Babi na Sha Tara

918 109 2
                                    

3 months later.

A cikin wataninan bawani abu da a faru illa shirye shiryen bikin fake faruwa a kowani family. Yau dai sauran sati daya kafin a fara bikin nasu. Afra ce zaune a cikin bathtub, ruwan kumfa ne Wanda aka saka bath bombs a ciki, bata dade da akaga gama yimata gyaran jiki ba. Fatar nan tata ta kara haske sai sheqi take yi. Kanta daure yake akan head rest yayin da ta lula tunani.

Wai itace auran ta saura kwanaki, auren ma ba da Wanda take so ba. It sai yanzu ma taga wawtarta ta da yadda da batun Omar. Ko da dai tayi mata alkawari ai ba shine ya sa dole sai dmta aure shi zata samu ba. Zata ma iya biya ayi mata. Mai ma ya kaita har da yarda da shi.

Ita Allah na gani bata shirya yin aure ba, dame ma zataji, auran ko alkawarin da ta daukar wa kanta. Ita dai ba yarinyar ce karama ba, tasa mai aure, tasan kuma hokokin sa da zai hau kanta da zaran an daura. Ko da har cikin zuciyoyin su sun san ba mai dorewa ba, amma ai aure ya fi gaban wasa, ba yanda za ayi tace bazata sauke hakkin sa dake kanta ba, domin ko Allah zai kamata da wannan laifin.

Runtsa idanun ta tayi tana mai dan jin zafi da zugin da ke mamaye zuciyar ta. Sai yanzu take regretting. Regret in ma marar amfani tunda dai aikin gama ya gama, aure dai kamar an daura sai dai kuma wani iko na Allah.

Tashi tayi daga cikin tub in a lokacin da ta lura ruwan ya fara sanyi, gashi ma kuma karar knocking kofar da yar uwarta, wato cousin in ta Aroosa take yi ya cika mata kune.

Wrapping jikinta tayi da pink bathrobe in ta. Tare da wrapping karamin pink towel akan jikaken gashin ta. Fitowa tayi daga cikin bathroom in ta hango su Aroosa tare da sauran cousins in ta Wanda suke shekaru daya.

" at long last kin fito, ai da na zata sabon skin zakiyi changing"  suhaila ta fada.

Aroosa tare da suhaila cousins in ta ne ta barin mama, while saura matan guda uku kuma na barin babanta ne.

Aliya paternal cousin in ta ne ta charap ta saka bakinta tare da cewa.

" aikam dai nima na zata hakan " dariya suka sa bakin daya, while ita kuma Afra tayi murmushi. Wucesu tayi zuwa cloeset in ta domin neman kayan da zata sa. Wata light nude gown ta dauko tare da veil in shi ta saka. Gown in bata da wani ado apart from stones in da akayi aiki da su a ta wuya.

Koma wa tayi ciki da zauna cikin sauran cousins in nata, yayin da ta saka baki a cikin maganan su. Labari suke Wanda daga gani suna jin dadinshi.

" wai ni kam Afra, Yaushe kikayi watsi da wannan akidar taki ta sai kin kai shekaru talatin zakiyi aure" Sofiya ta tambayeta.

In ba za su manta ba akwai wani lokaci da suka hadu, a lokacin ma bikin wata cousin in su ce ,toh ananne ake maganar yin aure, ita kam Afra budar bakinta tayi tace ai ita bazatayi aure ba sai takai shekaru talatin a duniya.

Murmushi tayi batare da tace musu komai ba.

" ni ma dai tunanin da nake kenan"  zahida tace.

" daman a da din bata samu Wanda take so bane " Aroosa tayi replying.                  
" wai ma mai ya kawo kune wai" Afra ta fada domin ta fara gajiya da tambayar su.

Khadija ce wacce tun dazu bata sa baki ba tace.

" ke fa yar rainin wayoce toh daman muna bride's maid baza mu zo tun kafin bikin ba.  ".

Dariya Afra tayi tace .

" toh ai kune kun fara damu na da wasu stupid questions."

Labari dai sukayi tayi yayin da suke tsara yanda bikin zai gabata. Wannan kenan.

***
Aqalla sunkai mintuna uku bawanda yayi magana a cikin su. Kallon ta Asad yakeyi. Yanason ya furta kalmar dake kan lebben shi amma ya kasa.

" are you happy. " ya fada bayan ya samu damar futo da maganar da ke bakin shi. 

Kallon tambaya take mishi tana mai mamakin tamabayar ta shi. Is she happy .mai yake so tace mishi. Ta bude cikin ta ta ratatapo mishi regrets in ta Kome. Tasan Asad yanzu yana sanin dalilin yin wannan aure Wato kashin ta zai bushe, domin tasan komai sai ya zayana wa iyanan su.

So Kawai sai tayi Nodding kanta as an answer. 

" kuma bakai jin regret ko," ya kara jefo mata tambayar.

" eh banaji ". Ta amsa a dan sukwane, tana jin kamar Asad yasan dalilin yin auren nata. 

" that's good. Once again congratulations, I wish you a blissful married life. " yafada yana mai mika mata wani babban present da akayi wrapping da purple wrapping sheet.

Karba tayi, tana mishi godiya kafin ya tashi ya tafi. Daman kawo mata gift in ne yasa shi kiranta domin yanaso ya sabawa kanshi yin baya baya da ita domin ko in tayi aure kuma ba dole su koma kamar da ba. Wannan kenan.

***   
Hayaniya ne ke tashi a cikin gidan, duk inda mutum ya wuce mata ne birjuk a wajen. A yau ne ranar kamun Afra. Jiya akayi nasu Abida, an gayace dangin Afra ma sun je don kara. Zaune take a kan stool makeup artist monette beauty take tsantsara mata make up. Afra kam tayi kyau har da gaji. Daukar hoton ta monettebeauty tayi kafin ta saka kayan kamun ta.

Magenta coloured komole tasa wace deola ce tayi mata, kanta ma ashoke ne colourn kayan. Komolen ya zauna a farar fatanta yamata kyau ba karya, gawan gwal da ya yarfo har zuwa wajen cikinta. Gold in an yi shi ne kamar wata falls, dan kunayen ta ma hawa uku ne, ga wasu manya manyan bangles guda biyu a both hannayen nata. Dan madai dai cin zube ne na diamonds wanda Abbin ta ya bata as a present, zagaye a middle fingern ta. 

Madugu ne tare da BigH suke ta daukan ta hoton yayin da galleriafilms shikuma yake aikin daukan clips na video.  Fitowa tayi daga cikin dakin ta tare da kawayenta. Suma kawayenata sun yi kyau har sun kaji. Sanye suke da wani exclusive Atampha purple and white mai silver embelishment a jiki. Kowace sanye take da fashion earrings da necklaces in su.

Wajen balcony da ke saman gidan su Afra a kayi directing in su suje. BigH ne ya fara daukan su pictures wani ya dauka da amaryar wani kuma yayi tare da kawayenta. Bayan an gama kashe su da hotunane kuma galleriafilms yafara nashi. Wani clip in sawa yayi Afra tayi rawa while friends into suka fara hailing in ta. Aikam daman gata yar rawa,haka tafara bese a hankali tana yin shi da class, bayan ya dauka ta ne ya ce sauran su shigo su fara nasu rawar. Aikam sun cashe sosai ba karya, kuma dai duk ba laifi sun iya rawa. Wannan kenan.

______________________________________

Not Edited.

This is all for today, hope you'll enjoy it.

Vote, share and comment
      

 AFRA Where stories live. Discover now