Babi na ashirin da uku

976 120 2
                                    

The next day.

Karar alarm in wayanta ne ya bata daman tashi, duba wayan tayi taga 5:06, mika tayi tareda furtar addu'ar tashi daga bacci. Dakin da duhu don haka sai ta kunna torch light in wayanta. Still da kwai dan ragowar bacci a jikinta don haka, ba zata taji ta bugi wani abu.  Hannu taji ya rike mata waist inta domin steadying inta kafin ta fadi.

Tsigar jikinta ne taji ta tashi tareda qaran sautin bugun zuciyar ta. Ita duk tunanin ta bai kai mata akwai wani a cikin dakin ba. waye wannan Wanda ya ke rike da ita, wani tsoro ne da furgici ya mamaye zuciyarta, addu'a tafara yi tana mai kiciniyar kwacen kanta daga rikon da mai hannun yayi mata. Ita shaf ta ma manta da wani Omar balle ma ta kawo ko shine tayi karon da.

" ke calm down " wannan muryar tashi mai taushi da daddadan sauraro ne ya bugi cikin dodon kunnenta.

Tsayawa tayi na yan sakwani kafin tace.

" let go of me ".

Da fadar ta da sakinta duk a lokaci daya ne ya faru, domin shima ko bata fada ba yayi niyar yin hakan. Juyawa yayi ya bata baya yana mai tafiya zuwa kofar da zata sada shi da waje, daman shigowa dakin yayi, yayi wanka,  ya shirya, duba da daman ba a dakin ya kwana ba. A hanyar shi ta fita ne ya kuna lights in, aikam dakin ya dauki haske.

Ita dai Afra abinda ta iya gani keyarshi ne kafin ya fita daga cikin dakin, yana mai kullo kofar bayan fitan na shi. Shrugging tayi, ta shiga cikin bathroom in. Wanka tayi tareda da dauro alwala kafin ta fito. Shiga cikin closet in tayi ta dauki wata dogowar Riga ta floral fabric ja mai manyan flowers da akayi musu kalar baki ta sa.

Fara bude drawers tayi tana neman hijab, a na karshen ne ta ganshi tareda abin sallah. Dauka tayi ta fito dakin, tsayawa tayi tana tunanin inda qibla take, gashi shikum wancen ya tafi ma bai fada mata ba. Ajiye praying mat tayi akan Ottoman, kafin ta dauki wayar ta, ta shiga cikin Muslim pro domin duba qiblar.

Inda app in yanuna mata qibla nan ne ta shimfida mat in kafin ta tada kabarar sallah. Sai da tayi nafila kafin ta kawo farillar. Tana idarwa kuma tafara sabah inta, sai da ta kai karfe shida da wasu mintuna a zaune, tana su zikr da karatun qurani.  Shiga tayi cikin call log inta ta nemi number suhaila domin ta kirata, don ko Afra a cike take da su. Wato ko su kira ta ma suji inda take, in da ma kasheta akayi ko saceta ba za su damu ba.

Ringing biyu wayar tayi, suhaila ta dauka tareda da sallama a bakinta. Amsa mata Afra tayi kafin tace.

" kun kyauta kunji, nagode, ko ku kirani ma kuji inda nake. "

Dariya Suhaila tayi tareda da bata amsa.

" afwan ukhty, taya mata tana tareda mijinta zamu damesu , ko so kike Omar ya haramta mana ganin ki ".

" mai kike nufi ".

" toh ai munsan tareda shi kike so mai afanin kira naki. Toh ya amarci"

Dan tsaki Afra tayi tana mai kauda zancen nata.

" ya kuke, ya su aroosa. "

" hmm duk Muna lafiya. Ya mijin naki".

Dan jim tayi tana so tace wani abu amma sai ta fasa, tareda da amsata da.

" ya na nan Lafiya ".

Dan labari sukaya na yan uwataka kafin ta kashe call in. Kiran Ummi tayi wace ta dauka suka sha hirarsu irin na ya da Uwa kafin ta kashe wayar. Jin bacci na idanunta ne yasa ta koma ba tareda ta dubo ko Omar na nan ba ko bai nan. Wannan kenan.

