Babi na Arba'in da hudu

975 122 3
                                    

A daren ranar tayi kwannan farinciki marar misaltuwa. Ta godewa Allah, ta kuma gode mishi kan amsa addu'arta da Allah yayi. Tashinta safiyan da tayi ne kuma mafarin komai. As usual yanda ta saba haka tayi yau ma, wanka tayi ta shirya cikin kayanta, doguwar rigace pink ta material Wanda aka mata dinki A shape mai aljihu, sai ta dako hula kalar kayan ta saka. Feshe jikinta tayi da turare me kamshin tsiya, kafin ta saka takalminta ta fita kitchen do min taga ko su Maria sun gama dafa mata dankalin da naman da ta sa su dafawa.

Aikam sun gama har ma dakan kayan miyan sunyi, dan haka sai tayi mashing popato tareda hada duk abinda ake bukata a yin potato balls. Haka dai tayi ta gama, sai kuma tayi sauce daman kuma ta saka tilapia fish a cikin oven tana gasashi, irin gashinan da ya ji albasa da attaruhu. Baiyan ta kamala komai ne ta debi kifin don ta yisu da dan yawa. Tasa ma mommy a cikin wata yar madaidaiciyar cooler, ta dako nasu kaka Alhaji ma ta sa musu.

Daman ta saba in dai tayi girki takan turamusu da shi don har Sunyi maganar da ta dai na wahalarda kanta amma taki, toh ya zasuyi haka suke karba even though deep down suna jin dadin abinda takeyi.

Bawa Mariya tayi ta kai na Mommy, dauar kuma ta kai na su Kaka Alhaji tareda hada su da driver domin dukan gidajen da dan nisa da nasu. Komawa sama tayi domin ta kara shiryawa don ko duk warin girki take. Shiryawa tayi cikin wata chiffon blouse blue tareda wani palazo pant Wanda iya shin inta ya tsaya mata.
Wannan karan bata sa hula a kan ba sai dai daure shi da tayi in a low pony tail. Sai da ta kara yin wanka turaren kafin ta fita daga dakin.

Tana cikin sakowa taji kamshi turaren Omar ya gauraye wajan, dan lumshe idonta tayi ta bude su sai akanshi Wanda shima yanzu ya gama sauko, sound in takalmin ta ne ya mishi iso zuwa dodan kunen sa shi ya sa ma ya juya kanshi. Ganin ta tsaya yayi tana mai sakar mishi murmushi.

" good morning".

Murmushi ya sakar mata tareda amsa mata.

" breakfast is ready, naga kamar sauri kake " tace mishi.

" ina da aikine da ban gama ba " yace mata tareda bin bayanta don ya je ya ci abinci.

" yau ma ragewa yayi shi yasa aka min tayi " ya tsokane ta, domin ko da in ma yasan kawai fada tayi na ragewan nan amma ba wai hakan bane.

Murmushi ta saki sanin tsokanarta yake yi kafin tace mishi.

" A'a yau as a thank you ne for fulfilling our end of the deal, sauran dayan."

Murmushi da ke kwance a kan fuskar shi ne ya kau a lokacin da yaji abinda ta fada. Haka dai ranshi ba a dadi ba ya ci abinci, bayan ya gama kuma ya tafi ya barta da sakin baki da hancin akan halin nashi. To mai na dauka da zafi akan abinda ta fada. Wai ma tsaya, ta fadi wani abu ne da be kamata ba da zai dau zafi haka.

****

Shiga tayi cikin dakin shi, sanyin ac da kamshin turaren shi ne yayi mata iso, taga alama wannan kamshin ya rike dakin domin ko indai ta shigo cikin dakin sai tayi sniffing in shi. Ganin dakin na shi kaca kaca da kaya ne ya bata mamaki. Daman dazu yayi mata text yana mai rokon ta da ta gyara mishi dakin. Ai ita bata zata haka yake a hargitse ba kamar Wanda akayi fada a ciki.

Kaya ne akan hargitsatsan gadon Wanda daga gani ba ma a sasu ba, sai kuma papers da ta gani duk an dun kule su an yar, Zasu kai wajan goma in bai ma fi ba. Haka dai ta tashi ta dauke kayan ta mayarda su ma ajiyan su kafin ta hau kan gadon ta gyara. Dan wannan abun da tayi sai taji duk ta gaji, haka dai ta hau tattara papers in, tana cikin haka sai wata zuciyar ta fada mata ta duba ta ga mai a ciki kar kuma yazo yazama important abune ta zubar bata san ni ba. Deep down ta san bayanda za ayi in important abune ya yarda shi amma kuma curiousity won over her.

Haka ta dauki guda daya ta bude, abinda tagani rubuce shi ya daure mata kai. Ni Omar na sa.. sai taga ba a karasa ba wannan yana nufi shine yasa shi yarda paper tareda dungule ta. Har wajan guda shidda duk a nan rubutun yake tsayawa. Ana bakwan ne taga ya dan karasa amma ba har inda Taso ba. Ni Omar na saki ma... Toh mai hakan ke nufi kenan.

 AFRA Where stories live. Discover now