Babi na Ashirin da takwas

1K 144 2
                                    

Juyawa sukayi suka ga mama zalikha ne tareda maryam a bayan ta. Zage zage da ashariya tafara yi bata ma damu da ganin su Inna a wajen ba.

" ina dan abu kazan kazan yake"  ta wagale baki tana fada.  kallon kowa ta farayi, idonta ya hadu da na Inna wace ke wurginta da wani irin kallo amma batayi relenting ba. Matsar da idonta tayi daga kan Inna ko dar bataji ba, balle ma wani abu wai mai suna kunya, aikam karap idonta ya hadu da na Omar.

Tagazan tagazan ta zo kamar zata buge shi amma kuma sai ta ja burki ta tsaya. Tsaya wa tayi tana kallon shi, kallon kallo suka tsaya yi, wani irin kwarjini taji ya mata, tayi sauri dauke idonta daga nashi amma hakan bai hanata misifar ta ba.

" wani dan ***** ne yace ka dakar min ya " ta lalliyo ashar ta hada da tambayarta.

Shiru yayi mata bai amsa ba, bawai kuma don yana jin tsoronta ba a'a Kawai dai don darajar kakaninshi dakuma Ahmad tunda auran baban Ahmad take, da kuma dai darajar itan kamar uwa take a gareshi.

" eh ba tambayar ka nake ba, mai ya sa ka dakarmin ya ". Ta kara wagale bakinta ta furta hakan.

" baki tambayi yar taki dalilin da yasa na daketan ba " ya bata amsa a takaice.

Saka hannu tayi a kugunta tana jijjiga kamar wace zata haushi da duka. Tana hura hanci, ido yayi ja, sai fitar da zazzafan munfashi take.

" eh ta fadamin, akan wannan kodaddiyar ne zaka daki yaruwarka sabida kai inda albarka yake ba ka nan " tace tana nuna Afra, wacce tayi tsuru tsuru tana kallon jibgegiyar matar.

" kul kar in karajin kin furta irin kalmar nan ga jikana. Yar taki da kike damun mu da ita ina cewa yayi bayayi toh mayasa sabida tsabar yada kai da rashin sanin mutuncin kai, zata huce haushinta kan matarshi, ta huce haushin mana akanshi in zata iya " Inna tafada da kakkausar murya.

" waa.  Inaaa Allah ya sawake yata ta aure ragowan wata ". Ta fada ba kunya idon Kaka Alhaji bale na Inna.

Kaka Alhaji shidai mamakine ya sa shi daskarewa, bai taba zata rashin kunyan Zalikha ba ya kai haka, amma ya lura tunda aka fasa hada auren Omar da yarta tazama wata irin mazaqakura. Yana cikin tunanin ne yaji wata sabuwar murya ta dakin kunnen sa.

" toh ai kuma kin makaro tunda dai sai da aka karayi mishi tayin ta a karo na biyu kuma yaki amsa " murya Umman su Hauwa ce ta bugi  kunnuwan mutanen wajen.

Shigowarta kenan ta ji abinda Mama Zalikha take fada ma Inna, ranta in yayi dubu ya baci domin batayi tsamanin rashin mutuncin Zalikha ya kai har haka ba.

Juyawa zalikha tayi tana mai kunfar baki tareda cewa.

"oho dai gwanda tawa ko ta yi kishin ma, ba auran wani akanta, kefa naki yar. Da auran wani take kishi da matar Wanda take so. " tana idar da zancenta ta juya ta kalli hauwa wacce a lokacin ji tayi kamar ta nitse cikin kasa don kunya, sai yau ta kara tabbatar da Mama Zalikha batada mutunci.

Affan ne ya juya yana kallon hauwa tareda da kara maimata kalaman zalikha a cikin zuciyarshi. zuciyarshi ta kasa gasgata mashi zancen nata. Amma kalo daya da yayi mata ya sa zuciyarshi fara tseren fita daga cikin gangar jikin shi.

Shi mamakin yammatan gidanasu yake ace akan mutum daya duk surunga hauka, mutumin ma da baisan suna yi ba.

Itama Umman hakan zuciyarta ta take , bakin ciki ne ya mamayeta tareda da wadai da halin yarta. Umma tasan da son da Hauwa take wa Omar amma bata zata har yanzu son na nan a zuciyarta ba. Ta zata nasihan da tayi mata ya ishe ta dagana da yarda da qaddararta. Umma na son bude bakin ta domin tayi retaliating amma wata tsawa da kaka Alhaji yayi shi ya dakatar da su.

" wai ya kuke wani abu kamar yarane, yanzu agaban surikan naku kuke zubar da mutuncin ku. "

Tsit kake ji a wajen. Kai kallon shi wajen Afra yayi domin ya lura ta tsorata daga wannan tashin hankalin da ta gani, ganinta yayi tayi tsuru tsuru, jikinta har wani kyarma yakeyi. Allah wadai yake da halin yan gidan tareda jin mamakin yanda basa jin kunyan nuna halinsu agaban ko wa ye. Su ko kunya ma babu, sun fara aje jikoki amma har yanzu halinsu bai canza ba.

 AFRA Where stories live. Discover now