Babi na Ashirn da tara.

1.1K 107 2
                                    

Lagos state.

Salim ne zaune a cikin wani haddaden garden Wanda aka kawata shi da fure masu kyau da kamshi, between his fingers kuma wata katuwar taba ce irin ta masu kudi sakale, time to time yana kai wa bakin shi yana zukar hayakin. Gefanshi kuma abokinshi ne Amir shima dai kamar Salim, hannun shi sakale yake da tabar sai dai shi a gefan shi akawai kwalbar giya tareda da dan karamin kofin da yake shan giyar da.

Abinda shikuma Salim bai yi kenan, shi kwata kwata ma giya bata cikin tsarin shi, bai damu ba in mutum ya sha amma shi dai bazai sha ba, domin duk abunda zai gusar mishi da tunani ba son shi yake ba. Balle ma yanzu da yasan yana da enemies, ai ya kamata kullum yana cikin hayacin shi sabida za'a iya kawo mishi hari.

" yau zamuje wajen su Sid ko " Salim yayi magana.

" eh ai sun ce za su zo da kudin merchandise in " Ameer ya bashi amsa kafin ya kara zukar tabar shi, sai da ya bari yayi yan sakoni kafin ya buso shi waje.

"okay " Salim yace tareda da yarda ragowar tabar hannun nashi.

" a wani club ne ?" Ya kara tambayar abokin nashi.

Shima Amir kamar Salim, yarda tabar yayi tareda sa dunduniyar takalminshi ya taka. Dauko kwalbar
giyar yayi, ya bude tare da Zuba wa a karamin kofin glass.

" a Club Quilox ". Ya amsawa abokin nashi kafin ya juye giyar da ya deba cikin cikinshi, dan yamuste fuska yayi domin giyar na da zafi amma a hakan yake jin dadinta. Kara deba yayi zai sha amma Salim yayi saurin karba tareda wuragar da kofin gefan shi.

" you need to stay sober, kasan fa Muna da fita yau ".

Hararar Salim yayi, kafin ya mayarda giyan ya ajiye sabida ya san shi yana daga cikin masu buguwa da wuri in sun sha giya. Kuma sabida sanin importance na aikin nasu ne ma yasa shi agreeing da aminin nashi. Wanna kenan.

*******
Wajen karfe 11 suka isa Lagos, sabida ma samun delay da sukayi ba suyi departing da wuri ba, ita dai sai da suka hau jirkin ma tasan da inda zasu tunda ta private jet in baban Omar suka tafi. So tayi mamakin da taji wai zasu tafi Lagos, toh suyi me a Lagos, amma kuma ganin da convoy in shi zasu tafi, yasa ta tinanin ko work related abu ne zai kai shi Lagos.

A gidan shi da ke ikoyi suka sauka. Gidan ba wani babba bane amma ya hadu sosai kamar a kasan turawa, yana kamada irin luxury houses in nan masu zagaye da glass. Hawa uku ne gidan, kuma yana da basement. Parlour daya ne a kasa amma irin makekenan ne da kitchen sai kuma toilet, hawa na biyun kuma dakuna ne manya manya guda biyu tareda da wani parlor, hawa na ukun kuma game room ne, sai wani indoor swimming, sai kuma green house.

Yau kwata kwata ba wani abun da tayi in ba bacci ba, tun bayan Sallah Fajr da Omar ya fita bai dawo ba, ita kuma gashi ba wai sanin garin tayi ba balle ta fita. Ganin har sha biyu tayine yasata tashi daga gadon domin ta je ta watsa ruwa ko ta saman ma cikinta abinda zata ci.

Tana fitowa daga bathroom in ta je cikin closet inda ta ajiye akwatin ta, budewa tayi ta dauko wata Hkg atampha wace akayi mata zanen lace. Dinkin riga peplum da skirt ne. Sakawa tayi ta feshi jikinta da turaren Victoria secret. Duba clock tayi taga sha biyu da hamsi don haka ta dauki hijabn ta tayi nafila, tana zaune aka kira sallah. Don haka sallah tayi kafin ta je wajen mirror ta dan fara light makeup.

Gira tayi tareda da saka eyeliner, sai kuma baking under eyes inta da tayi tareda da forehead inta da chin, sai kuma blinding highlight in da ta saka, lining lips inta tayi da wani light brown pencil, tareda saka nude lipstick akan lips in nata.

MashaaAllah wannan simple make up in ya karbi fuskarta. Daurin turban tayi tare da fito da jelar gashin ta kafin ta dauki wayarta ta fara selfie. Sai da ta dauki kusan guda goma kafin ta tashi ta fita daga dakin. Sauka kasa tayi ta je kitchen domin nai man abinci.

 AFRA Where stories live. Discover now