Babi na Arba'in da Tara

1K 117 6
                                    

Federal High court kaduna.
A federal high court dake nan NDA junction nane ya cika makil da mutane ba ma masaka tsinki, kun dai san yanda mutane suke da anji za'ayi sharia a kotu toh da kwansu da kwarkwartasu duk sai sun halara a wajan.

Yau ne ranar da za a shigar da su Salim kotu domin zarce musu hukunci, don dama a ringada an samo concrete evidence da baza su iya escaping sentence in su ba. Kamar yanda wajan ya cika haka cikin ya cika da mutane, wasu zaune a kan kujerun da aka tanada ma masu kallo wasu kuma a tsaye, kai har akwai masu leke ta window ma. Su Salim ne tsaye agaban kotu a ta right hand side, kowanen su an kama mishi hannun shi da ankwa ga kuma police guda hudu da ke bayan su. Sai kuma alkali dake zaune a kan mumbarin shi. Lauyoyine zaune a in da aka tana da musu, da masu kare su Salim da wanda suke opposing in su.

A ta bayan su kuma yan ICPC ne tareda dubin jama'a da suka zo kallon shari'ah. Omar dasu Sam duk suna cikin mutanan suna me jiran suji ya zata kaya domin duk da sun san sun sami evidence amma kasar Nigeria abin tsoro ce za'a iya murda evidence in nan a rage musu prison time. 

Buga gudumar dake hannunshi alkalin yayi Wanda ya sa wajan zama tsit kowa na jira ya ji me za'a ce domin ko ba a dade da dawowa daga dan hutun da alkalin ya bukaci a yi ba domin yin nazari da kuma kara yin binciken hojojjin da aka kawo mishi, don kar ya yanke hukunci me tsauri akan su kuma daga baya a ga offense in nasu be kai a yanke musu tsatsauran hukunci ba.

****
Zaune take a wajan garden na gidan nata tana me duba social media yayin da iska me sanye ke busu wa, sai ta ji dadin iskan domin dama garin da akwai zafi, chilled mixed fruit drink ne kuma ajiye a gabanta Wanda take sha domin ko har ya kai rabi ma. Nothern blog take dubawa tana me jiran dawowar Omar taji inda zancen ya tsirga. Ta so zuwa yau amma Omar ya kule idonshi ya hanata zuwa, don ba yanda zatayi hakan ya sa ta hakura bawai don ta so ba, sai don kawai a zauna Lafiya.  

Don haka yau bayan ta dawo daga wajan su kaka Alhaji, bata zarce ko ina ba sai wajan garden domin ta shaki sanyayar iskar da ke kadawa.
Tana cikin duba Instagram ba tareda ta kawo kome ba ta ji wani abu me dumin ya kulle mata ganin ta, bude idanunta ta karayi taga bata ganin ko me sai duhu domin an kule mata ido ne da tafin hannu me taushi, jin kamshi turaran Omar da kuma texture hannun da ta ji a fuskarta ne ya bata daman sanin mijinta ne culprit in.

" Omar " ta furta a hankali tana me zare hannunshi daga fuskarta. Tashi tsaye tayi tareda juyawa ta ganshi tsaye a bayanta fuskar shi cike da annuri. Janyo shi tayi da hannun da take rike da tana me mishi masauki a kujera da ke gefan ta, ita ma sai ta zauna a gefan shi.

" ya gajiya " ta kara furta wata kalmar.

Dan lumshe idonshi yayi yana mai daukan wasu sakoni kafin ya amsa mata.

" Lafiya Alhamdulilah ".

Sagale hannun ta tayi a baya wuyan shi tana me dan rankafowa tareda pecking goshin shi. Kallon ta cikin ido yayi ya ga sai murmushi take aika mishi, shima murmushin yayi mata.

" wannan murmushin haka, I think I deserve to hear this good news" ta fada hucin numfashin ta na bugan fatar fuskarshi.

Kasala yaji ta sauke mishi tareda wani sonta na kara shiga cikin shi, wai shi Omar yau ne yake jin son wata na mishi haka a cikin zuciya, abin na bashi mamaki matuka yanda ganin ta kawai ke sa shi cikin nishadi.

" an yanke wa Alhaji Babayo da dan kwalisa hukuncin kisa, shikuma Salim da sauran su life in prisonment". Ya ce mata yana me yawo da finger in shi, kamar me zanen wani abu akan hannun nata da ya ke rike da shi.

" oh my dayss, you kidding me " tace tana mai washe hakoranta. Abin ya bata mamaki matuka tayanda akayi wannan shari'ar ba tareda wani tangarda ba.

Jin jina kanshi yayi yana me murmusawa.

" I'm serious".

Sabida dadi ma bata san lokacin da ta bashi wani bear hug ba sauran kadan ma ta kada shi sabida a bazato abin ya zo mishi.

