Babi na talatin da bakwai

1K 138 2
                                    

" in fa bakuyi sauri ba ni zan tafi na barku " ya fada ta cikin wayarta, bai tsaya jiran amsar ta ba ya kashe waya tareda cusata cikin aljihun wando shi. Sanye yake cikin wata brown shadda da akayi mata aiki ata wajen aljihun riga.  Dinkin na zamani ne wanda ba'a wani cika zare a kan shaddar ba, anyi sewing inshi to his size, yayi mishi kyau ba karya. Hula ce tangaran multi-colored sanye a hanshi, sai wani sheki yake tareda wani annuri yayi enveloping in shi, takalmin kafarshi kuma wani bakin sandals ne na Gucci, kamshi turarenan nashi mai dadi sai tashi yake.

Tsaye yake jingine da wata bakar mota kirar mesarati, Wanda ta sha wanki sai kyali take, daman ga bakin abu da daukar ido. A murtuke fuskar shi take, domin ko ya fara gajiya da jiran su Afran da yake yi, even though ko minti biyu bai cika da jiran nasu ba amma yana da wajen zuwa bayan gidan surukan nasa. Yau ne shi da su Sam suke son kawo karshen da aikinsu, although su Sam sun dan fara amma rashin lokaci da bai samu ba ya sa su pausing, da tuni sun gama ma, because they have a lot of evidence da zai sa ko yau ne za'a iya raiding gidan kashe ahu.

Yana cikin wannan tunanin ne yaji kamshin sassanyar turaren Afra ya bugo shi, daga idonshi yayi yaga har sun rigada suna karaso Kusa da shi. Afra ya fara kallo ya ganta sanye ciki wani red Hkg lace mai manya manya flowers, dinkin bubu akayi mata, kuma ya zauna mata a jiki, daurin ture kaga tsiya tayi kuma yayi mata kyau sosai, sai kuma wasu dankune na gold da ta saka a kunnen ta, wani bakin veil ta yafa a kafadan ta to complete the look. Fuskar ta tasha simple make up Wanda even though simple ne amma tayi kyau.

Hannunta sagale yake da bakin micheal kors  purse tareda takalmin shi Sanye a kafarta. Abida kuma Sanye take cikin Hkg pink coloured Atampha mai lace wace akayi ma dinkin bubu ita ma,  tayi kyau ita ma, gashi ita ma simple make up tayi, just like Afra itama the same daurin ture kaga tsiyan tayi. Murmushi ne kwance akan fuskokinsu yayinda suke karaso wajen shi.

Hada rai yayi kamar Wanda bai taba dariya ba, yana kallonsu daya bayan dayan kafin yace.

" kowacen ku either ta gyara daurin kanta ko kuma ta canzo kanton mayafin da zai rufe gada kanta har kasa"

Tsayawa sukayi cak suna mishi kallon mamaki, kowaccen su kallon jikinta tayi taga wani aibu, da kuma rashin dacewa a dressing inta amma basu gani ba, toh mai illar shigar da sukayi da zai ce musu haka.

" ya Faruq mai laifin shigar mu, are we not dressed decently."

Shakeke yayi, ya jingina da motar, ya sarke hannayen shi biyu a ta wajan kirjin shi, yana kallon su daga kasa har Sama, kai daganin kallon ma sai mutum ya sha jinin jikin shi, domin ko karar zaka gane kishin da kuma haushin nasu da yake ji, ganin su kwata kwata ma basuga aibun shigar tasu ba.

" yanzu wannan ne decent, jibe ki " ya nuna Abida kafin ya cigaba da.

" just look at what you are wearing, matar aurece kefa, amma kayanan is sewn to your size kuma a haka za ki fita da wani karamin veil ko wanne tom and jerry ma ya kalle ki, ga kuma wani dauri, just look at yourself don Allah, gashinki Wanda yake al auran ki a wajen hakan ne kuma zaki fita ."

Sai kuma ya juyo kan Afra wace tunda yafara wa Abida magana itama ta sha jinin jikin ta, gashi kuma yanda yayi ficifici da idonshi yana surfa ma Abida bala'i ita sai ta dan ji tsoro. Ba komai ya bata tsoro ba illa ganin yanda ya dau abin da zafi. Tasan Omar ba baya ba wajen fada amma bata zata fadan nashi har ya kai hakan ba, domin a yau ne ta gasgata zancen Abidar da take ce mata yayan nata mafadaci ne.

" ki je ki chanza daurin nan kuma ki hado da babban veil " shine kawai abinda ya iya cemata don wani takaicinta ma yake ji.

Shifa Omar a rayuwarshi ya ki jinin ya ga matar aure tana abu kamar wata budurwa, in lokacin tana budurwa ne tayi haka ba wai zai wani damu bane amma yanzu ai wani nauyin ya hau kanta, ya kamata ta san mai ya dace da wanda be dace ba. Gashi kuma Allah yayi shi daman da bala'in kishi, dama dama ma masu musu tsoron gida suna da dan nesa da inda yayi parking motarshi, don haka yana da yakinin ba Wanda ya kalli adon matarshi balle aje da jin kamshin turarenta da sabida tsabar dadin kamshin yake sashi wata duniyar daban. 

 AFRA Where stories live. Discover now