Babi na sha shida

939 124 4
                                    

Maska Estate .

Yau ranar asabar ce, ranar da kowani ma aikacin gomnati yake gida yana hutawa. Fitowarshi kenan daga wanka, yana tsane kanshi da dan karamin towel, yayin da jikin shi ke rufe da farin bathrobe. Daki ne babban gaske, Wanda aka kawata da makeken gado kalar ash, patin dakin kuma off white ne, tare da ash coloured labulaye. Tsaye yake a gaban mirror, turaruna ne da man gashi da na jiki masu kyau da tsada ajeyi akan table in.

Body lotion ya fara shafawa a ko ina na jikinshi, kafin ya fesa turare mai dan karan kanshi a jikin, kana ya deba wani hair oil ya sa a low cut hair in shi wanda a take wani sihirtacen kamshi ya garwaye dakin. Closet in shi ya nufa domin naiman kayan sawa. Wani army green cargo pants ya dauko, tare da hadda shi da black T-shirt, da ya dan yi hugging physique in shi.

A gurguje yasa domin yaga yana nai man yin letti, domin ko sunyi niyyar shi da su Affan suje gidan gonan Baba Alhaji, domin shakatawa. Kara feshe jikin shi yayi, kafin ya dauki green snapback in shi tare da ray ban in shi ya fita daga cikin dakin.

****
" Big man ya gari " Abdullah ya fada yana mai mika ma Omar hannu.

Gaisawa sukayi irinta musulunce kafin su karasa isowa wajen da motoci suke. Daman tun Jiya Omar yayi da Abdullah ya zo sai su tafi tare tunda shi Abdullahi ma yagama dutin shi, so suna neman hutawa without any hinderance.

A tsaya suka sami sauran mazajen. Daman Affan ne, da Hafiz tare da Alamin. Uncle H yayi tafiya, So shi kadai ne missing person a cikin group in na su. Gaggaisawa sukayi da su kafin su dunguma cikin wata bakar Lexus 2019 SUV, Affan ne yayi volunteering din tukasu.

Shiga sukayi duka ana raha, kowa na kawo nasa labarin shi, shi dai Omar nashi kallon su. Shi mamakin su Affan ma yakeyi yanda in suka fara surutu ba kakkautawa. Kwata-kwata ba su san yin shiru ko na second daya ba.

" ya naga ka yi shiru ne Omar, ko dai tunani ta ake ne " Abdullah ya tsokaneshi, yayin da yake daga ma Omar gira daya.

Dariya sauran sukayi suna mai jiran jin amsar Omar in. Duk sun san tsokana ne irin na Abdullahi, amma ai kowa yasan Omar da shegen miskilanci. Su abin ma da ke basu mamaki wai Omar ne har da budurwa. Don dai har ansa ranar auren ne da sai suce karya yake yi ma.

" yes. I really miss her. Don dai na yi promising zan biku farm house ne da na je naga Noor of my heart ". Ya fada, yana wani lumshe idanunshi kai kace dagaske abin har zuciyarshi yake.

Aiko duk mazan bawanda bai yi shewa ba, duk suna mai tofa albarkatun bakunan su.

" oh wayaga su Omar, baban soyayya. Sai fa Noor of your heart " Hafiz ya fada.

" aikam dai ni har mamakin Omar nakeyi, in ka ga yanda yake ji da Afra, sai ka bude baki " Affan ya kara nashi.

" chab kai kenan ma da ake wa maganar ta, ni akwai ranar da nace mishi ya kaini wajenta domin in ganta ka ga wani kallo da aka min, ai Kawai sai na ja bakina nayi shiru " Alamin ya fada.

Dariya suka kwashe da shi. Shi dai Omar yana jin su bai ce musu komai ba, amma shima fa yana dariyan a ci-ciki.

" Ai kasan Omar in na mu ne akwai kishi"  Abdullah yafada. Yana mai kai duban shi zuwa barin da Omar yake a zaune, amma kwata kwata ma zaka zata bai san mai suke ba domin ya lumshe idanun shi tare da leaning kanshi a headrest in kujerar.

" ba kadan ba. Ai ni zan fada maka haka " Affan ya kara fadi yana mai dariya.

Ahaka ana raha, sukayi tafiya mai dan Nisa har sai da suka iso maraban jos, wani kwana suka yanke suka shiga in da zai sada mutum zuwa ga gonakin mutane. Gargada ce hanyar, hakan ne ma yasa su dauko mota mai dan bussa, domin samin saukin tafiyar tasu.

Ba'a fi tafiyan mintuna kalilan ba suka iso gaban wani fancy looking gate. Armed securities ne tsaye a gaban gate in, ga kuma cctv camera tana hasko su. Duk da sanin suwaye a motar, haka bai hana daya daga cikin guard in zuwa wajen su ba. Jawo glass in kasa sukayi domin su basu damar yin aikin su, suma kuma su bi dokan da aka saka.

Da hannu guard yayi alamar da abude musu. Wani dan room ne a gefan gate wanda shine control room in. Wani abu guard in da ke ciki ya danna Wanda ya bawa gate daman budewa.

Shiga sukayi ciki. Wajen babbane na karshe. Yana da wasu maka makan gidaje biyu, ga parkin lot in da zai ishe motoci guda ashirin ma. Bishiyoyine a ko ina wa enda suke bawa wajen shade. Affan na parking, duk suka fito.

Dukan su sanye suke da similar attire da Omar ya sa sai da bambanci colour. Affan nashi black cargo pants ne ya dora red T-shirt da kuma red snapback, shi kuma Abdullah black pants ne tare da black T-shirt, shima snap back in shi black ne. Hamza da Alamin kam nasu gajerun wanduna ne masu kalar ruwan kasa sai different coloured T-shirts da suka saka. Na Hamza fari, na Alamin kum green.

Mika sukayi domin duk sun dan gaji, sabida gargarar hanyar. Toh abinka da ajebotas.  Tafiya sukayi suna bawa buildings in baya. Suna shiga ta ciki ciki inda dawakai ke a daure.

Kowa wajen dokin da ya saba hawa yayi. Shi na Omar wani White horse ne Wanda babansa ya siyo mishi daga Turkey as a birthday present. Sauran kuma nasu daga masu coppery colour sai baki wuluk.

Shafa kan dokin nashi Omar yakeyi, shikuma dokin yana ta miko kanshi wanda ke nuni da sun saba da juna. Kunto mishi dokin akayi, ya fito da ga stall in. Kama igiyar dokin yayi ya fito da shi zuwa wani plain field, anan ya  samu sauran duk sun hau kan nasu, shima hawa yayi suka tsaya a jere kafin yace.

" who is ready to beat the undefeated"  ya fada jokingly.

" we are " Abdullah ya amsa musu.

Fara counting yayi daga ten kasa, kafin su harba da dokunan nasu with a speed da sai da naji tsoro.  Wannan kenan.
____________________________________________________________________________

And I'm done.

Kai typing akwai wuya..
Ku dan ratatapo min comments, kila ku sami wani update anjima.

Vote, share and comment.                            

 AFRA Where stories live. Discover now