Babi na Ashirin da Shidda

962 112 0
                                    

Kwance take akan jikinshi, sai shagwaba take faman yi mishi shi kuma yana biye mata. Abidace kwance a kan cinyar Affan, jikinta  rufe yake da wani farin throw blanket, zazzabine ya rufeta tun daren jiya, har yanzu kuma yaki sauka. Affan yayi yayi da ita ta barshi ya kira likita amma taki, wai ai zai sauka ne.

" amma baby haka zan tsaya dake, baki ji jikinki bane. Ya fa yi zafi " Affan yayi maganar a lokacin da yake taba yuwan Abida.

Noke kafadarta tayi tana shaking head in ta. " ni fa ba wani zazzabi dake damuna, kuma ma ai kai ka jawo"  tafada a shagwabance, tana pouting lips inta.

Dan dariya yayi da jin zanceta, yana mamakin ragwancin irin nata.
" toh ai na bada hakuri ko ".

Dan harara ta aika masa tana mai dan dukan kirjin shi. " wato kai dariya ma  kake yi. Banda Lafiya amma ko a jikinka ".

Sakar baki Affan yayi yana mamakin furucin ta, wai matar da ya gama ma magiya ta bari a kira doctor shine zata ce bai damuba, kai mata dai halinsu sai su.

Suna cikin haka ne, door bell na gidan su ta fara qara. Mamaki duk sukayi na waye ya ke dannawa da wannan lokaci, sabida kusan tara yanzu, ai in ma su zuwa ganin amarya ne yanzu yayi safiya da yawa.

" Baby barin je in duba in ga waye ."

" toh sweetheart"  taya ta tashi yake son yin, amma sai jin sallama sukayi daga kofar shiga parlor, muryam Omar ce ta daki kunnen su, ashe mai aikin su taji lokacin da yake danna bell so taje ta bude mishi.

" wa'alaikumus salam yayanmu shigo " Affan ya bashi izini.

Sai da aka dauki wajen sakoni kafin ya shigo. Shi aladar Omar in dai zai shiga waje toh sai yayi sallama kuma ko an bashi izini sai ya dan jira kafin ya shiga sabida bai san a wani hali zai sami mutum ba.

Gaisawa sukayi da abokin nashi kafin Abida ta gaida shi. Ganin Abida da yayi a kwance kan cinyar abokin nashi, dan tabe bakinshi yayi yace.

" wannan kuma fa, ta wani kwanta kamar kyana wanki ".    

Dariya Affan yayi while ita kuma ta dan fara shure shure, tana shuno bakinta.

" kai ya Faruq yanzu banda Lafiya ma ko kayimin ya jiki shine kake min tsiya ".

Take fuskar shi ta dan canza zuwa ta damuwa. Shi a rayuwarshi ya ki jinin ya ga yan uwan shi ba Lafiya, duk sai ya sa ya shiga cikin damuwa.

" bakida Lafiya ne, mai yake damun ki " ya fada a hankali with a little bit of kulawa a maganar shi.

" zazzabine yake damun ta tun dare, yanzunan da kazo ma so nake ta barin in kira doctor ya duba ta amma taki ".

Kallon Affan, Omar yayi yana dan mamakin furucin shi amma bai ce mishi komai ba sai dai yace.

" ai Abdullah na hanya, in ya iso ya duba ta ".

" yauwa yaya ina aunti nane " Abida ta tambaye shi domin sanin Lafiyar kawartata.

" tana nan Lafiya ".

Tashi yayi daga kan kujera tareda cewa.

" barin ta fi daman na zo ne ka raka ni gidan su zawjati gaisuwan surukai, amma tunda baby sis ba lafiya, a kulan min da ita " yace yana kallon abokinashi.

Abida murmushine Kawai kwance akan fuskarta, tana mai jindadin yanda yayanata yake nuna kulawa ga matar ta shi, tun ba yau ba ta lura da kamar fa yayinta ya na son Afra, ita dai kawartatace bata sani ba ko tanasan yayan nata ko akasin hakan.

" yaya ai naji sauki, ba sai ya tsayaba, daman anjima ina so na je wajen su kaka Alhaji ma. Kawai ku tafi. "

Nodding yayi yace ." Toh Allah ya kara Lafiya, "  sannan ya kali abokinshi yace " sai ka fito". Wannan kenan.

 AFRA Where stories live. Discover now