Babi na Ashirin.

902 108 1
                                    

Wurin kamu an gyarashi da kayan aladar wacce mairoAbdullahi ce tayi musu gyaran a wajen event centre mai suna silver sand wand zai iya daukan mutane dari shida ma. Aikam hall in a cike yake makil da mutane. 

Fitowa akayi da ita daga motar, kwayenta suma duk sun fito. Daman dan mintuna da suka wuce Wanda basukai minute uku ba Ummi ta shiga tareda tawagar qawayenta. A tsakiya aka tsaya da Afra, wanda su suhaila ne suka sata a tsakiyan.  suna rike da turaren Wuta, ana musu kidan kwarya yayin da suke takawa ciki. Shuma masu dauka hoto da video suna yi.

Shiga sukayi ciki, aka kaita inda zata zauna, kanta rufe da wani shara-sharan mayafi. Zama sauran kawayen nata sukayi a kasa a ta gefan hagu da damanta. Mc ce ta mace mai suna surkymata, ita suka gayato domin ta kyatar da su da barkwancin ta. Fara event in akayi da addu'a kafin aka fara in. Dangin agon ne aka gaiyata su fito su siya mayafin amarya domin a bude musu fuskar ta su ganta. Aunties in Umar ne guda biyu, tare da cousins sister's in shi biyu Bilkisu da khadeeja matan su Huzaifa da ya Muhammad, Aisha ma matar Abdullah tana wajen, tareda wasu mata yan uwansu suka fito suka je wajen da amarya da kawayenta suke.

Sauko wa suhaila, da  Zahida, da Aroosa suka suka iso inda suke.

" toh yanzu dai dangin ango suna so su san nawa zaku siyarda mayafin amaryar " mc ta tambaya.

Mika wa zahida microphone in akayi ta karba tana mai cewa.

" ga amaryamu da kunganta san kowa kin Wanda ya rasa. Muna son ku bamu 10 million ba wai don ba ta wuce 10 mill ba sai don Kawai muyi muku sassauci. ".

Ihu aka sake tareda guda ya circulating wajen. Microphone in da ka a hannu zahida ta mika wa mc while sukuma family ango suka fara tattauna wa a tsakanin su. Bayan wasu in mintuna ne auntin Omar mai suna Hajiya Asiya ta karbi microphone in tace.

" mun siya mayafin amma sai dai a kudi kalilan mai Albarka, bawai don amaryar tamu ba ta kai hakan bane.  Zamu bada miliyan uku ".

" kun yarda " surykmata ta tambayi kawayen amaryar.

Dan kuskus su suhaila sukayi kafin, Zahida ta karbi mic in tace " mun yarda " .

Murmushin manya Hajiya Asiya tayi tana mai mika musu wata envelope take dauke da check in kudi.

Karba sukayi aka fara guda. Nan da nan yan uwan ango suka garzaya zuwa wajen Afra da ke rufe da mayafin. Turaren mai dadin kamshi aka fara fesawa har sai da ya qare, guda na tashi ta ko ina, Hajiya Asiya ce ta bude fuskar Afra, a lokacin da idanunta yayi tozali ta fuskar Afra, a lokacin ne ta bude bakin ta tace .

" Mashaa Allah, sannu ki da shigowa gidan mu, yata".

Duka sauran ma suka ringa yaba kyaun da Afra tayi. Fara daukar hotuna aka ringa yi. Ita dai Afra nata tayi ta kakalo murmushi domin hutunan suyi kyau. Ba a jima ba kuma akayi sanarwar zuwan ango da abokanen shi.

Tashi Afra tayi, ta sauka tare da suhaila, fita sukayi daga hall in, wata bakar Mercedes ce parke a gaban su shiga sukayi motar taja, sai wani dakin da suka kama a wajen. Shiga ciki sukayi suka tarar da makeup artist in da suka kira tana zaman jiran su. Touches aka kara yi wa makeup in tan tareda da chanja lipstick in lebben ta zuwa nude colour.

Chanja kayanta tayi zuwa wata dogon riga mai peplum ta Hkg lace kalar ruwan gwal mai ratsin milk a jiki. Dauri akayi mata da dankwalin lace in tare da pinning long veil a bayan kanta. Kara feshe ta akayi da dolce sheriff humra in Amne. Take kamshi ya garwaye dakin.

Fitowa sukayi inda sukaga mota ce daban ke jiran su. Fitowa drivern yayi ganin Abdullah ne yasa Afra fadada murmushin ta. Gaisawa sukayi yana tsokanar ta da amarya kafin ya bude mata kofar baya ta shiga, ita kuma suhaila ta shiga gaban motar.  Kashin familiar turaren Omar ne yasata juyar da kanta gefan ta inda ta ganshi zaune idanun shi na a kule, sanye yake shima a dakakiyar shadda golden colour wace akayi ma aiki da milk zare. Kanshi kuma sanye yake da milk hula. Yayi kyau har ya gaji. Ita kanta Afra sai da ta yaba kyaun da yayi.

