Babi na Sha Hudu

1K 176 10
                                    

Qauyen birnin gwari.

A cikin qauyen birnin gwari, a cikin daji kan wani dutse mai dan fade. Anan ne gidan wani hatsabibin boka Wanda ba wanda bai sanshi a iya hatsabibanci ba. Mostly ma manya  manyan mutane ne ke zuwa mishi sabida aikin shi kama yankan wuka ne.

Tafe mama zalikha take tare da aminiyarta laure. Kutsawa suke ta cikin dajin ba tsoro ko fargaba a ransu, domin ko zuciyar su ta gama kekashewa ma,  su kansu wani ya gansu sai su bashi tsoro. Domin kuwa a wani daddaudan kayan suke, jikin su duk doyi yakeyi amma su ko basa ji ne ko kuma sunyi deciding kar su jine oho.

Shi dama a kaidar zuwa gurin bokan baka zuwa mishi da tsarki, tareda da kuma tsabata domin halitun da yake amfani da su ba susan tsabta. Shiyasa duk Wadanda za su zo gurin shi zaka gansu kamar mahaukatan sabon kuma.

Tafiya sukeyi suna sauri, suna mai addu'ar kar su sami mutane dayawa duddadai har yanzu garin bai gama wayewa ba, sabida shi in dai zaka ganshi to kayi asibanci in bahaka ba rana nayi bazaka samu daman ganinshi ba sabida layin da ake yi .

Isa sukayi wajen gidan shi, abinda zai ba wa mutum mamaki shine gidan nashi ma wani dan tsurkukun gini ne na laka Wanda daga gani inda yake surkulenshi ne kawai yayi making up gidan. Mama zalikha ne take niyar shiga Kawai taji an daka mata tsaya da wata kakkausar murya.

" wace wannan zata shigo mana ta gaba ".

" afuwa boka finkiru " mama zalikha ta fada da sauri, tana mai shiga cikin akurkin da baya.

Binta laure tayi itama ta shiga suka samu bokan a zaune duk dauda jikin shi, gashi fuskar shi bakikirin, ga manya manyan jajayen ido da yake da su, dakin shi kam sabida wari kamar Wanda aka yarda mushe a ciki amma su sabida muguwar zuciya ce garesu ba sa ma jin warin.

" mai ke tafe daku. Ko da ma dai an fada min dalilin zuwan ku amma in na so inji da bakin ku".

" hmm boka finkiru 'ya ta ce wanda take so shi kuma bai sonta,  kai in takaice ma dai har an kai kudin gaisuwansa,  an sa bikin sa nan da wata uku , toh ni Gaskiya in naso ne in da hali a fasa bikin da wacen yarinyar ayi da 'yata." Ta gama zuban da take kafin ta kai aya.

Dan bubuga kasa yayi yana wani surkulen sa kafin yayi dan murmushi mugunta, yayinda yake kallon su laure da wani irin kallon da ba za su iya fassarawa ba. Sai da ya dau mintuna ahaka kafin yace. " kuje ku dawo nan da kwana biyu , ina so in yi bincike akan al amarin ".

Godiya sukayi, suka tashi tare da ajiye mish rafar dubu daya guda biyu. Shi daman al adarshi ce in dai kazo wajen shi sai ka ajiye makuden kudi. Fita sukayi da baya kowace na cikin farinciki suna ganin ai har ma aikin su yayi. Wannan kenan.

******

Zaune yake a cikin mota, motar a kune take don haka ACn da ya kuna tana ta busowa a hankali, ga wani kamshi turaren wuta da ke tashi a cikin motar kai kace cikin dakin wata amaryar kanuri kashiga.

Sanye yake da black wando, da white long sleeve shirt, amma yayi folding hannun ya tsayar da shi iya elbow in shi. Kanshi kuma ya kifa snapback ne , ga kuma ray ban glasses manne a idonshi.

Tapping stiring wheel in yake yana mai jiran isowar Afra. Tun mintuna uku da suka wuce ya iso gidansu, a lokacin da ya iso ne ya kirata, yana mai ce mata da ta shirya su tafi. Toh shine dai har yanzu yana jiranta.

Jin karar bude kofar da akayi ta wajen mai zaman banza ne ya bashi damar kallon wajen, Afra ya gani sanye da doguwar bakar abaya da ta karbi jikin ta tayi mata kyau sosai, tayi wrapping scarf inta kamar irin na basma kahie, while idonta na kulle da glasses itama na ray ban.

