Babi na Ashirin da hudu

1K 131 5
                                    

Waye Salim saif.

Malam saifullahi mai tabarmi shine sunan mahaifin Salim. Baban shi yana yin tabarmine yana siyarwa a kasuwan bacci dake tudun wada. Salim ya tashi a gidansu ba kwaba balle tsawa. Mahaifinshi yana da mata hudu amma kuma kafin su yayi wajen mata biyar amma ya rabu da su kuma duk sun haihu mishi, akalla malam saifullahi yana da yara ashirin.

Shi dama saifullahi irin masu maqonanne bai wa iyalinshi komai sai dai su suyi ma kansu, toh su ma masu iyayen agidan ba wani abun kirki suke ba bale irin su Salim da shi Uwarshi ma ba'a gidan take ba. Haka ya tashi yana bi kwararo, in matan uban ne ma sunji tausayin shi suke dan bashi abinci, barin ma uwar gidan Saifullahi duka tafisu hakuri da tausayi don haka a kulum su Salim suna samun abincin ci, ko da dai itama ba wani kudin kirki take samu ba a dan sana'ar tata, ta sai da su spices, amma kuma Allah na albarkatan kudin nata domin mutuniyar kirkice kwarai.

Haka dai Salim ya taso ba sallah bale alwala shidai Kawai a bakine muslumi amma banda a ayukan shi. Tunda ya fara girma ya fara bin wasu yan kwayan da ke unguwan su, zuwa wajaje daban daban ba wanda bai yi, kai wiwi nan kanta ko gaban Ubanshi ne busata yake yi. A haka dai da yawace yawacen shi ya hadu da wani qarkuzun dan safara da miyagun kwayoyi mai suna Alhaji Babayo.

Alhaji babayo dai ya dade a harkar wannan kwawowin kama da su cocaine da dai sauran su. Gashi drug dealer, ga kuma bariki tayi mishi katutu. Shi ba abinda baiyi kama daga raping in tsofafi zuwa yara don Kawai samun duniya. Gashi da bala'in bin bokaye kamar bamaguce, wai ahaka kuma yana sallah da azumi.

Lokacin da Salim ya hadu da Babayo a wani wajen Shakatawa ne, Salim ya nuna mishi yana kwadayin aiki da shi domin an bawa Salim labarin mutumun tun kama ya je wajensa. Ganin Salim ya mishi sai ya dauke shi aiki, tun Salim na siyarda kwaya ga mutane, har yakai ya kawo yana daga cikin masu safara daga gari zuwa gari, daga nan ma ganin hazakar shi da kuma wayon shi yasa Alhaji Babayo fara turashi yin safaran na International ma, kuma wani ikon Allah ba'a taba kamashi ba even though yana zuwa irin su Australia Wanda suke da tight security amma a haka yake wuce wa.

Allah yayi Salim da kwakwalwane Wanda ba kowaye yake da wannan sa'ar ba, shi da yaga abu so daya to yana rike shi, ko fuskar mutum ne ya gani sau daya toh fa duk inda ya ga mutumin nan zai ganeshi. Wannan kenan.                       

****

Tafiya sukayi a kafa da zai kai mintuna biyar kafin su isa gate in. kofar abude take, hakan shine ya basu damar shiga ciki, ganin tsirarun mutane sukayi kowa na harkokin gabanshi. Shima dai wannan gidan kamar wancan ne, parts parts ne sai kuma babba a tsakiyan Wanda yake kamar lobby, da kuma offices in manyan wajen a cikinshi.

" Sannu wa kuka zo nema " wata yarinyar ce da bazata wuce shekaru ashirin zuwa ashirin da biyu ba tayi magana. Sanye take da wasu kayan silk wanda ya lafe a jikinta ya bayana surarta. Kyakyawa ce domin irin fararen nan ne, Wanda farinsu ke daukar ido da hankalin mutane, kamanin ta yana yi kamar na yan chadi ko buzaye Wanda suke cikin dadi.

A gabansu ta tasya tana hura sigari in a professional way. Har wani ring yake yi intayi exhaling. Idanunta tar akansu tana kallon su amma hankalinta ya fi karkata zuwaga Omar Wanda take taji ya mata.

Murmushi da ke qara ma fuskar shi kyau ya sakarmata take ta susuce bata ma san sanda ta yarda cigarette in hannun ta ba. 

" we are actually new here. Daman cemana akayi, in dai Muna neman first grade na chicas, nan ne. Kuma I can see that they weren't lying. " ya fada yana mai harba mata wani shu'umin murmushi.

Take ta saki wani murmushi na jin dadin tana dan fari da long lashes in da ke kan idonta. Dadine ya mamaye zuciyarta tana mai jin dadin complement in shi.  

 AFRA Where stories live. Discover now