Dan bude idanunshi Omar yayi bayan motar ta fara tafiya. Tun shigowar Afra cikin motar, kanshin turaren ta ne ya bugi hancin sa Wanda yayi sanadiyar sa munfashin shi tsayawa cak, a rayuwar bai taba jin kamshi turaren da ya burge shi ba irin wanna. Lumshe idonun shi yayi yana mai shakar kamshi, kamshi da ya jefa shi cikin wani nishadi na daban.

Kallon ta yayi wace ita kuwa hankalinta bai ma wajen shi. Karemata kallo yayi a zuciyar shi yana mai yin hailala ga Sarkin da yayi wannan kyakyawar halita. Jin tsayuwar motar ne ya dawo dashi hayacin shi.

Fita yayi daga motar kafin ya je ta barin da Afra ke zaune, bude mata kofar yayi ta fito. Abokanshi ne su wajen shidda a ta wajen hall in. Suna tsaye sunata dan labarin su da kawayenta. Abin ya bata mamaki yanda suka saki jiki da su haka, ita dai ta san cousins in ta most especially aroosa ba wani sakin jiki take da maza ba amma yau wai har wani dariya take yi.

Yanzu kuma kawayenta da abokan Omar ne suka fara shiga, kafin ita da shi su shiga. Zama sukayi a wajen kafin a koma da event in daman a rigada an rabawa mutane abincin ci. Haka dai aka kwashi hour ana partying kafin a tashi da ga wacen. Wannan kenan.

******
Yau ne ranar daurin auren. Both gidan amaren da na angwayen a cike yake da yan uwa da abokan arziki.

Abida ce tare da Hauwa da Sadiqa zaune suke a cikin dakin da aka ware domin zaman su tare da kawayenta. Labari kawayen nasu suke basu game da kuma Afra da sukaje domin su basu sami daman zuwa ba.

" kaiii mashaaAllah yayi Omar is very lucky " Aliya ta fada. Wata yarinya da take gefanta ne mai suna rumaisa ta harare Aliya tareda yin tsaki.

Aliya ta dade tana son Omar amma bata samu chance ba. Daman tana daga cikin yammata da suke yi masa waya amma dai bata yi sa'ar samun kamshi ba.

" oho sai da a hararen ni ni ba zan ki fadan gaskiya ba " Aliya ta sake fada daman ta lura da hararan da Rumaisa ta mata.

" wai da wa kike ne Aliya " Safna, kawar Abida ta tambaya.

" ai ita ta san kanta, in banda rashi aji ma mace an nuna miki ba aso ba sai ki hakura ba amma ke har wani.kishi kike ".

Dariya Fadila wace duk a cikin kawayen amaryan take tayi tareda da ce. " Allah dai ya rabamu da san maso wani " .

Daman duk suna lura da take taken Rumaisa kuma sun gano son Omar in take, domin throughout daren Jiya a sukuku tayi shi ba walwala.

"Amin"  duk matan suka amsa amma banda Rumaisa da Maryam. Rumaisa dai kawar Abida ce kuma ta dade da son Omar amma kuma ita bata ma gaban shi.

Ita dai Abida ba abinda tace domin ta sha yiwa Rumaisa fada akan ta cire rai domin ita tasan Omar tunda bai nuna yana bidi ba toh ta hakura amma taki, har fada ma sukayi wataran akan hakan amma dai suka shirya, duk da dai ma Rumaisa ce mai nace ma Abida kuma ba don komai bane sai don tasamu Omar.

Wani zancen suka fara yi ana shewa ana tafi. Duk amaran sun yi ado cikin white lace dinkin Riga da skirt ya musu kyau ainun. Suma kawayen sanye suke da jan atamphar chiganvy.
Suna cikin zama labari yayi dadi Kawai suka ji guda suna jin an fadan daurin auren da aka gama yi a yanzu.

Amaran duk suka yi hamdalah tare da kawayen su. Wani hawaye mai zafi ne ya fara zubuwa Maryam. Wani bakin ciki ne marar misaltuwa ya mamaye ta ji take kamar ta kurma ihun bakin ciki amma ba yanda zata iya. Itama barin rumaisa hakan yake amma itakuma ta kuduri aniyar ko a ta biyune sai ta shigo. Ni kam na ce hmmm. Toh Allah ya bada sa'a. Wannan kenan.

************************************************************************



 AFRA Where stories live. Discover now