Babi na Sha Uku

1K 163 3
                                    

Zaune take a kan stool tana fasa turaren oud fazza a jikin kayanta. Sanye take a cikin da wani HKG lace kalar ruwan toka da ratsin silver a jiki, bubu tayi irin ta zamani wadda ta fito da kuruciyarta da kuma kara bayana kyawunta.

Dauri tayi irin na zara buhari, wanda gashin ta mai santsi da tayi parking ya fita yayi him a keyanta, ash mayafi ta yafa a yuwanta yayinda ta saka silver Fendi shoes in ta. Kallon kanta tayi a mirror taga ko akwai abinda tayi missing amma komai yaji.

Yau ba wani make up tayi ba, Kawai powder ta shafa sai dan lipgloss sai kuma kwali da tasaka a idanunta. Ba taso tayi wani heavy makeup ma da zai bama Omar daman tinanin ko wai ta ma damu da shi ne ko ta fara son shine zai sa tayi makeup in.

Ita dai Afra ma'abociyar makeup ce, duk da kyaun da Allah yayi mata bai sa ta ba fuskar ta looking so pale and dull ba, kullin ka ganta zaga ganta da makeup inta. Maybe don ta tashi taga mamanta nayi ne, domin Ummi itama ba bayaba wajen cin ado, kullin kafanta da yatsun hannun ta zaka ganshi zagaye da jan lalle, daman ga farar fata sai lallen ya fito da kyau yayi radau dashi.

Itama dai Afran baka rabata da lalle either bakin ko jan, yanzu ma hannuta zagaye yake da ja Wanda har yazama maroon sabida kamu, irin wannan Wanda ake yayi ne na cellotape ne a hannun nata.

Daukar wayarta tayi tareda fita daga dakin nata, a cikin parlourn tane taga an ajiye ladoji, turus tayi, tana mai mamakin yauwan ladojin amma ba ta tsaya duba abinda ke ciki ba sanin Wanda ya kawo su, sai Kawai ta karasa fita daga part in ta. Tafiya mai dan nisane ya saddata da guest lounge in.

Da sallama a bakinta tashiga. Duk su biyu suka amsa mata, suna mai daga idanun su, su kalle ta domin kuwa kamshi turarenta ne ma ya fara musu sallama kafin suji ainihin muryar nata.

Kallo daya Abdullah yayi ya maida kallon shi zuwa TV da ke a kune. Duba da ba muharramashi bace kuma ma ai shi zance ya rako bai kamata ya tsirawa budurwar aminin shi ido ba.

Shiko gogan naku, kusan zuzucewa ne kawai bai yi ba. He was tranfixed by her beauty. Har ga Allah in yace Afra bata mishi kyau toh yayi karya. In da a lokacin da yake niyar yin aure ne ya hadu da ita toh ba abinda zai hanashi barin zuciyar shi ta so ta, amma sai dai kuma kash bai shirya ba wa wata 'ya mace zuciyar shi ba.

Gaishe da Abdullah tafarayi wanda ya amsa mata da fara'a, kafin tajuya ta gaida Omar, shima ya amsa amma kamar ana tursasamasa. Tabe bakin ta tayi kafin ta zauna a kan one sitter dake ta gefan Omar.

Sunkai yan sakonin ba ayi magana ba kafin Abdullah yayi yunkurin magana.

" toh Gashi dai munzo zance amma fa sai dai kiyi hakuri da mu kinsa sabon shiga " ya fada in a playful way.

Itama murmushi tayi tafin ta replying mishi. " ba komai ai. "

" toh ya kike, ya karatu ".

" Alhamdulilah, ya maman Iman da su Iman ". Wannan tambayar da Afra tayi shi ya ja hankali Omar kansu don shi da amfani Kawai yake da wayar shi ma.

A ina ta san matar Abdullah kuma, shine tambayar da yake wa kanshi.

" duk suna nan Lafiya, tana ma gaishe da ke, har ta yi fushi ma, ta gaji da jin zaki zo, zaki zo amma har yanzu baki cika alkawari ba " ya fada yana murmushi.

" ina amsawa, kuma ka mace mata tayi hakuri, makaranta ne yake cimin time, kasan munkusa fara exams so duk ban zaunaba Gaskiya, amma kace mata in muka sami break zanzo In Shaa Allah ".

Shaking head in shi Abdullah yayi kafin ya amsa da. " toh Allah ya sa dai ki cika wannan alkawarin ".

Amsawa tayi da "amin ".

Shiko Omar naku ya cika da tambayoyi da yasan bazai samu amsarsu ba, gwanda ma awajen Abdullah kila ya fada mishi tayanda Afra tasan maman Iman. Abdullah ne ya tashi yace bari ya basu wuri sudan zanta.

 AFRA Where stories live. Discover now