Ganin nose ring in dake makalle a gefen dan tsiririn hancin ta ne ya bashi mamaki. Daman tana sa abin hanci ne. A rayuwar Omar yana son ganin mace da nose ring, although ba ko wani iri ba, amma indai mace zata sa kuma yayi mata kyau yana son haka. Shagala yayi da kallonta bai masan ta shigo ba sai da kanshi turarenta ya bugo hancin shi tukunna ya farga daga tunani da ya lulla.

Gaishe shi tayi, Wanda ta samu amsar da ga wurin shi a dakile, yana wani ciccin magana, kai kace Wanda yaga wani abu mara kyau. Ita dai Afra bama ta kulla shi ba illa gyara nose ring dinta don taga kamar bai tsaya dai dai ba.

Daman tun daa tana saka nose ring, duba da al adarsuce kuma ma ta tashi taga Ummin ta na sawa, sai abin ya bata sha'awa itama tafara sawa. Shikon dalilin da yasa Omar bai taba sani ba, shine duk ranar da zasu hadu, ita kuma aranar batajin sha'awar sawa shiyasa baisan tana sawa ba.

Tafiya sukayi mai dan nisa kafin su iso kwanar da ke facing bulsawa filling station ta dayan barin. Parking yayi ata gefan hanya. Yana mai baza ido ta inda mutumin zai fito.

Qarar ringing tone in Afra ne ya sashi maida kallon shi kanta, gani yayi tayi picking call in , shiru yayi yana jiran ya ji mai zata ce.

" hello. Eh black Mercedes" ta amsa wa mutumin a dayan bangaren.

Magana take masa wanda ke nuni da directions yake bata, wannan ne yasa Omar kuna motar , da hannu tafara masa da ya shiga ta cikin hanyar da ke gefan su , while shikuma mutumin na bata direction. Tafiya suka yi yar gajeriya kafin su shiga ta wani dan lungu da ke rufer da manya manyan bishiyu. Ba komai awajen sai wani warehouse da ke dan nesa da su.

Kashe wayar tayi tareda fita daga cikin motar. Daukan jacket in shi yayi da ke ajiye a bayan motar, kafin ya bude compartment na motar ya fito da wata black pistol, tare da saurin maqale ta a jikin wandon shi, daman ya rigada ya saka sheath a wando so sai ya rike bindigar gam, saka denim jacket in yayi domin yayi concealing pistol din kafin ya fito.

Yana fitowa yayi arba da fuskar Afra dake jifanshi da wani suspicious look, ita dai batasan mai ya tsaya yi aciki ba, ta dai san ya dan dade kuma ma duba da tint din da ke motar bai sa ta hango abinda yake yi ba.

Shrugging Kawai tayi, ta bi bayan shi without uttering a word. Tafiya suka danyi kafin suka iso abandoned warehouse in. Shiga kanta tsaye tayi niyar yi amma Omar ya ja hannu abayan nata ya dawo da ita baya.

" wai ke bakida hankaline, kikasan maye a ciki da zaki shiga kanki tsaye " ya fada a hasalance yana mai maka mata wata uwar harara. Pouting tayi tareda komawa ta tsaya a gefen shi tana jiran ta ji tayanda za su shiga.

" kitsaya anan, barin shiga in duba"  wani kallon ka raina min hankali ma ta jefe shi da shi kafin ta yi yar karamar tsaki tana mai sa kai ciki turning a deaf ear to kiranta da yake yi.

" this girl will be the death of me "  yayi muttering kafin ya bi bayanta.

Cikin wajen a bude yake ta sama, so hasken rana ya haske wajen tar, a tsaye ya ganta tana mai kai duban ta ga wani mutum da ya tsaya dan baya da su, ba sa iya ganin shi sai dai shadow in shi sabida wajen haske ranar bai kai ba. Wannan kenan.

************************************************************************

Okay.

Please and please you guys should be commenting mana. Or are you guys not enjoying it.?

So here it is , I want to see at least ten comments before I post another chapter, I want to be interacting with my readers, to know what they like or dislike about each character.

Rashin comments in ku na sani jin kamar bakwa son book in, ko dai in dai na ne?

Please ,vote comment and share

 AFRA Where stories live. Discover now