Babi na goma

1K 134 1
                                    

Saurin dauke idonta tayi daga kanshi lura da tayi duk hayaniyar da ke tashi a cikin dakin ya lafa. Maza uku ne, Omar, Affan da Uncle Y tare da Maryam a dakin together with them kuma Baba Alhaji ne tare da inna wace ke zauna kusa da Maryam.

Sallama Afra da Abida sukayi a tare, amsa musu akai. Daga kanshi kaka Alhaji yayi ya kallo su Abida kafin ya madai Kallon shi ga Omar Wanda haryanzu Afra ya ke kallo ya ma manta da yana tare da mutane.   

Mayar da idonshi yayi akan Afra, ya mata kallon yan sakoni kafin ya dauke idonshi daga kanta yana dan murmusawa mai tarin ma'anoni.

Wurin da Inna ke zaune Abida ta je ta zauna, with Afra following suit. Gaishe da inna suka fara yi, inna ta amsa musu da fara'a kafin su kamar da hankalin su kan Baba Alhaji, shima gaishar da shi sukayi daya bayan dayan yana amsa musu da fara'a tare da yar tsokanar Abida.

" Wannan kuma matar tawa fa " ya tambayi Abida yana mai nuni da Afra.
 
Juyo da hankalinsu sukayi kan shi, Uncle Y yana dan satan Kallon Afra. Yarinyar tayi mishi a ko ina. Yana mai tunani tambayar Abida wace ita in sun kebe.

Har Abida ta bude baki zatace kawarta sai ta tuna da abin da Afra tayi mata dazu, Kawai sai naga tayi muushi tare da Kallon Afra kafin ta mayar da kallon ta kan Omar Wanda shima yake kallon ta duk suna jiran suji mai zata ce .

" Surikarku ce " ta Abida a taikace tana ma Baba Alhaji nuni da barin da Omar yake.

Ai kuwa nan da nan kaka Alhaji ya dago ta, ya kalli omar kafin ya Juyo.da hankalin shi kan Afra, wace kuwa a lokacin take jefawa Abida kallon tuhuma da tambaya. A ina ta zama suruka, wai ma mai Abida take nufi da haka.

" wai waye yayi kamun ta ne ni kun barni a dubu"  Inna tayi maganar tana mai son jin karin bayani.

" waye  in ba wannan ja'irin yaran ba " kaka Alhaji ya amsa mata yan mai dafa omar, wanda yayi mutuwar zaune.

Kara jaddada maganar Abida yake aranshi, yana tunani mai ya kai Abida wannan katubarar. Ita Afra a wajenta haka abin yake don ita ta zata da wasa Abida ta fada ma kaka Alhaji. Ita tama rasa da Wanda za ayi wasan hadin sai da Omar.

Uncle Y kam kusan shima mutuwar zancen yayi. Ashe dai an rigashi har da yake tunani cusa kanshi ashe kam da yayi abin kunya, da na su kuma uba yaso. Allah ma ya soshi ba furtar komai ba.

" ayereyere dan nan ka iya zabe"  inna tayi guda wace sai da tabawa su Omar mamaki, Maryam kam ta cika ta yi fam. Don raini hankali da son cusa mata shine har da wani guda, daman tasan Inna ba wani damuwa tayi da ita ba amma ba ta zata rashin son had yakai haka ba, tsaki tayi tare da tashi daga wajen ta barmusu dakin domin ji tayi wani abu ya tokare mata a wuyan ta, daman it tunda ta ga Afra taji yarinyar bata mata ba. Ba suma kula da fitar Maryam ko kuma dai sun share ita dai Inna jawo Afra tayi jikin ta wace tayi tsuru tsuru tanajin abin mamaki.

Kunya ce da takaici ta lulube Afra sanadiyar jin shigowar wata yar tsohuwar mace wacce gudar Inna ce ta shiga da ita cikin sanin coward ba abi kadan ne zai sa Inna guda ba sai abin farin ciki. Aikuwa inna ta zaiyana ma Aunty mama abinda ke faruwa wace itama ta rangada gudar tata dama gata gwanar guda.

Shikansa Baba Alhaji murmusawa Kawai yake yana kallon matan nasa suna ta murna, shima kanshi murnar yake domin ya lura da Afran natsatsiya ce kuma ma ai yasan Omar bazai yi zaben tumun dare ba. Hamdala yayi a zuciyarshi shima yana nuna na shi jin dadin amma a cikin ranshi

Ba abinda Abida ke yi sai murmushi Wanda ya kai har kunnenta. Duk ita Afra sai taji kanta a takure tare da jefa ma Abida harara. Shikon gogan ku kasa cewa komai ma yayi,  ya rasa ma me yake ji game da abinda Abida tayi. A wani bagare kuma yana jin wani sanyi na ratsa shi yarasa na maiye. Ta ka maimai dai bai ma san mai yake ji ba a lokacin.

 AFRA Where stories live. Discover now