Babi na talatin da hudu

1K 127 9
                                    

I am dedicating this chapter to @HannatuDavid. Thank you for your support and comments.

______________________________________

Qarar jiniyace ke tashi Wanda yasa motoccin da suke kan hanya matsawa domin subawa masu jiniyar hanyar wuce wa. Motoci hudune kirar hilux in nan amma ta sojoji agaba, tareda wata bakar Maserati sai kuma wasu hilux in guda uku a baya, tareda tanka daya wace wani kurtun soja yake Tsaye da bindigar tana nunowa ta cikin passage way dakayi domin bindigar.

Omar ne yanzu a cikin Maserati a hanyar shi na zuwa jaji domin akwai wani meeting da suke da shi na gaggawa. Bama su dadi da dawo wa kaduna ba akayi mishi waya domin ana nemanshi, don haka ko wajen iyayenshi bai je ba ya kama hanya, Kawai Mommy ce ma ya kira domin sanar mata da meeting din.

Zaune yake a ta wurin owners corner, ya jinginar da jikin shi a kujerar motar, tareda da kallon waje ta cikin tinted glass, yana ganin yanda suke sharar hudu, motoci sai kauce musu sukeyi. Dan lumshe idonshi yayi domin gaskiya in ba don meeting da zasuyi ba, da beyi niyyar fitama ayau ba kwata-kwata, domin ya huta kafin gobe ya koma aiki.

Kallan wrist watch dake sakale a wrist na hannunshi yayi yaga 9am dot. Dan tsaki yayi domin meeting din nasu 10 ne, which means akwai sauran time. Tafiya dai sukayi mai nisa kafin su iso jaji. Shiga sukayi cikin military cantonment, sukayi tafiya mai nisa kafin suka isa division na su.

Parking motocin sukayi a wajen parking lot, da sauri kurtun da suke tareda Omar a cikin mota daya, mai suna Ozo ya fito daga gaba tareda saurin budewa Omar kofa. Kamardai yanda ya saba yauma hakan ce ta faru. Louis vuitton shoes in sa aka fara gani Wanda yake da initials in shi a jiki, wato UKM kafin ya fito da gangar jikinshi. Sanye yake cikin uniform in su, Wanda ya karbi jikinshi sosai, wajan collarn rigar  three stars ne da ya ke nuni da rank in shi, a ta gefan rigar shi wajen kirjinshi kuma sunan shi ne a ta right hand side sai kuma sunan kasanshi a ta left.

Duk kuratan wajen kamewa sukayi tareda mishi saluting. Mayar musu shima yayi kafin ya dunguma zuwa hall in da zasuyi meeting. Mara mishi baya sukayi suna mai tsaronshi, ko da dai sun san ba wai wajen enemies suke ba amma a hakan akawai Wanda zai iya shahada ya kai mishi hari.

Shiga yayi wajen yana mai ganin wasu daga ciki colleagues in nashi, ko da dai ba duka ne suka iso ba. Saluting juna sukayi kafin ya je wajen zaman shi ya zauna, daman duk kowa da sunanshi a wajen. Wajen da ya zauna Kusa da wajen general Sadiq NaAbba ne wani abokinshi Wanda suke dan dasawa da shi domin duk kusan halinsu daya.

Gaisawa sukayi da NaAbba a cikin raha da annashuwa.

" ango ango. Ya naga sai wani fresh kakeyi ne, it seems like amaryar tamu  na kula da kai fa " NaAbba ya fada.

Dan murmusa Omar yayi kafin yace.

" Alhamdulilah ".

" ai walahi banji dadin rashin zuwana wedding in ka ba, da banyi tafiyan nan ba ba abinda zai hanani ".

"ai na sanka da son zuwa biki.  ya ma su mommy suke hope dai komai Lafiya."

Dariya NaAbba yayi domin abinda Omar yace gaskiya ne, in akwai a reni Muje biki a maza toh NaAbba ne domin kusan kowani biki sai ka ganshi a wajen. Shikuma ba abinda yake sashi zuwa biki sai don kawai yayi rawa. A rayuwarshi yana bala'in son rawa.  Abinda ma yasa bai je bikin Omar ba shine lokacin bikin  NaAbba bai gari domin ya tafi wajen mahaifiyarshi can garin sokoto domin ance mai bata da lafia to dole ya dauki leave yaje don ya ganta.

" Alhamdulilah ,tasa mu sauki fa. Daman blood pressure ta ne ya hau , ta sama kanta damuwa, wai don Kawai har yanzu ban yi aure ba. Kasan dai yanda iyayen nan suke, sai susa ma kansu damuwa akan abinda ba mutumne yake yi wa kanshi ba ".

 AFRA Where stories live. Discover now