Babi na Sha Biyu

1K 162 2
                                    

Idanun tan sunyi luhu luhu wanda ke nuni da ta dade tana zubar da hawaye , don ko sunyi jajur da su. Zuciyar ta wani irin tafarfasa take, tarasa in zata sa kanta ta ji dadi.

Bude kofar dakin nata akayi, wacce wata yar dattijowa ce tashigo ciki. Ganin yanayin da yartata take ciki ne yasa ta yin hanzari ta isa gareta tare da cewa .

" wai har yanzu maryam kuka kikeyi ".

Kara narke wa maryam in tayi tace
" toh mama yakike so nayi kina ganin fa yau su Abul bait sukaje neman wa ya Faruq aure, ni kuma kenan inyi ya.".

Ita abin naba ma maryam bakin ciki ace wai har da babanta akeje niman auren mutumin da kai tsaye ya nuna bai son aurenta, amma ubanta ne ma  a gaba gaban masu zuwa neman mishi auren bare.

Hade rai mama tayi tare da yin kwafa kafin tace . " kaiya kefa maryam , dadina da ke gajen hakuri, bai dai na ce ki bar komai a hunnan na ba ?".

Nodding head in ta maryam tayi Wanda ya sa maman gogemata hawayenta.

" toh kiyi hakuri, ki shiru ba dai yace baya sonki ba, sai Wannan kodadiyar mai jin masu jan kunnuwan nan. Zai dawo da kanshi ne ma yace kai zai aura, barni da da su " maman ta sake yin kwafa kafin tafara kwantar wa da yarta hankali tana kwararo mata alqawaruruka da take ganin zata iya cikamata. Wannan kenan.

******
Zaune yake a cikin office in shi mai girma da kyau. Office in dan babbane mai dauke da deep mahogany desk Wanda ke dauke da apple computer da wasu yan tsirarun files. Gefen office in ta haunnun hagu wani shelf ne da aka hadashi jikin wall in, files ne da books ajere neatly a ciki. Sai kuma bai right wasun two sitter couch ne da one sitter, irin na zamani masu kyau. Sai kuma yar madaidaiciyar plasma TV dake daure a jikin bango tana facing in kujeru.

Hankalin shi gaba daya na kan computer, yana surfing through wasu abubuwa. Knocing in da akayi a ta kofar ne ya bashi dama daga idanun shi zuwa kofar, yana mai jirin Captain in da ya kira yan mintuna da suka wuce ya zo.     

Shigowa Captain Sidi yayi bayanda Omar ya bashi daman shiga, zuwayayi gabanshi tare da sara mishi, yana mai cewa.

" sir, gani " .

Dan lumshe manyan idanun shi yayi kafin ya bude su, sai da ya dauki yan sakonin kafin ya kai hanun shi ga wani blue file wanda yake a yashe kusa da sauran files in, mika ma Captain Sidi file in yayi, yana mai masa bayani.

"ina so kaje wajen Sam yayimin tracking number nan, amma jar ka bari kowa yasan da wannan  ." .

" okay sir " ya amsa.

" you can go " yayi waving dismissive hand Wanda ya ba Sidi daman tafiya bayan da ya kara saluting mashi.

Dan jim yayi kamar mai tunani wani abu. Ko da yake tunanin yake mana tunda an sa shi yin abin da baiyi niyaba. Shi kwata kwata aure ma baya gabanshi yanzu, a bari yamaji da hayaniyar aikin shi za a sa shi dauko wani nauyi yadora a kanshi.

Shi don dai ba yanda zaiyi ne shiyasa har ma ya deciding Kawai ya nemi aure Afra, after all yaga yanda kakaninshi sukayi acting a lokacin da Abida ta shararo musu karyanan, kuma mai dai gwanda ita da Wannan marakunyar yarinyar da aka so hadashi da.

Koda maryam yar uwarshi ce bai taba jin so na yanuwantaka wa yarinyar ba Kawai he despises both ita da maman nata. Yana cikin tunaninan ne wayar shi ta Fara ringing, duba screen in yayi yaga sunan Abdullahi radau a jiki, dan murmushi yayi kafin ya kai hannun shi kan phone in, yana mai tunani lalle wannan kiran na Abdullahi ba zai rasa nasaba da kin zuwa gidan shi da yayi promising zai je ba, amma he was busy, kwata kwata week in nan bai samu ya zauna ya huta bama.

Sliding yayi yai receiving kafin ya kara a kunenshi.

" Assalamu alaikum. "

" wa alaikumus sallam, Omar ka kyauta, kaji " Abdullah ya ansa a dan hasale, domin ba karamin jin haushi Omar yake yi.

 AFRA Where stories live. Discover now