya wanda akayema ada da golden stones a jikinta, blonde wig ne a kanta Wanda da parka a tsakiyan kanta, yayin da ta yana siririn mayafin abayan a kanta. Black ray bands ne a karan siririn hancin ta wanda ya k'awata kyayyawar fuskar ta.

Tafiya take yi tana yasine fuska, Kai da ka gan ta kasan tafi k'arfin zuwa irin gidan duba da yanda fatar jikin ta take Mai laushi, tare ta santsi da kuma kyalin da take. Duk inda ta Kai idanun ta sai tayi istigifar doman kuwa masha'a kawai ake a tsakar gidan.

Dogon tafiya tayi kafin ta sada ta da babban gidan, shiga tayi kanta tsaye domin kofar abud'e take, kai da ka gani kasan gidan kamar hotel yake amma fa na karuwai. Cikin a k'awace yake da stainless glasses a ta wajen reception in. Sai kuma waiting chairs kamar guda hudu a jere a wajen.

Wajen Wani saurayin namiji ne wanda bazai wuce shekara talatin ba, wanda yake zaune a gaban desk in reception din ta nufa da takun nan nata kamar na hawainiya, dab da glass in ta tsaya tana mai taunar chew gum k'as k'as  yayin da ta d'an buga two fingers in ta akan desk din, shiyayi sanadiyar jawo hankalin receptionist din.

Murmushi ya fara sakar mata yayin da idanun shi yayi artabu da ita, ba abinda yake tunani sai yau sun sami sabuwar jini wanda yake ji a jikinshi zata kawo musu customers duba da irin kyaun da dirin da Allah yayi ta da shi.

" Hello barka da zuwa gidan kashe ahu, muna miki marhaba da zuwa aljannar duniya " yafada a yayin da yake murmushi.

Murmushin ita ma ta sakar mashi wanda yayi sanadiyar sashi had'iye wani yawun da bai shirya ba. Murmushin ta kad'ai abin kallo ne  ya fad'a a zuciyar shi.

" thank you " ta fad'a a gajerance.

" I'm looking for Ya tsana, hope she is around"  tayi tambayar yayinda take kare ma reception in kallon. Balaifi wajen yana da kyau sai dai kash ba irin wajen mutuncin da mutum zaije bane.

" Barin duba miki"  ya fada a takaice, kafin yaje ga computer dake gabanshi, dubawa yafarayi yaga ko yar Tsana is available. Bayan en mintunane ya juya kallonshi gareta.

 AFRA Where stories live. Discover now