Babi na Sha Daya.

1K 170 10
                                    

Kallon shi tayi sakoko, tana mai mamakin wannan furucin nashi. Marry me. A Wanne garin mahaukatan ne aka ce mishi ana haka Kawai bata san shi ba, bata san halinshi ba,  bai santa ba balle sanin ya halinta yake sai ya ce ta aure shi, Kawai don zai taimaka mata ya kawo mata sauki cikin abinda tayi shekara daya tana neman sa'a akai.

" in aure ka fa kace " ta kara maimaita mishi abinda taji yafito daga bakin shi.

Murmushin gefan kumatu yayi Wanda nan take fuskar shi ta koma kamar hadari kafin yace " look don't think you are really special, Kawai you want something, ni ma kuma in return I want something. My family, they adore you and I have been given some months to bring a girl that I will want to marry or else kuma a bane wata stupid girl.  toh a cikin candidates dina you are more reliable kuma ma ba zama na dindin din bane, once you achieve your aim zan sawake miki ki aure love of your life "

Kalmar shi na karshe ya dan bata mamaki, mai ya dauki aure ne wai, wasan yara ko kuma karanta abcd. Kuma ma don ya raina mata wayo shine zai wani ce she's more reliable sai kace wace tanun ta damu da shi tana son shi. Tayi niyar fada mishi bakar magana amma sai ta tuno da promise din da tayi Mata, ba za ta iya karyawa ba, kuma ai in ta tuna alqawarin ai cewa tayi kowace hanya sai ta bi ta bi Mata hakin ta, ta rama mata abinda akayi mata. To ai Wannan ma wata damar ce ai ko. Kuma ma ai Wannan ba in an illegal way zatayi ramakon bama, kinga kenan ta jefe tsuntsu biyu da dutse daya ne.

Numfasawa tayi kafin tace.

" na yarda though akwai certain things, sharuda da nake son gindaya wa kafin ya faru ".

" I'll talk to my lawyer, nan da jibi he will draft an agreement and zan kawo sai ki cike"  ya fada kafin ya tada motar ya fara tuki zuwa gidan su Afra. Wannan kenan.

******

Two days after

" Afra Habibty " Ummi ta shigo cikin dakin Afra. Samun Afra tayi a zaune a kan gadon ta, laptop din ta ne a kan cinyar ta. Alamu ya nuna wani abu take amma kuma kwata kwata hankalinta ba a kan screen din yake ba, ta lula wani tunani na daban.

Jin kiran sunan ta ne ya fargar da ita, dawo wa tayi hayacin ta taga Ummi ce zaune a kan gabar gadon ta.

" Ummi yaushe kika shigo " ta tambayar mahaifiyar tata domin ko bata ji shigowar ta ba.

" yanzu nan. Kin yi bako "

" Bako kuma " ta tambayi Ummi tana mamaki don dai tasan in Asad ne ai zai kirata kuma ma sunyi waya da shi dazu kuma bai ce mata zai zo ba, ai kuma ma Ummi bazata kira Asad bako ba. Toh waye.

" Eh mana Omar ko bakisan da zuwan shi bane,  " Ummi ta fada mata tana jefan ta da kallon tuhuma.

Ganin kallon da Ummi take mata ne yasa tace " eh nasani, ai bansan yanzu zai zo bane na zata sai anjima " ta wayance don ko bai cemata zai zo ba, ita rabon da ta mishi magana ma tun bayan da ya dawo da ita gida ya ce ta rubuto masa sharudan da za ayi drafting bata sake jin shi ba, ta zata ma ya fasa ne. 

" wai in tambaye ki "

" inajinki Ummi " .

" is there something going on between you and Omar " Ummi ta tambaya in curiosity.

Dan murmushi tayi tana mai jin kunyar tambayar da Ummi tayi mata. Ita ba wai son Omar take ba, ko daya bai cikin jerin mazan da take so amma Kawai tambayar Ummin ce tasata jin kunya.

Ganin Afra batada niyar bata amsa ne yasa Ummi cewa.

"toh I have approved. sai ki tashi ki shirya kije ko, nasa an kai masa abin motsa baki ". Ummi tace tare da tashi domin barin dakin Afra.

" also kiyi sauri dai kar ki barshi yayi ta jiran ki, sabida dai na sanki da nawa"  Ummi ta ambata tare da sa kai domin ficewa.

" kai Ummi " ta fada a shawagbe tana dan bubbuga kafarta a kasa. Dariya Ummi tayi ta karasa fita daga cikin dakin. Wannan kenan.

****
Shiga ciki tayi da sallama dauke akan lebben ta. Su biyu tagani zaune akan two sitter couch, Omar ne tare da wanda take yakini akan shine lawyer.  duk sunyi shigar alfarma. Omar sanya yake cikin wani yadi mai tsada fari qal sai kyali yake, yayin da shi kuma lawyer yake sanye da wani bakin yadi. Shima din duk kusan sa'anine da Omar in ma zai girme shi toh da shekaru biyune zuwa uku.

Amsa mata sallamar sukayi. Kallon ta Omar yayi sanye take da wani lace golden mai zane manya manya. Riga ne da skirt Wanda yayi fitting in ta, sai mayafi da ta yafa a gefen kafadarta ta hagu , ta yi kyau Sosai a cikin kaya, domin ko sun amshe ta . Shima kanshi Omar sai da ya yaba irin kyau da tayi, ganin irin kallon da Aminu wato lawyern shi yake mata sai yaji wani tukukun abu ya tokare mokoshi shin.

Wai ita wace irin yarinya ce haka da hijabi bai dame ta ba. Duk sanda ya hadu da ita toh bata taba sa hijabi. Wani kishi ne yaji ya kamashi ko ba komai ai niyar auren ta yake yi bai kamata ko wani na miji yana ganin kwaliyyar taba.

Omar yana daga cikin jerin mazanan masu Bala'in kishi domin tun yana karamin in dai aka sai musu abu toh fa ba mai tabawa in bahaka ba za aga baccin ranshi. He hates sharing.

Tsuka ya ja wanda ya dawo da haiyacin Aminu kan shi. Ganin fuskar Omar a murtukewar,.ya fargar da Aminu akan abin da yayi. Shi kwata kwata yama manta da irin kishi na Omar. Aminu has been his friend since a university, though ba course daya suka karanta ba amma sabida hostel daya suka zaune, room din Wannan na facing na dayan, kuma ma jinin su ya hadu shi ya jawo abotan su.

" Afuwa aboki " yayi whispering wa Omar Wanda ya ke jifan shi da harara.

Mai da kallon shi ya zuwa wajen Afra wace ta zauna kanta na kasa tana kallon wayar ta. Ita tarasa mai yasa in dai yana wuri sai ta ringa jin kunya ta lulube ta, ita dai tasan she's a confident person kuma da wuya kaga ta irin nuna tana jin kunya magana a wajen mutane amma presence in shi na sata feeling tongue tied.

Gyaran murya Aminu yayi ganin ba mai magana a tsakanin Afra da Omar in. Fara mata bayani yayi dala dala yanda zata gane kafin ya fito da papers in ya mika mata, yana mai nuna mata inda zatayi signing.

Kallon inda zatayi signing in tayi kafin ta maida kallonta gurin su Aminun kamar mai tunani wani abu, sai kuma ta komar da attention in ta kan papers in tare the signing without looking at the contents written a jikin paper. Wannan kenan.

____________________________________________________________________________

 toh abinda dai zance shine please vote, like and comment.

Gaskiya kuma ina neman comment in ku sosai domin ya qarfafamin gwiwar yin rubutu .

 AFRA Where stories live. Discover now