Babi na shida.

1.1K 109 5
                                    

Juyowa sukayi shida Abdullah yayin da idanunsu yayi artabu da nata. Zuciyarshi ce ta bada wani sautin bugu kafin gashin jikinshi ya fara tashi. Kodai yayi gamo ne, tunanin ne yazo mishi alokacin da tsigar jikinshi ya tashi, domin ko yaji ance in suna kusa yana iya janyo haka.

Ayatu kursiy ya fara karantawa a hankali yayin da ya tsaya kare ma yarinyar kallo. kallon yan sakwani yayi mata kafin ya dauke idanun shi daga ita don haka kawai yake jin bugun zuciyar shi na qaruwa sabida kallon kwayar idanun ta da yayi.

Afra Allah yayita da baiwar kyawawan idanu da indai mutum ya kale ta sai ya so kara kallon ta, kalar idanun ta grey ne wanda suke iya canjawa a duhu suzama baki.

" Sannu ko " Abdullah yayi magana don ya ga Abokin nashi bai shirin yin magana ba.

Daga kanta tayi mishi kafin tace "Yauwa, don Allah ina ne nan " ta fadi haka ne a dan daddare domin haryanzun tunani take ko Salim ne ya kamata ya kawota nan gidan da take.

" Gidan yankan kai ne " Umar ya fada sarcastically. Fuskar nan tashi a harde kamar hadari. Dan tsorata tayi da batun Wanda yayi sanadiyar sata motsawa har ta kunsa fadi kasa, Allah ya so Abdullah na wajen yayi saurin tarota kar taje ta jima kanta ciwo.

Hararar Umar yayi kafin ya koma kan Afra. " kar ki damu da wancen, haka yake, yana da dan tabin hankaline" ya ce yanason bawa Umar in haushi. Aikuwa Umar ya ji haushin don ko wani harara da ya sakar ma abokin nashi sai da nayi zaton zubewa manyan idanun nashi zasuyi.

Shiko Abdullah ko a jikin shi, sai ma bata hakuri dayayi kanna ya fada mata dalilin zuwanta gida. Jin jina kanta tayi yayin da abin da ya faro awowi da suka Wuce ya shiga replaying a mind in ta. So dama wannan ne dalilin ciwon da ta ji kenan, ciwon da ta ji a bayanta ashe ta sanadiyar faduwar da tayi ne, Allah ya so ma ba abinda ya samu bayan nata. Hamdala tayi da kawai minor injury tasamu a goshin ta Wanda yayi sanadiyar sata dan ciwon kai, hakazalika tana kuma jin dadin tsere ma Salim da tayi, bataso ma sun hadu ba, ita ana ta tunani bazai gane ta ba in tayi baddabami ashe shegen zai iya, amma fa tayi underestimating in shi duk da daman ance mata shegen na da kwakwalwa, kuma da wuya in ya ga mutum so daya ya kasa gane shi a karo na biyu.

" na gode amma don Allah ina nake, kuma karfe nawa " ta tambayi wanda taga yafi mutunci a cikin su.

Duba wayanshi Abdullah yayi ya fada mata time, wanda a lokaci daya ta dibibice, hankalinta yayi mumunan tashi, ya akayi tayi dare haka bata koma gida ba, yanzu tansan in hankalin Ummi yayi dubu ya tashi.

" La haula, don Allah ko zan iya samun abin hawa a kusa " ta kara mai tambaya yayin da ta tashi daga kan lallausar kujerar da aka kwantar da ita a kai, sai yanzu ta kara yi wa parlourn kalo don wacen karanma a magagin ciwone take kale kale.

Parlourn ya hadu iya hadu domin kuwa a wani barin tun daga sama har kasa glass ne wanda zaka iya hango wajen duk da dai yanzu dare ne kuma akwai fitilu a parlourn hakan ne yasa bata ganin wajen. Fararre kujerune guda biyu da kuma wasu loveseats guda biyu masu ruwan kasa, kai tsayawa ma kwatanta kyan parlour is a waste of time amma ya hadu iya haduwa. Toh shikuma wannan waye tayi tambayan a zuciyan ta koda dai ta saba ganin wajaje masu kyau amma dai irin ginin nan akasarnanne bata taba gani ba.

Tashin da tayi ne yasa hankalinta ya je ga mayafin abayarta dake ajiye akan centre table da kuma wig in kanta wanda ke nuni da ba komai kenan akanta, hannu takai kanta don tayi confirming aiko sai taji ta taba lallausar bakin gashin ta. Sukuwa kusan mutuwar tsaye sukayi barin ma Umar, lokacin da ta tashi a lokacin ne kuma dan elastic band in da ta kama gashin ta da shi ya tsinke wanda yayi sanadiyar sakin dogon gashi nata wanda ya kwanta a gadon bayanta, ganin kallon da suke mata ne ya fargar da ita tayi saurin surar mayafinta tayafa akanta, Umar dai kamar ya ce karta kule sai kuma fa ya tuna ba muharammar shi bace. Yar gyarar murya Abdullah yayi kafin ya fara magana.

" ni a nawa ganin da kin bari gobe tayi sai ki koma gida, don yanzu dare yayi kuma samun abin hawa ma zai yi wuya ".

