Babi na Ashirin da bakwai

1K 112 1
                                    

Staircase yake hawa wanda aka yishi in an S shape, handle na staircase in da glass akayi, kasan kuma white, fluff carpet aka shimfida har zuwa ending of the stairs, so dan haka in mutum na tafiya ba'a jin takun sautin tafiyar mutum. Haka ne yake faruwa da shi, sai da yazo ta wajen karshin hawan, ya farajin tashin qira'a mai dadin sauraro.

Karasa hawa yayi ya wuce ta wani dogon hallway, wanda dakin Afra na a daman shi while shikuma dakinshi na a dan nesa da nata. Ta wajen dakinta yazo zai wuce, domin dole sai ya wuce dakinta kafin ya isa na shi, jin daddadar qira'a na fitowa daga dakinta ne yasa shi tsayawa. Dan jingina yayi da bangon yana mai sauraran karatun nata.

Rabon shi da Afra tun Jiya da daddare, don ko yau ma da safe da ya je tashinta sallah samu yayi tarigada ta shiga bathroom. Jin karatun ya tsaya ne ya bashi damar bude kofar dakin.

Da salama a bakinshi ya shiga. Ita kuma Afra lokacin tana folding mat data yi sallah da, juyawa tayi ta kalle shi kafin ta amsa salamar tashi. Shiga yayi cikin dakin tareda da zama akan Ottoman na gadonta.

Shiga cikin closet ta tayi domin ajiye abin sallar ta, kafin ta fito daga ciki. Sanye take cikin wata silk bubu da ta zauna a jikinta tayi mata kyau duk da ba wani ado ne a jikin rigar ba, sai kuma kanta da ta kama da ribbon amma bata sa dan kwalin a kan ba.

" ina kwana " ta gaishe da shine Kawai don darajar abu uku, a farko domin ko yayane ma dai aurenta yake, na biyu don darajar Umminta da irin nasihar da tayi mata, na uku kam sabida tana ganin kimar Mahaifiyar shi mai sonta.

Kallon ta yayi yana admiring in ta, wani kyau yaga tayi mishi a hakan even though bata yi kwaliya ba,  baby hair in ta ne ya kwanta luff a gaban goshinta Wanda ya kara fito da yarintarta ta.

" Lafiya"  ya amsa a kansan makoshin shi.

Shiru ne ya mamaye dakin ba mai shirin yin magana a tsakanin su. Zama Afra tayi a kan gadonta tana mai daukan wayarta don duba what's app in ta.

" we have made some progress,  mungano inda Salim ya fi zama. " ya fada mata.

Abin ya zo mata a bazata, sabida batayi tsammanin samun komai da ya dangancin maganar Salim daga wajen shi ba. Dago kanta tayi ta Zuba idonta a kanshi already daman shi ma kallonta yakeyi.

" I thought kace baruwana da wannan maganar " tayi mishi tambaya.

Shrugging shouldern shi yayi kafin yace.

" yeah na yi tunani ne naga be kamata ba although ba shine yake nufin zaki shiga cikin ba, Kawai dai in na samu important information, I have decided to let you know ne ".

" toh thank you ". Ta ce mishi.

Tashi yayi daga kan Ottoman in ya fara nufan kofar fita, sai da ya kai bakin kofar kuma sai ya ja birki ya tsaya. Juyawa yayi ya tako har wurin gadon ta.

Dan leaning yayi, yayi kissing forehead inta, which took her by surprise, kafinta fara mishi korafinta kuma ya cire ribbon din dake kanta tareda da cemata.

" leave your hair down, yafi miki kyau ". Daga haka kuma ya fita daga dakin tareda da ribbon innata a hannunshi, ya barta da sakin baki, zuciyarta kuma mamakin shine yake mamayeta.

Wai mai yake nufi da ita ne, ina agreement in da suka rubuta yake, wai anya ma zai iya cikamata burin ganin karshen Salim kuwa. Toh in dai har zai iya watsi da agreement insu ai tana ganin ba wani abu mai wuya bane yayi watsi da maganar Salim. Amma she prays hakan ba zai faru ba. Wanna kenan.

****
" Sannun ku da zuwa " tace musu da murmushi a kan fuskarta tana mai musu iso cikin parlor bakin.

Yan uwan Omar ne suka zo mata, su wajen su biyar manya, tareda yaransu yammata su Uku. Dan tsugunawa tayi kasa ta gaishe da manyan, sukum yammatan suka gaishe da ita, daya ce Kawai bata gaishe ta ba itama ganin su'artace sai dai kwai tayi mata murmushi.

 AFRA Where stories live. Discover now