Babi na Arba'in da Biyar

939 124 17
                                    

Hada kayanta take, duk tayi kaca kaca da closet in, sabida tsabar bacin rai ma jikinta har rawa yake, ga wasu hawaye masu dacci da suke bin kan kuncinta. Ita tama rasa mai yake mata dadi, ta rasa wannan bakin cikin ne yafi wani. Na rashin cika alkawarin shi ko kuma na yi mata wasa da hanakali da yayi, ya ci amanarta, she trusted him bata zata haka zai mata ba, ta zata yanda yake babba haka yake da honesty da kuma cika alkawari, amma ashe ba hakan yake ba.

Share hawayen ta tayi da bayan hannuta kafin ta dauki akwatin da zata iya rike wa, sauran in ya sawake mata a zo a dauke mata su. Fita tayi daga dakinta ta kullo kofar, kafin ta sauko kasa. Wajan tsit ba motsin mutane domin ko su masu aikinta sun tafi gida don dama jeka ka dawo sukeyi.

Fita tayi daga gidan tareda zuwa inda motarta kirar audi r8 take, daman da dan dadewa Abbinta yayi gifting mata motar kawai dai don ba inda take zuwane so bata wani hawan ta. Danna remote in red audin tayi tareda saka jakanta a dayan side in, while ta shiga wajan driver's side. Zama tayi ta kuna motan ta dan tsaya domin oil in ya hauro kafin ta yi reverse ta doshi wajan da gate na gidan yake, ganin su Faruq a tsaya a wajan ko wa da bingidar shi a hannu ne ya sa tayi horn, amma ko motsi ba Wanda yayi a cikin su, kara yin horn tayi amma kamar ma basusan tayi ba.

Kashe motar tayi tareda fita daga ciki tana mai watsa musu harar.

" wai ya ina ta horn ne kun tsaya kamar bakwa jin na " ta fada a masifance domin fa daman Afra ba dai masifa ba, gashi kuma an tabo ta. 

" Hajiya sorry ohh na oga we come tell us not to let you out " Ozo ya fada yana dan risinawa na girmamawa.

" well I don't care if you follow what he said ,but just open the gate for me or am i a prisoner in my own house " ta fada tana zaru kyawawan idanunta.

" hajiya kiyi hakuri ki koma domin ya haramta mana amsa miki kawai mun amsa miki ne yanzu ma out of courtesy " Faruq ya fada tareda tamke fuskar shi.

Wani bakin ciki ne ya mamayeta haka kawai sai ta ji hawaye ya fara zubo mata, don kar suga kukanta haka ta Juya ta koma cikin gidan tareda barin motar a parke gaban gate, don ko ma ta kan motar bata bi ba.

Zuge labulan windown yayi ya kule bayan ya ga shigarta cikin gida. Tun dazu yake tsaya a ta windown yana kallon abinda ya faru, ganin ta shigo har ya ji bugun kofar dakinta ne ya bashi daman fita daga nashi, dakinta yaje ya murda zai bude amma ya ji shi a kulle, sai ya bar wajan ya sauko kasa. Inda su Ozo suke yaje tareda kara musu kashedin su sa idon kar su bari ta fita, shikuma sai ya shiga motar tata ya dawo da ita inda take tareda dako a kwatin nata ya fito mata da shi. Wannan kenan.

****
Tana jin ana buga kofar amma taki bude wa,kuma tasan ba kowa bane sai Omar domin kullum sai yayi mata magiya amma bata ma kulashi balle taji abinda yake chewa. Rabonta da ta ganshi yau kwana biyu kenan, tun randa su Ozo suka hanata fita bata kara bari sun hadu da shi ba. Tana bari sai taji tafiyan shi sai ta fito tayi abinda zata tayi, da zaran kuma ta ga lokacin dawowar shi yayi sai ta koma dakinta ta kulle. Abin mamaki kuma kullum bai gajiya da zuwa even though yasan ba bude mishi kofar zatayi ba.

Jin an dai na buga kofar ne yasata komawa ta kwanta akan gadonta, hawayen bakin ciki ne suka fara zaryo mata a kan kumatun ta. Ita tarasa wani irin naci ne da shi da bai zai barta ta tafi ba, ita ba wai son shi take ba kuma tana da yakinin shima hakan ne ta wajan shi, toh mai yasa ba zai barta ta tafi ba ko duk a cikin muguntar tashi ne da rashin tausayin da yake da shi.

Barin Omar kuma da yaji ta ki bude kofar sai ya fita daga gidan, gidan Abida ya je domin yana da yakinin in ita ce taje zata bude mata. Kwana biyun nan da yayi bai ganta ba yasa kwata kwata hankalinshi ba a kwance yake ba, ace bai ganta ba for two days, kuma mutum yayi ta kulle kanshi a daki in wani abun ya sameta taya zai sani.

Da sallama a kan bakin shi ya shiga, amsa mishi sukayi, ganin shi sukayi ya shigo cikin gidan. Abida kallon yayan nata take taga kamar damuwa a cikin idanun shi, gashi kuma taga ma ya dan zabge kamar dai Wanda ke cikin tashin hankali. Daa har zuciyarta ta fara hasaso mata ko wani abu ne ya faru da Afra amma sai ta tuna ko dazu dazu Sunyi waya da ita kuma tasan lafiyanta kalau, ko da dai daga jin muryar Afra taji kamar ma bata wani jin dadin amma dai Afran tace mata lafiyan ta kalau.

" Ya Faruq sannu da zuwa "

" Yauwa. " ya amsa mata

Gaisawa yayi da Affan Wanda yake mishi kallon tambaya ko wani abu na damun shi amma sai yayi murmushin yake don ya kawar mishi da wani kokwanto dake mind in shi.

" baabaa I need your wife's assistance" ya neme izini daga wajan Affan Wanda ya bashi batareda sanin dalili ba tunda yaga Omar bai sanar dashi ba toh ba hurumunshi bane ya sani. Bin shi Abida tayi zuwa gidan shi a nan ne yake labarta mata dalilin da yasa yake neman assistance inta, ganin shakuwar su da Afra ne yasa ya kirata, don maybe in ta ji maganarta ta bude kofar.

Abin ya ba Abida mamaki, wane irin bacin rai ne Afra tayi da zata kule kanta a cikin daki, ita tunda take da ita bata taba jin tayi irin haka ba. Kallon tuhuma tayi ma yayan nata tana mai tunanin wani irin abu yayi wa kawartata har tayi fushi dashi haka.

Suna isowa gaban dakin, Abida taje Kusa da kofar tare da murdawa taji ko abude yake amma ta ji shi a rufe. Kwankwasawa ta farayi.

" Afra " ta kira sunnanta tana mai jiran taji ko zata amsa mata amma taji shiru.

" Afra zo ki bude min " ta kara furtawa amma ko motsi ma batayi ba balle ta nuna da mutum a cikin. Numfashin ta taja a hankali kafin ta sake shi.

Afra na jinta, amma tayi kamar bata wajan, haushinta ma taji da ta zo, wato ita ga me dan Uwa shine take supporting in shi. Murguda bakinta tayi kamar tana gaban su, kafin ta kawar da kanta ta kwanta. Jin taki kula Abidar ma yasa ya ce mata ta tafi shikuma ya hau motarshi ya fita tareda jaddada ma su Ozo kar su sake su bari ta fita. Wannan kenan.

____________________________________________________________________________
Tohh another chapter.
Please vote, share and comment.

 AFRA Where stories live. Discover now