" thank you, thank you, thank you, ka gama min komai a duniyar nan tunda har ka iya temakawa don kawo karshe azzaluman nan, ban san da wani irin abu zan gode ma ba "

" bakisani ba " ya daga girar shi daya yana me jifanta da wani mischievous look. Hada giranta biyu tayi tana me pursuing lips in ta, wanan look in da yake jifanta da shi batasan na me ba amma kuma bata ma son sani. So sai kawai tayi shaking head in ta tareda barin wajen, shima biyo bayanta yayi yana me darawa daga reaction in ta.

****
" wai ko sai jirgin ya tafi zaki fito " Omar ya fada yana me leka ciki dakin ta. Ganinta yayi tana jan akwatina manya guda biyu a hannunta kuma ta sagale bakar hand bag inta a kafadarta. Karasawa yayi domin ya temaka mata don ya ga kamar sun mata nauyi.

" yi hakuri, I had to change my outfit ne shiyasa " tace dashi tana me mika mishi akwatunan.

Kallonta yayi yagan ta sanye cikin wani farar free abaya wace ta karbe ta tayi mata kyau, yau dai ranar ta farko da ya ga bata sa makeup ba duk da fita zatayi, sai yaga ta kara mishi kyau ma. 

" bakomai, kinyi kyau "yace mata.

" thank you, kai ma kayi " ta ce mishi tana me jefan shi da murmushi. Sanye shima yake cikin wani wandon trousers black, yayi pairing inshi da wani farin long sleeve shirt, bottons in farko da na biyu duk a bude suke, sunam me bayan faffadan kirjinshi me dauke da gashi da ke a kwance.

Fita sukayi daga cikin gidan, dama kuma tun jiya sukayi wa mahaifan Afra da na Omar in salama. Don haka daga gidan su kawai airport suka zarce inda jirgi ke jiran su. Daman da private jet in daddy zasu tafi da don haka ba su wani sha wuya ba suka samu suka shiga jirgin. Aikam ba a yi mintuna ba jirgi ya lula Sama sai kasar Rome, Italy.

*****
Bangaren su Mama Zalikha.

Tunda Zalikha tayi wannan hauka a gaban su KakaAlhaji bata kara zuwa wajan su da sunan gaisuwa ba, sai dai fafutuka sukayi tayi domin karkato da hankalin Omar kan yarta amma abin ya ci tura tun suna zuwa wajan malamai har ya kai ga suka fara ziyartar malaman tsibbu don kawai haqar su ta cima ruwa amma inaa babu, gashi kuma baban su Maryam ganin su Abida duk sun yi aure, don haka ne ya taso ta a gaba domin ta fidda mijin aure, daman kuma yana yawan ganin ta da samari suna zuwa wajanta zance, amma ita duk cikin su babu Wanda yayi mata, ba wai kuma basuda kudi bane kawai dai ita ta raina arzikinsu ne gani take basu kai irin arzikin da take so ba.

" ya maganar mu da mukayi kwanaki " Abbi ya tambayi maryam.

Daman tun lokacin da yayi mata maganar ta fito da miji ko ya bata Wanda yaga yayi mishi shine mama Zalikha ta yi tsale ta dira tana me cewa ba a isa ayi ma yarta auran dole ba, wannan abun da tayi har sai da ya sa suka haura da mijin nata dama gashi a cike yake da ita ganin cin mutuncin da tayi ma iyayenta, daga baya dai ya sako ganin in yace zai biye mata shima mahaukacin ze zama kamar ita, don haka sai ya ba Maryam wata daya ta fitar da miji daga wa'enda suke zuwa neman ta.    

" Abbi dama dama " ta fara fada sai tayi shiru bata karasa ba.

" ina jinki daman me ".

Kin bashi amsa tayi sai ta Juya ta kalli zalikha dake faman zuba murmushi ba kakkautawa.

" daman wani ne yazo wajan ta basu wani dadi ba dai amma wai dan Alhaji Isa Saminaka ne".

" toh toh toh wani Saminakan ba dai me gidajan mai ba ".

Dan murmushi Zalikha tayi tana me jin jina mishi kai .

" eh shifa".

"Allahu akbar, toh madalla, ai dai Kina sonsa ko " ya Juya akalar tambayar shi ga yar tashi. Jin jin Kanta tayi tana me sunsune kanta wai ita tana jin kunya.

" toh ai tunda kinason shi shima yana sonki ai kawai kice nace ya turo " .

" shikenan " tace tana me tashi ta bar wajan ita ala dole kunya take ji. Duk bin ta sukayi suna me dariyan kunya nata kafin su koma kuma kan nasu harka.

______________________________________

Kuyi hakuri da rashin samun update da wuri.

Vote, comment and share.

     

 AFRA Where stories live. Discover now