Idanun tane suka fara ciciko da hawaye yayin da ta fara girgiza kanta. " don Allah ni dai ko ba rickshaw ko dan babir ne ma na samu babu komai, don wallahi nasan yanzu Ummi hankalinta a tashe tana chan tana jiran dawowata".

Harara Umar ya aikamata kafin yace " da kinsan bakison tashin hankalinata kika baro gida kika je yawonki ".

Wani kallon ta wurgeshi da shi Wanda ita kanta batasan irin kallon da take aikamishi, ita dai tasan inda yana kisa toh da tarigada ta kashe shi. Wai shi wane irin mutumne ma ya buge ta babu bada hakorin kuma yanzu yazo yana gayamata maganar banza, toh ina ma ruwanshi da daga inda tafito.

" toh ina ne gidan naku " Abdullah ya tambaya, domin ko yarinyar ta bashi tausayi kuma tunda yaga so take ta tafi gwanda ya kaita tunda daman a hanya yake. Kwatancen gidansu tayi mishi wanda ya sa ba shikadai bama har Umar sai da sukayi mamaki, domin kuwa yawancin kowa yasan gidansu duba da mahaifinta Attajirine kuma dan kasuwa ne so duk abokan aikinsa suna yawancin haduwa da shi a gidan sa, suma su Abdullah abinda yasa suka san gidan sabida suna da share in da suka siya a companyn shi na sarafa karafunane shiyasa ma suka sanshi. Toh tana yar Alhaji Muhammad safana mai ya kawota irin wajennan, kuma ma ita kadai shine tambayar da suke wa kansu.

" Ayya kice ma kanwar muce, ai nasan mahaifinki, mutumin kirki " Abdullah ya fada yana dan mata murmushi.

Itama din murmushi ta mayar mai da. Excuse ya dauka kafin ya je ga abokin shi da ke tsaye kikam sai kace soja ko da yake ma a sojan ne. Shi dai Umar Allah yayi shi da bala'in son gashi, shidai mace ko batada kyaun fuska in dai tana da gashi toh zai yaba, bawai kuma yana nufi zai so ta bane don shi a rayuwarshi ma be taba son wata ya mace ba duk da yammata nasan shi kuma ba laifin yana kula wasu domin kuwa yana respecting mace. A nashi mace mai rauni ce kuma in har kace da zafi zakayi mata toh kuwa zai kawo raini, amma ka lalaba su ku rabu lafiya yafi yin jan ido.

Apart from kaninshi mata da yake dan wa fada in sunyi ba daidai ba toh sai Afra, ita ce mace ta farko da zata iya mishi shaida da zama marar mutunci. Jawo shi Abdullah yayi suka dan matsa daga inda yake kafin Abdullah ya fara magana kamar haka.

" Abokin na jimana " .

Harara ya buga mai don haryanzu yana jin haushi kiranshi mahaukacin da yayi. Amma dai sai yayi deciding yaji da abinda ya zo.

Magana sukeyi amma daga gani kasan arguing suke, duba da yanda Umar yake motsi da hannayanshi in a frustrated way, kuma ma hararar da yake aikawa Afra dashi, wace take a dan nesa da su though bata jin abin da suke cewa ma, kawai dai tana iya hango motsin bakin Umar wanda shine ke facing in ta, while bayan Abdullah ke kallon ta. Itama harara take mayar mishi duk da dai bata san ba'asin nashi hararar ba amma nata kuwa ya kunshi abubuwa da dama, acikin su akwai na buge ta da ya kusan yi da motar shi amma ko ya jiki bai mata ba, na biyu kuma rashin mutuncin da ya mata alokacin da ta farka tana tambayar inda take.

Sai da suka dau mintuna suna muhawarar su kafin daga bisani taga Abdullah yayi hugging Umar kamar dai godiya yake mishi. Juyo da hankalin su sukayi wajen ta yayin da Abdullah ya fara takowa izuwa wurin da take a tsaye.

" kiyi hakuri mun bata miki lokacin ko, Ki shirya Umar zai kaiki " ya fad'a mata tare da dauko blonde wig in ta da ke kan saman centre table in. Hade fuska tayi Wanda ke nuni da bata ji dadin maganar ba, taya ma za aci wannan mara mutuncin ne zai kaita gida.

Lura da yanayi fuskan ta ne ya sa Abdullah dan matsowa kusa da ita " kanwata kiyi hakuri ki bishi, ni gidana ba ta nan yake ba da na kaiki kinji "

Nodding kanta tayi tareda da karbar wig in da ya mika mata. Bin su tayi abaya har suka fita daga gidan, mamaki ne karara a fuskar ta yayin da tayi artabu da dajin da ke zagaye da gidan, daman bata bar unguwan ba ashe. Tawajen wani stone pavement suka bi, wajen ya qawatu da shrubs tare da qananan lightens da suka haska wajen binsu take a baya yayin da ta lunstuma tunani halin da mahaifiyarta take ciki.........

__________________________________________________________________________________________________________________

Koyi hakuri na dade banyi posting ba, karatune ya hanani amma zan rinka kokarin posting in na samu time.

Now enjoy .😁

 AFRA Where stories live. Discover now