Babi na tara

1K 139 1
                                    

Sai da suka dauki yan sakoni suna kallon juna kafin Afra ta dawo hayacinta ta dauke idonta daga nashi wanda shima a bagaran shi hakan yake. Abinda Abida da Afra basu taba zata bane suke ji ya amsa gaisuwar tata har da tambayan ta ya makaranta.

Amsa mishi tayi da " Lafiya " a taikace kafin ta juyawa kawarta wace ke jifan su da alamar tambaya. Tana lura da duk wasu moves in su, toh ko dai sun san junane ta tambayi kanta, amma kuma tasan mutanen nata kowa da dan gutun girman kanshi ko sun sani ma ba nuna wa zasuyi ba, amma dai tabbas akwai ayar tambaya a Kallon da sukayi wa juna.

Juyawa Afra tayi bayan tayi ma Abida sallama zata koma inda suke amma sai taji Aibda takira sunanta, turning tayi ta kalli Abida yayin da ta daga mata gira daya in a questioning way .

" ya faruq yace wai kizo mu sauke ki "  Abida tafada tana Kallon kawartata a ido domin ganin reaction in ta.

Abinda yasa Omar yasan da daukar ta driver zaiyi shine Sabida a lokacin da ya kaita, mamarta ta umarce ta da tabasu waje su dan gana da omar domin ta fahimce akwai magana a bakin shi, toh shi yayi wa ummi bayanin in da ya hadu da ita har abin ya faru kuma ya ba da shawarar anemo mata mai kaita don nan gaba ba'asan ina zata iya jefa kanta ba.

Haka kawai tun haduwarshi da yarinyar yaji yana jin wani overprotectiveness akanta, jinta yake kamar Abida even though ya lura tana da tsiwa.

" a'a da ya barshi don na rigada na kira....." ai bai bari ta karasa fadan abinda zata fada ba ya hade rai tareda cewa " get in " yayi anfani da kanshi yayi gesturing tashiga cikin motar.

Hade rai tayi taso tace a'a amma Sabida darajar Abida, don kartaga ko ta raina mata yaya ne yasa ta bude back seat ta shige tare da kullowa. Murmushi mai ma'anoni da fassara Abida tayi kafin ta shiga motar ta zauna a seat in gaba.

Tukin nan nashi yake yi wanda kamar bai da wajen zuwa while Abida da Afra suna ta chatting a waya.  Abida na tambayar ta ko daman tasan ya faruq in ne amma sai tace mata bata sani ba, karasawa dai suke da chatting ta wayar ba mai cewa komai sai dai karar ACn motar da na inji ta ke tashi.

Maida idonshi yayi zuwa ga mirror ya ga sai murmushi take tana Kallon wani abu a wayarta . Furrowing brows inshi yayi kafin kuma ko mai yatuna naga ya mayarda hankalinshi kan windshield in.

Wanna abinda yayi kuwa akan idon Abida, abin na suma ita har ya fara bata dariya, ita Afra tace bata sanshi ba, ita kuma ta lura da yayanta, akwai sanya tsakaninshi da Afra a idanunshi. Toh mai hakan ke nufi kenan tayi ma kanta magana. Sanin bazata sami answer da take nema bane yasa kawai tabar abin a zuciyar ta domin tasan ma kawai inta damu ma ciwon kai zata sama kanta.       

Ita kuma Afra abinda ya sa tayi karyar cewa bata sanshi ba shine tasan in tace ta sanshi to Abida zata so jin a ina ita kuma gaskiya bazata iya fadamata ba don min tasan Abida in dai taji dalili to zatace zata taimaka mata ita kuma bata son sakan wani acikin wannan matsalar. Wannan kenan.

**********
" ya Faruq ya naga kayi hanyar gida ka manta zamu sauke Afra ne " Abida tayi mishi tambayar ayayin da taga ya karya kwana zuwa unguwar su.

Jijiga kanshi yayi yace a taikace  " ban manta ba, sauri nekeyi akwai abinda zanyi ne, in na gama sai in maidata ".

Shiru tayi batace komai ba ita kuma Afra tacika tayi pam da haushi abinda yayi take, da yasan yanada wajen zuwa ya daukota ko da ma yayi ne don ya musguna mata don ta lura ba wani mutanci ne dashi ba.

****
Maska Estate.

Welcome to maska estate ne a rubuci a saman gate in estate in. Afra tayi mamakin ganin unguwa guda ne Abida take cema family house, toh dama dai ita Afra bata taba zuwa gidan su Abida ba dalili kuwa shine ko fita zasuyi sai dai su hadu a waje kamar su zuwa Kallon polo ko kuma zuwa restaurant aci abinci so ita bata taba kawowa wai estate guda ne gidan su ba.

 AFRA Where stories live. Discover now