Babi na Arba'in da biyu

901 117 3
                                    

Abuja.

Zaune yake a cikin mota, kamar dai yanda ya saba tafiya, haka ma yau da escorts insa yake, Sanye yake cikin ceremonial uniform in su. Kayan ya zauna mishi a jiki yayi kyau, ko da dai daman shifa kowani irin kaya yasaka ko bai da kyau toh jikinshi na sasu yin kyau, kuma ba wai hakan na nufi in wani ya saka zai mishi kyau bane, yana da jikin da mutane suke kira da athletic built.

Yanzu a hanya suke na zuwa branch office na ICPC dake a garki. Bai wani dade da isowa ba, tunda ya sauka a gadinsu dake maitama, kawai abinci yaci tareda sauya kayanshi, sai kawai ya dau hanya, domin ko ba yan nan ma, yanada meeting da zasu shiga a company da yake da share a ciki, wanda na baban Afra ne.  Daman meeting in ma yana daya daga cikin reason in shi na yin wannan tafiyan.

Dan jim yayi yana mai tuno da abinda ya faru tsakin shi da Afra dazu. Besan what came to his mind ba amma dai yasan bazai iya bari ba tareda yayi abinda zuciyarshi tayi ta azazzalashi da yi ba tun ba ma yau ba. Dan murmushi yayi yana mai dan lumshe manyan idanun shi.

Sunyi tafiya mai dan nisa domin daga maitama zuwa garkin akwai dan nisa,  duba da yawan traffic lights in dake a hanya. Shiga ciki sukayi bayan an bude musu gate. Wajen babban gini ne mai hawa Kusan goma Wanda akayi gini da glass Wanda yake da duhu domin ba a iya ganin cikin wajan. An dan kawatashi da flowers masu kyau. Ozo ne ya fita ya bude masa kofa, fita yayi daga motar, duka escort in nashi suma suka fito. Wajan su goma, haka suka dunguma cikin wajen.

Cikin ginin in mutum ya shiga da reception zai fara tozali, wanda aka kawatashi da stainless steel a ta wajan receptionist in sai kuma wasu kyawawan kujeru da aka ajeyi su a waiting space in, saman ceiling in high ne dake dauke da wasu intricate designs da akayi a pop, sai kuma wutacen da aka saka duk suka kawata wajan.

Mutanen dake aiki a wajan duk kai kawo suke yi amma ganin shigowar Omar duk suka fara bashi girman shi sabida mukamin da yake kai, annan ma suka hadu da Abdul Wanda yayi mishi jagoran zuwa Office in head nasu wato Alhaji Bukar Gana. Anan kasa ya baro sojojinshi ganin ai the man does not pose as a threat to their boss.

Bayan sun fito daga elevator ne sai suka nemi izinin ganawa da Alhaji Gana, sakatariyarshi taje neman musu izini ko da dai ma shi Alhajin ya san da zuwan su. Fitowa tayi daga office in tareda cemusu su shiga yana jiran su.

****
Gidan kashe ahu kaduna dan kande.

Yau ma kida ne ke tashi, na yau ma kidan ya fi na kullum domin ko yau gidan a cike yake makil ba masaka tsinke. Tun daga gate ma mutum zai gane ana sha'ani domin motocine manya manya kirar su Mercedes Benz, zuwa su audi kai da dai sauran su.

Kishingide suke su biyu akan kujeru ta alfarma kamar wasu sarakai. Daka gansu kaga Uba da da. Gefan su kuma wasu hadaddun mata ne, Wanda kyaun su kadai ya isa ya sa mutum pausing just to stare at them. Kowanen su guda biyu ne a gefan shi suna ta holewarsu da ita bama sa jin tsoron Allah balle idon mutane. Allah ya samu dace.

