Babi na Arba'in

1K 130 5
                                    

Tuki yake hankalinshi kwance, ko ince persona in shi a lokacin zai nuna ma mutum kamar hankalin nashi a kwancen yake, amma kuma deep down wani ruruwan hadarin tashin hankaline yake nukurkusa a cikin zuciyar shi. Yarasa mai yake mishi dadi, kai yama rasa dalilin wannan bakin cikin. Kuma shi dai ba zai iya tantance dalilin da yasa yake jin hakan ba.

Traffic light da ke ta wajan ahmadu bello way ne ta tsayar da hannun da yake. Tsayawa yayi yana mai jiran ganin green light domin ya wuce, jin motsin mutum a ta gefan shine ya bashi daman dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga. Gefan shi ya kalla, ganin Afra zaune tana mai daddana wayarta ne ya tunatar da shi da ba shi kadai bane.

Kallonta ya tsaya yi yana mai jin wani nauyi akasan zuciyarshi. Ba zai iya cewa ga abinda ya jawo nauyi ba amma yasan yana da nasaba da ita ne. Mai yasa yake jin haka, mai zuciyarshi take neman jefa shi ciki ne.

" Lafiya" ya tsinkayo daddadar muryarta a yayin da ta bugi dodon kunnenshi wace tayi nasara kawar mishi da tunanin da ya addabeshi.

Blinking yayi so daya, kafin ya daga giranshi daya yana me jefan ta da kallon tambaya.

" naga sai kallona kake kamar wani" sai kuma tayi shiru ta kasa karasa zancen nata.

" kamar wani me " ya jefo mata tambayar. Ganin an ba barin su hannune ya sa shi mayarda hankalinshi kan windshield in, shima ya fara tafiya.

Shiru tayi mishi bata bashi amsar da yake bid'a ba,ta wutsiyar idon shi ya kallota yaga kwata kwata hankalinta kacokam ta mayar ga kallon wajan da suke wucewa.

" kamar wani tsohon maye ko " muryarsa ce ta tsinkayo ta cikin dodon kunnenta. Kallon shi tayi taga kamar ma ba shi yayi maganar ba, fuskar sa dai gata nan ba yabo ba fallasa, bazata taba sanin what goes through his mind ba. Ita bata son wannan sabon Omar in, she can manage with the playful one amma wannan yana bata tsoro. Kwata kwata tunda suka tashi yau ta fuskanci kamar a wani sukuku yake, kwata kwata ko dan wasan nan ma da ya saba mata kwai don ya ga irritation inta bai yi ba.

Bawai kuma zata ce fushi yake ba, don hakan ma bai nuna a expression in shi ba. Toh mai matsalar shi, ko kuma daman dai hakan yake itace bai nunawa ba. Domin sau da dama Abida tana nuna mata cewa ai Omar ya dan canza tun bayan auran su, har ta kan yi dariya ta ce mata a hakan, don ita yanda ta sanshi kafin suyi aure hakan yake, ko da dai playful side in shi sai da sukayi auren ta san da shi. Abida kan yi murmushi tanuna mata ba hakan yake ba.

Mutum na biyu da ya kara mata irin wannan zancen ne Aisha matar Abdullah, so sai abin yake sata tunanin in da ba haka yake ba, ya yake daa, wani irin haline da shi da har mutane zasu ringa cewa ya canza.

" tunda kasan mai nayi niyar fada mai na son in karasawa. "

" toh mai yasa baki karasa ba ". Ya jefo mata tambayar.

" I did it out of curtesy"

Dan murmushin gefan baki yayi kafin daga bisani yace.

" toh yayi kyau matar tsohon maye " shine kawai abinda ya fada.

Dan dariya tayi tana mai shaking head in ta, a sigar da ya furta kalaman ne yabata dariya. Shima kallon ta yayi na yan sakonni kafin ya mayarda idonshi kan tukin da yakeyi. Yana me jin kaso ashirin a cikin dari ya ragu daga cikin damuwar da yake ciki.

*****
" Sannun ku da zuwa " Amina ta furta tana mai yi wa Afra wani bear hug. Hugging inta Afra tayi baya, tareda amsa mata. Shi kuma Omar takalmashi ya karasa cire wa tareda shiga ciki inda ya taradda Uncle H shima na kokarin fita.

" ah ashe kun iso, ina Afran " ya ce mishi, yana mai kai mishi hannu suyi salama.

" na barsu a porch, kasan mata da wani feleken su, in aka tsaya gaisawa kamar ba za a dena ba." Ya dan tabe bakinshi.

 AFRA Where stories live. Discover now