Babi na talatin da biyu

1K 117 5
                                    

Kaduna.
Maska Estate.

Parlorn Kaka Alhaji cike yake yau makil babu masaka tsinke ma. Dika immediate family na Maska sun halarci wannan sudden meeting in. Kaka Alhaji da matayanshi ne zaune akan three seater, Abul bait, daddy tareda Abbi kuma suna zaune waje daya. Asiya wato Ummi mahaifiyar Al amin ita kuma tana zaune a dayan kujerar one seater. Sukuma matayen su Abul bait suma a gefan Ummi suke zaune akan wata doguwar kujera da zata iya daukan mutane biyar. 'Yayansu kuma duk zazzaune suke a kasa. Uncle H shima ya zo da matarshi Amina wace take zaune Kusa da su Abida, su Yaya huzaifa, Affan da dai sauran mazan gidan duk a Kusa da iyaye mazan suka zauna, su kuma su ya Bilkisu da sauran a tawajen iyaye mata suka zauna. Wa'enda basa wajen Kawai jikokine Wanda aka barsu tareda da masu aiki.

Duk sun zauna wajen ya dau shiru, sai dai kawai wasu dasuke zulumun dalilin wannan meeting in. Kallon duka yan parlorn kaka Alhaji yayi yaga ba mutum daya a ciki. Amma kafin yayi tambayar inda ya ke, sai da ya umarti Abul bait da ya bude taro da addu'a. Wajen yayi tsit kawai addu'ar Abul bait ce ke tashi.

Gyaran muryan Kaka Alhaji yayi kafin ya fara kamar haka.

" nasan kuna cikin zulumin dalilin da ya sa na kira wannan meeting, amma kafin nan ina Omar da matarshi ".

Dan shiru akayi, yawancin mutanen wajen sai yanzu suka lura da bai wajen ma.

" ya samu tafiyar gaggawa ne zuwa Lagos Wanda aka turashi daga wajen aiki. " Daddy ya fada.

Nodding kaka Alhaji yayi yana mai son yin magana amma Inna tayi sauri ta ce.

" bawani aiki, sun dai koreshi da bakin halin su ". Duk mutanen wajen kacire Wanda suke wajen lokacin da abinda mama zalikha tayi, duk sai ta sasu a duhu domin su basusan mai ya faru ba.

" Inna mai kike nufi, wani abunne ya faru " Abul bait ya tambaya domin duk suna cikin duhu.

" shine dalilin tarakun ma da nayi " kaka Alhaji ya bashi amsa.

Nan kowa yayi shiru suna jiran jin abinda ya faru. Daya bayan daya kaka Alhaji ya zayyana musu abinda ya faru amma banda maganar da mama zalikha tafada akan Hauwa, domin yaga wannan bai kamata kowa ya sani ba, za dai su sameta ita kadai suyi mata magana. Daga masu sallalami sai masu cike da mamaki.

Abul bait ne ya kalli Umma yana mai maka mata harara, ita dai kunya ma ta hanata dago kanta balle taga hararar da mijinta yake aikamata.

Mommy (mamar Omar ) kam wani daci taji aranta jin wannan rashin mutuncin da aka yi ma surukartata. Tana mamakin irin bakin halin yan gidan. Gaskiya har ga Allah bata ji dadin abinan ba yanzu in iyayenta suka ji mai za suce, bata iya rike musu amanar da suka bata ba.

" wannan ne dalilin da ya sa daman na tara domin in ja muku kune, wannan yarinyar dai kusan daga inda tafito, tafi karfin wulakancin ku da na yayanku, abu na gaba kuma amana ce aka kawo mana don haka baza mu Zuba ido mugan kuna muzguna ma amanar mu ba."

" ku tabbatar wannan ne zai zama na farko kuma na karshe da zan karajin irin haka ya faru." Kaka Alhaji ya karasa.

Umma ce ta bude bakinta tareda cewa a kunyace.

" Alhaji ayi mana afuwa In shaa Allah irin haka bazai kara faruwa ba. "

" ya fi kam, don haka duk Kuyi wa yayan ku kashe de, domin abinda Omar yayi ma maryam kadan daga cikin abinda Omar zai iya ne, don haka tunka fin azo ana aibantamin jika don Kawai ya kare matarshi, Kuyi wa yayan ku fada " Inna ta fada tana mai yar harare harare daka gani har yanzu tana jin haushin abinda zalikha tayi.

"yauwa daman wannan ne dalilin da yasa na taraku. Don Allah a ringa hakuri da juna, in kuna wannan halin kuna tunani zuri'ar mu ta gaba zatayi zumucin da muke fata". Kaka Alhaji ya tambaya.

 AFRA Where stories live. Discover now