Shi Alhaji babayo rike yake da katuwar kwalbar giya, lokaci zuwa lokaci yana kai wa bakinshi ya tultula kafin kuma ya koma abinda yake yi. Shikuma Salim hannun shi rike ne da irin katuwar taban nan yana zuka yana kallon matan dake entertaining in shi, kwata kwata sun shagala, hankalinsu a kwance, suna ganin ai su ba mai kamasu, sun manta da Allah na ganin su, sun manta da karin maganar da ake cewa kwana casa'in da tara na barawo, kwana daya na mai kaya. Toh hakan ne ke shirin faruwa da su. Sun zata they are invisible, sun zata su in wasu special beings ne amongst humans, sun zata duniyar tasu ce su kadai suyi holewarsu, su zalinci Wanda suka zalinta su zauna Lafiya. 

Amma ina sun manta da no condition is permanent. Suna cikin haka, bazato ba tsamani, domin da dayan su yasan da haka ma,wannan partin ma ba a yishi ba, ko kuma ma toh za'a neme mishi a rasa.  Suna tsaka da jin dadinsu sai kwai jin wani sanyin metal na dogaran keyansu. Abin ya basu mamaki matuka, domin a gidanan bawanda yake da livern yi musu haka, kuma ma dai mai wannan metal in da ke dunguran keyarsu. Abu na biyu kuma da ya basu mamaki shine daina jin karan kidan da ke tashi seconds ago, abu na uku da ya kara harzuka musu hanjin cikinsu shi ne ganin yanda kowa, da bugaggun da Wanda ba su bugun da giya ba duk sun tsaya cak suna kallonsu da tsoro fal zuciyarsu, fuskarsu da idanun su ya nuna tsananin tsoron da suka shiga a yan sakoninan.

Salim ne yayi ta maza ya fara Juya kanshi amma sai ji yayi an damki wuyan shi an qara kara mishi metal in a bayan keyarshi, tip in na digging cikin tulin gashin shi.  

"  Salim, and babayo you are here by arrested, you are required to remain silent or else what you'll say will be used against you in the court of law ".

Ba kadai Salim ba ko shi Alhaji Babayo sai da cikin shi ya bada kara kuuuu kai kace Wanda yaci wani abu ya bata mishi ciki. Jin qaran tafiyane ta gaban su ya sa su kai hankalinsu wajan, domin da duk sun lula duniyar tunanin tayanda zasuyi escaping even though ba ta yanda Zasu iya.

Ganin dan kwalisa sanye da ankwa a hannunshi ne ya basu mamaki, ga kuma wani murdaddan katon mutum a tabayan shi yana mai turashi zuwa inda suka.

" what is the meaning..." Salim ya fara amma na bayan shi yayi using butt na bindugar ya dake shi da shi, wani irin zafine da ya rasa na meye ya buge shi ai besan lokacin da ya rusa wata rikitattan kara ba. Yin hankan da yayi kuma ya ba mutumin daman kama hanayen shi biyu ya sa ankwa, Shima Babayo haka aka mishi. Mutsu mutsu ya fara yi wai shi gashi mai taurin kai, amma da mutumin na bayan shi ya kwashe shi da mari ai sai ya natsu.

" kai wato taurin kai zaka mana ko"  mutumin yace yana kara dauke shi da mari. Haka mutumin yayi mishi lilis sai da yaga ya daku don ko yar yatsar shi da kyar yake dagawa sai ya barshi. 

Daukar su akayi, tareda duksauran mutanan gidan, daman sun zo da police wajan guda talatin, suna fita daga gidan suka ga sauran yan gidan na barin dan bushiya suma an je an taho da su, yau su yar tsana an koma dan tsana domin in da ban ga kayan dake jikinshi ba da bazan zata ma shi bane domin fuskar nan tashi yayi jirwaye da kuka, da jinnin da ya ke diga daga hancin shi, daga gani shima yayi gardaman ne shine kuma ya ci na jaki.

Tasa kyarasu akayi aka shigar da su cikin motan tareda mutanen su, domin in dai su Babayo kadai aka kama toh anyi ba ayi ba ne, domin wasu Wanda akayi training Zasu iya cigaba da harkar, sukuma ai so suke suyi abolishing abun ma gaba daya.wannan kenan.

______________________________________

Toh yaudai su Salim za ayi kwanan cell .

Vote, comment and share

 AFRA Where stories live. Discover now