Babi na Uku

1.5K 116 0
                                    

Iska ce mai sanyi ke busowa, iskar na daukan da light dust da dirts in da suke k'asa tana wurgi da su a sararin samaniya. Zaune take a karkashin bishiyar mangoro yayinda take duba MacBook in da yake kan cinyar ta, tana yi tan shan strawberry smothien ta.

Cikakar giranta ta hada waje guda which shows duk concentration din ta na kan abin da take yi. all of a sudden taji an warce rubber smothien daga hannunta, juya idanunta tayi tana dan murmushi dan tasan wanda zai yi mata haka.

" Asad " ta kira sunan shi da sanyayyar muryar, yayin da ta dan daura fuska, wai ita anan tayi fushi. Dan saurayin da takira da Asad ne yayi murmushi mai sauti kafin ya kafa bakin shi a cikin cupin ya kurba gulps har sai da ya karar ya ajiye.

Hararran gefen ido tayi mishi jad'e da  turo bakinta tana pouting while looking down disappointedly.

" shine ka shanye mun smoothie, kasan kuwa banyi breakfast ba na fito" ta fada.

Dariya mai sauti yayi wanda ya janyoy idanun passers by in da suke wuce wa kafin ya gyara zamashi akan bench in gamida da cewa.

" toh sarkin rowa yaudai na sha abin hannun, tunda kullum sai dai ke kadai ba a ma mutum tayi "

" aiko kasan I'm not like that, kowa yasan ban da rowan abin hannu " tafadi gamida rolling eyes in ta.

Murmushi yayi da yasa dimple din shi lotsawa kafin ya bata amsa.

"toh dai ni a kaina ban taba ganin haka ba " gwalo yayi mata yana kauce wa hannun da ta daga zata duke shi da shi. Juya idon ta tayi takalle shi, tun zuwan da yayi yanzu ne ta dago ido ta kalle shi. Asad kyakkyawa ne na bugawa a jarida, cousin in ta ne na wajen Baba amma mahaifiyar shi yar Sudan ce gaba da bayanta, shiyasa da ka ganshi ka san either balaraben morroco or Sudan. Asad has been her friend since diapers don dama kusan shekarun su daya kawai dai ya girme mata ne da wata hudu. Wannan kenan

****
" so what are you doing. " ya tambaya gamida lek'a screen in laptop in. Wasu maps yagan wanda akayi dotting wasu wajaje a jikin map in. Murmushin da ke kan fuskar shi ne ya kau a lokacin da kwayar idon shi tayi arba da abin da ke k'asan map din.

Wai yaushe Afra zata hakura ne yake tambayan kanshi. D'ago idanun shi yayi yasaka akan fuskarta da take kallon screen in with keen interest.

" Afra wai yaushe zaki hakura ne " ya jefo mata tambayan. Tone in voice din shi na nuna rashin dacewan abin da take.

Kallon shi tayi, ta gefan ido kafan ta d'aga kafadunta. " kai kafi kowa sanina Asad, kasan kuma bazan hakura ba sai na sami abinda nake so ".

Girgiza Kansa yayi yana mamakin taurin kai irin na Afra, ko da ike bazai yi mamaki ba don kuwa tun suna k'anana take da wannan taurin kan amma baizata zata yi taurin kai akan abinda is risky ba.

" amma kisan wannan wasa da rayuwarki kike ko, you surely know how these men are. We are talking of a drug gang malama. Gaskiya ki chanza tunanin ki " ya fad'a a fusace yayin da yake furzar da iska daga bakin shi.

Ajiyar numfashi tayi, kana ta kulle laptop in kafin ta juya attention din ta ga Asad, wanda in yayi duba ranshi ya b'aci. Ko da yanayin fuskar shima ya isa yanuna iyakar b'acin ran da yake ciki.

" kasan alkawari nayi mata, kuma ni gaskiya ba zan karya alkawari ba. " ta bashi amsan ta atakaice.

" oh alkawari " yasaki wata yar dariya da batakai zuci ba. Girarshi d'aya ne ya d'aga yayin da yayi relaxing sosai a kan bench in.

" toh in ba ki ciki alkawari ba ai kya kai kanki lahira kuma in gayamiki in kin mutu ta dalilin haka Jahannam khalideena fi ha abada would be your final abode".

Girgiza kanta tayi. Ita ta kasa gane hail irin na Asad, yasani sarai bakyau k'arya alkawari, amma shine yake so tayi. " look brother, kawai ka tayani da addu'a that's all I would need " tafada nonchalantly.

Girgiza kanshi yayi kafin ya tashi, excusing kanshi yayi dan yanada lecture at that time kafin ya barta a wajen cike da kala kalan tunanuka. Wannan kenan.

*****
Fitowa tayi daga cikin motarta bak'a k'irar BMW, sanye take da pink gown na material mai embroidery a gaban, mayafi pink ne yafe a kanta, jakar birkin ce bak'a sagale a hannun ta.

Kulle kofar tayi kafin ta fara takawa izuwa wajen shigan ASD mall. Ba ta fi taku goma ba ta shiga, straight hanyar wajen elevator ta wucce. Nan da nan ta shiga ciki Sabida daman a ground floor yake. Danna fourth floor tayi, yayin da ta tsaya jiran isowa floor in.

Ding!!! Sound in isowar ya buga, fita tayi tak'arasa saman rooftop inda restaurant/lounge in su mai sunan Shifu yake. Ta wajen outside view ta zauna yayin da take jiran wanda sukayi appointment in da ya zo. Bini bini takan kai duban ta ta wajen staircase in ko Zata ga mutumin amma haryanzu bai iso ba, a haka har ordern ta ya zo, waitress din ta ajiye mata akan table a gabanta.

D'an fara tsakurar abincin tayi, dan dama da yunwa tazo hasalima ita bata wasa da cikin ta. Tana ci abinci tana kallon wayanta, har lokacin dai hankalinta na zuwa wajen shigowan.
Ba'afi minti talatin da fara cin abincin ta ba, naga ta ajeyi cokalin yayin da ta kai duban ta ga wani dan saurayi da bazai wuce shekara talatin ko ashirin da tara, tahowa yake wajen da take, hannun shi dauke da wata brown envelope.

Murmushi ta sakarmishi a lokacin da ya iso wajen ta. Gaisawa sukayi kafin ya samu wuri ya zauna.

" I'm sorry na mana ordering abincin. I hope it's to your taste " tayi nuni da nashi untouched abincin. Murmushi yayi tare da mata godia, sannan shima ya fara ci. Ahaka suka ci in silence har sai da dessert din datayi ordering na cheese cake yazo. Sai da sukayi nak sanan suka fara sana'a wato abin da ya kawo shi.

Mik'a mata envelope in yayi yana mata bayanin abin da ke ciki, sosai tayi murna da hakan kafin ta fito da mak'udan kud'i daga ciki jakanta ta mik'a mishi, don daman tasan aikinsa na da tsada amma duk da tsadan kuma yana da inganci sosai don duk aikin daka sa shi toh fa zaimaka in dai a fannin bincike ne.

Sai da tabiya kud'in abincin tukuna kafinta tafi tana mai murnar abin da ya zo mata a saukak'e. Wannan kenan.

 AFRA Where stories live. Discover now