Babi na Arba'in da shida

992 119 7
                                    

Shiga cikin gidan Uncle H yayi afujajan kamar wanda yake da tabin hankali domin kwana biyu nan jin shi yake wani iri, bai taba zaton haka yake jin Afra a zuciyar shi, bai taba zaton it din tana da wani special place a wajan ba, sai da ya ga idanuwan shi basuyi tozali da kyakyawar fuskarta ba na kwana biyu, duk sai ya ji duniyar bata masa dadi, ashe haske ce a gareshi tunda yanzu baki duniyar tayi mishi . Da sallama a bakinshi yake kokarin shiga cikin parlor gidan, ganin Uncle H shi kadai ne ya bashi daman shiga ciki.

Uncle H ne ya amsa mishi tareda kallon shi yana mai aiyana abubuwa a kwakwalwarshi. Ya san dai wannan abun na da nasaba da maganar da sukayi da Omar kwanakin baya.

Zama yayi a kujerar da Uncle H ke zaune tareda sa tafin hannun shi ya kulle fuskar shi yana mai shakar isa yana busarwa, kowa ya ganshi yaga Wanda yake cikin matsakaicin tashin hankali.

" Omar ya, Lafiya".

" ban san ya zanyi ba " shine amsar da Omar yaba Uncle H.

" kamar ya bangane ba " Uncle H ya tambayeshi with confusion, tareda rankwafowa yana mai kallon Omar.

" kasan nace ma ai mun kama su Salim ko ". Nodding Uncle H yayi yana jiran ya ji karashen maganar.

" toh tasani, yanzu tace wai sai na sake ta. "

" toh me a ciki ba sai ta saketan ba " Uncle H ya fada with a non chalant expression.

Wani harara Omar ya jefe shi dashi amma bai ce mishi komai ba. Dan murmushi Uncle H yayi kafin ya sa hannun sa akan kafadan Omar yana mai ce mishi.

" Bawai cewa nayi ka sake ta ba " yayi pausing wa wasu sakoni, sai kuma ya rada ma Omar wani abu a cikin kunnenshi, ni dai banji mai yace ba amma dai gani nayi Omar ya saki fuskar shi, sai murmushi yake zubawa kamar Wanda akayi mishi bishara da wani abu mai dadi. Cigaba sukayi da tattauna lamarin suna saka da warwara domin plan in nasu yaje yanda suke so. Wannan kenan.

****
Dawowan shi kenan yanzu daga gidan Uncle H, sai da ma yayi maghrib tareda yin dinner kafin ya baro gidan. Shigowa yayi yaji ko ina tsit kamar ba mutum, in ba don su Ozo ma sun fada mishi Afra batayi kokarin tafiya ba da sai ya ce ko taje gidane.

Hawa kan matatakalar yayi yana nufi hanyar dakinta, shima haka wajan tsit,  murza kofar dakin yayi yaga ta bude. Wani dadi ne marar misaltuwa ya ziyarce shi. Yana kuma mamakin yanda ta bar kofar abude, shiga yayi cikin dakin. Sassanyar turaren ta da yayi missing shi ya bugi kafofin hancin shi. Shakar kamshin yayi yana mai lumshe idonshi. Wata kasala ce ta ziyarce shi. Yarasa mai yasa duk lokacin da yaji kamshi turarenta yake shiga cikin irin wannan yanayin.

Kallon dakin yayi ya ganshi fes fes. Abinda yake kara burgeshi da Afra kenan tsabtarta, shi fa a rayuwa yana soon tsabta shiyasa shi dakinshi ba a taba ganinshi da datti. Jin qaran shower ne ya dawo mishi da hankalinshi daga tunani da ya shiga. Wanka ta shiga kenan shiyasa ta manta bata kulle kofar ba, tunani da ya ziyarci zuciyarshi kenan.

Stool in dake gaban mirror ya janyo tareda zama akai yana mai jiran fitowarta. Tunani yake akan plan in da sukayi da uncle H, anya ko zai iya yin abinda yace yayi ko kuma ya, shifa tsoranshi kar garin neman gira a rasa ido. Dan shiru yayi kamar me wani tunanin amma kuma ba shi yake yi ba, kawai dai yayi zeroing mind in shi ne, domin neman wa kanshi Lafiya da mafita, ganin dai bai da wani solution illa ya bi da abinda Uncle H in ya fada ya sashi furta wasu addu'o'i domin samun nasara.

Ba'a fi mintuna kadan da zaman shi ba, Afra wacce batayi zata akwai mutum a cikin dakin ba ta fito, sanyi take cikin wani karamin pink towel Wanda bai gama rufe santala santalan cinyoyin ta ba, amfani take da wani karamin towel kuma tana drying silky gashinta.

Kallonta ya tsaya yi, yau ne zai iya cewa rana ta farko da ya taba ganinta a haka, ji yayi wani abu na mishi yawo a jiki, wani yanayine yashiga ganin ta a haka, irin yana yin da bai taba ziyarcen shi ba, wani yawu ya hadiye yana mai rintsa idanun sa. Jiyayi kamar yayi violating right inta, don har yanzu batasan da zuwan shi ba.

 AFRA Where stories live. Discover now