****
Fita yayi daga gidan tareda da shiga motarshi.  Sojoji guda hudu masu mishi gadine a wajen gate, suna ganinshi suka taso domin bada gaisuwa.

Amsa musu yayi tareda basu umarnin komawa wajen gate domin bai da niyar fita da su, kuma ma ai bai kamata ya bar yar mutane ba security ba.

Danna remote na gate yayi, Wanda ya bawa gate in daman bude wa. Fita yayi daga gidan tareda da dannan wani jan remote Wanda ya mai da gate in ya rufe ruf. Tuki yake yi a kan gargadar nan, yana jin speaker masalatai na fito da sautin kiran sallah. Tafiya yayi da bata fi mintin uku ba ya isa wajen wani karamin masallaci da ake kiran sallar fajr. Parking yayi kafin ya fita yaje wajen da wasu mutane suke suna alwala.

Gaisawa yayi da su kafin ya karasa shiga cikin masallacin. Babu laifi masallacin a gyare yake amma yana needing kwaskwarima gaskiya. Take wani tunani ya shiga ranshi, bari yayi sai da akayi sallah kafin ya sami limamin. Dan tautaunawa sukayi da limamin kafin ya fita da ga masallacin.

Shiga yayi motar shi, yana mai isa kan kwaltan da zai fito da mutum daga millennium city. Tafiya yake yi yanda ya saba a hankali, har yanzu garin bai gama yin haske ba. A haka har yakai wajen da intelligence division yake, Wanda ke Kusa da gidan lord lugard.

Tsayawa yayi a gefan wajen kafin ya dauki wayar shi ya kira Sidi, ringing daya yayi sidi ya dauka.

" Good morning sir ".

" morning, kuna tareda Sam ne ."

" eh, sir gamunan da shi".

" toh ku fito ina jiran ku " ya fada kafin ya kashe wayar.

Ba'a fi mintuna biyu ba suka fito daga cikin wajen suka iso inda yayi parking. Gaishe shi Sam yayi, ya amsa mishi kafin ya basu izinin shiga cike. Tafiya ya fara yi ko ina ya dauki shiru, tafiya mai nisa yayi kafin su iso dan kande. Anane su Sidi suka fara mishi kwatance gidan kashe ahu dake ta barin nan. Wajen a wani lungu yake da in mutum bai sani ba bazama ka taba sanin akwai wani gida a wajen ba. Gidan dai makeke ne na gaske har ma yafi Wanda Afra ta je wance karan. Parking motarshi yayi da dan nesa da gidan kafin ya fito yana mai bawa su Sam izinin su fito.

Sai kuma a yanazu ne na kare mishi kallo naga ashe yayi disguising kanshi, suma su Sam duk sun sa disguise, although duk bakin kaya suka sa Wanda aladar wajence saka bakin kaya.  shi Omar wata baggy hoodie ce jinkin shi, ya saka hula ta kullo wajen rabin fuskar shi, daman kuma ga snap back in da ya saka a kanshi, su kuma su Sam duk gemun karya da gashin baki na karya suka saka tareda da kifa beanie akan su, ga wasu glasses bakake da ke fuskar su Wanda ya kulle kalar idanun na su.

Gidan Kashe ahu dai gidan ne na karuwai, in dai mutum na neman karuwa first class toh ya zo gidan kashe ahu. Su karuwan wajen ma ba kowane kalar mutum suke kulawa ba in ba sun ganshi da kudi ba. A gidan kashe ahu har karuwan maza ma akwai, Wanda manya manya tsofafin hajiyoyi suke amfani da.

Gidan dai akwashi a waje biyu ne, na wajen sabuwar kaduna da kuma na wajen dan kande, kuma dai from intel in da suka samu Salim ne mai wajen, kuma ma an ce ya fi zama a wajen na dan kande a dalilin nan ne headquater kuma ma sun fi samun customers a wajen domin ko ya fi na sabuwar kaduna sirri. Wannan kenan.                        

************************************

Kuyi hakuri ban muku typing da wuri, latafine ba a rubuce yake ba so sai idea ya zo min nake iya samu daman rubutu amma zan kokarta in dan ringa yi da wuri.

Vote, share and comment.

 AFRA Место, где живут истории. Откройте их для себя