Babi Ashirin da biyu

1K 103 3
                                    

Tafiya mai dan nisa ne ya sadasu da event hall in da ke a karje. Suna isa Omar yayi parking motar a ta dan baya wajen ba wasu mutane amma kuma bawani light a wajen. Ta gefan idonta Afra take kallon Omar tana so ta mai shi tambaya amma ta kasa. Mai yasa bai bi sauran ba mai yasa yayi parking a ta wajen baya hall in.

Kashe injin motar yayi amma instead of taga ya fita sai taga yayi shiru, shi bai fita ba kuma shi baice komai ba. Kallon shi tayi taga mai yakeyi sai taga ita yake ma kallon. Narrowing eyes inta tayi tareda cewa.

" it's rude to stare. ".

Murmushin gefan kumatu yayi kafin ya ce.

" when it doesn't not belong to you. Kefa a idon jama'a fa you are mine, just like I am yours " sai kuma ya tasaya yaki karasawa.

" mai yasa kayi parking a nan " ta kalli wajen tana dan yatsina fuska.

Bude murfin kofar yayi ya fita, kule wa yayi kafin ya karaso ta gefanta, ya bude mata. Fitowa tayi tana mai sun furta wani abu amma ya riga ya fara janta zuwa inda take hango sauran yan tafiyar nasu.

" Afra, finally tunda aka fara bikinan sai yau muka hadu " Abida ta fada tana mai hugging Afra.

Itama Afra hugging inta baya tayi kafin tace.

" aikam dai." 

Gaisawa tayi da sauran amaren kafin a jera su domin su shiga. Mutum dayan ne Kawai bai zoba shine uncle H ,shi kuma yace bai zai yi event tareda yayanshi ba so shi nashi a wani hall in ne kuma wasu daga cikin family in su sun halarci nashi even though sun fi yawa a nasu Affan.

Su Affan ne da Abida suka fara shiga sai Hafiz da hauwa sai kuma Alamin da sadiqa, su Omar ne akarshi wannan kuma ta dalilin Omar ne domin shi yace yana so su shiga a karshen.

Rike hannunta yayi gam yayinda suka fara tafiya cikin hall in. Yan kawayenta dai da abokanshi sai tikar rawar suke, daman gasu soldiers kuma dai kunsan yanda sojoji basuda kunya, hakan kam sukayi ta leg work da su bese. Kowa wajen sai da suka birge su domin kam sunyi entertaining in su.

Cikin hall in cike yake da mutane maqil har ma wasu ba su sami wajen zama ba. An kawata wajen da purple and black light, ambiance in wajen is superb. Karasawa sukayi wajen da aka tanada domin zaman su. Jira yayi sai da ta zauna kafin ya zauna a gefan ta. Dan matsawa Afra tayi ganin yanda ya matso daf da ita ya zauna ganin kuma kujerar ba wai karama bace.

Yana lura da ita amma sai yayi birus kamar bai sani ba, amma wasu tunanuka suna ta yawo a qwaqwal wanshi. An fara program in da addu'a kafin a gayyato ali jita yazo yayi waka.  Bayan ya gama ne yan rawar suka zo sukayi, sai kuma aka kira kawayen amaren su zo suyi rawa, nan ba wacce aka barta a baya domin ko duk sun nuna bajintar su, yayin da galleriafilms shi kuma yayi ta daukan su.

Bayan haka ne aka kira angwayen daya bayan daya su fito suyi rawa da amaren su. Once again su Omar ne a na karshi. Da lokacin first dance in su yayi, da Afra kin tashi tayi, amma jin ya tashi kuma yana kokarin tashin ta yasa ta tashi itama, wajen dance floor in yayi leading inta.

Tayawa sukayi yayin da wakar ed shareen take tashi, bawanda yayi motsi a cikin su. Ita Afra ba wai tana jin kunyar yin rawa a gaban mutane bane Kawai dai ta tsinci kanta ne da kasayin rawa. Ganin sunki juyawa ba kamar sauran ba Wanda suka dan taka ba laifi. Mc in ne ya zo yana zungurin Omar tare da.

" oga this is your first dance, abeg make un show madam some love nahh " .

Dan murmushi Omar yayi kafin ya dora hannunshi akan waist in ta, jawota yayi jikin shi Wanda inda tsawon su daya ma hancin su zai na gogan na juna. Draping hannayen ta biyu tayi akan kafadar shi yayin da suka dan fara juyawa. Suna cikin rawar ne idanun ta yayi mata tozali da wani abunda ya sa ta tsaya cak na wasu yan sakonin, tun Omar bai gane ba har ya ganota domin jikin ta ya fara shaking.

 AFRA Where stories live. Discover now