Babi na sha bakwai

1K 121 10
                                    

I am dedicating this whole chapter to @hassieymumin . Thank you for loving this book.

************************************

A hankali take saukowa daga kan flights na staircase in. Sanye take a cikin lace mai dan tsada, wadda tayi ma dinki bubu. Anyi ado a gaban bubun da bakin lace. Kunnenta da wuyanta ya sha gwal dan madaidaici.

Fuskar ta kam tasha powder da jan lipstick, daman gata fara sai yayi mata kyau. Wannan mata ba kowa bace ila mama zalikha, matar Salman ta biyu, wato babban su Affan. Hanyar wajen dinning tayi inda ta iske mijinta zaune yana jiranta. Daman yau a gidanta yake shiyasa tun da safe ta tashi tasa masu aiki sukayi ma mai gidan nata breakfast mai rai.

Sautin takon tane ya sa Abbi kai kallonshi kanta. Murmushi ne ya fadada a kan fuskar shi yana mai duban ta da kulawa shimfide akan idanun shi. Murmushin da yake bala'in kauna ita ta sakar mishi.

" Good morning my love " ya furtamata yayin da ta karaso wajenshi.

" morning Abbin su " ta amsa masa tana mai jan kujerar kusa da shi ta zauna.

Murmushi dan tsohon nata ya sakarmata while ita kuma ta shiga bubude coolers in. Dakaline da aka soya shi da kwai, sai kuma farfesun kaza da kidney saurce, da kuma kosai sai flask na ruwan zafi, da jug da nake kautata zaton kunu ne a ciki .

" Abbin su a fara sama pepper soup in na ko kuma kosai da kunu?".

" saka min kosan dai da kunu in fara warming cikin nawa " ya fada yana yar dariya.

Itama dariyar ta saki kafin ta fara masa serving. Sai da yaci yayi nak kafin ya tashi suka dunguma zuwa sitting room. Zama tayi kusa da shi suka dan fara labarin duniya. Akwai magana a bakinta amma tana son sai labarin nasu ya dan yi nisa kafin ta sako maganar.

Bari tayi sai da suka dan yi mintuna kafin tace

" umm Abbin su nace ba" tayi pausing.

Mai da hankalinshi yayi kanta kafin yace.

" mai, da matsala ne ?".

" eh toh " tace tana dan nodding.

" toh fadamin Amaryata, mai matsalar ki " .

" ni tsoro nake ji kada kayiwa maganar tawa wata fahimta ta daban" ta fada a hankali tana mai lagabar da kanta.

" haba ba wani Abu, Kawai fadi bukatar ki " ya fadamata.

Dan shiru tayi, kafin ta fara magana. Wannan kenan.

****
Falon Baba Alhaji cike yake da familyn Maska. Kowa ka ganshi zaune da peers in shi while suna jiran suji mai ya kawo musababin wannan sudden meeting in.

Yauwa ma kamar kowace ranar Abul bait ne, babban dan Baba Alhaji ya bude taro da addu'a.

" kamar yarda nasan kowa na mamakin wannan sudden meeting in ba komai ne yasani yi ba sai don in nuna godiya ta gare ku " ya nuna barin da yammata gidan suke, tare kuma da nuna barin su Omar ma.

" da baku watsa min kasa a ido ba, na yanke hukuncin akan ku kuma duk kuka dauke shi hannu bi-biyu batare da kun min musu ba, Allah yayi muku albarka ".

" amin " aka amsa a tare.

" abu na biyu kuma inaso ince muku, na zauna da iyayen ku, mun zanta da su, mun sa bikin nan da wata uku mai zuwa. Allah ya sa mukai lokacin " ya karasa.

"Amin" .

Wa'azi yayi musu akan aure, da kuma hakokin da ze rataya akan su. Dukanin mutanen wajen sai da jikinsu yayi sanya, domin ko wa'azin ya ratsa zukatan masu sauraro. Bayan ya gama ne Baba Alhaji ya kai dubanshi barin mazan.

 AFRA Kde žijí příběhy. Začni objevovat