Babi na Arba'in da bakwai

949 117 9
                                    

" toh yanzu mai kika yanke yi kenan " Abida ta tambayi Afra.

Zaune suke a sitting room, tun dazu Abida ta zo wa Afra, wace ita Afran ce ta kirata domin ta zayane mata duk abinda ke faruwa, ko A bata bari ba da ta zo bata labarin dan taga ya kamata ta sani. Lokacin da Abida taji labarin nan ta shiga cikin rudani, gani tayi kamar ita ta jawo hakan ta faru, inda batayi wasannan ba da kila hakan bai faru ba.

On the other hand kuma gaskiya she is disappointed in them, sabida taga danyan kan da sukayi, kuma gaskiya ta tausayawa Afra domin ta san Omar ne da lefi, ko wajen waye shi za aba lefi sabida shine babba kuma shine yakamata ace ya fi Afra tunani ba wai ace shine ma ya kawo shawaran hakan ba.

" ban sani ba, shiyasa ma nakira, wallah kai na ya dauri ". Afra ta bata amsa.

" Kina son shi ".

Dan jim tayi domin bata san amsar da zata bama Abida ba, shin tana son Omar ko batayi, itama kanta bata sani ba.  " ban sani ba " shine amsar da ta kara bata.

Dan numfasawa Abida tayi.

" toh in ya sakeki fa, ya zakiji ".

Zuciyarta ce tabada wani sauti mai karfin gaske, she fears Abida might have heard the sound. Da tambayan Abidan da bugun zuciyar ta a tare suka fito. Batasan wani irin abu ne ba amma wani abu ya mamaye mata zuciya, ita dai tasan ba san shi take ba, amma kuma wannan abin mai yake nufi, shakuwace kenan ko ya. Abida na zaune tana kallon reaction in Afra, ashe ba kadai zuciyar ta ne ya nuna rashin son jin wannan kalmar ba harta a fuskarta ya nuna.

" your reaction shows that baki so ku rabu ".

Numfasawa Afra tayi tana ma massaging temple in ta kafin ta bude bakinta ta furta.

" baza ki gane bane, nifa rashin cika alqawarinsa ya bani haushi amma abunda ya fi damuna shine dalilin da yasa ya canja zancen shi daga agreement in da mukayi. Yes he fell in love with me amma abinda ya kamata ayi shine mu zauna mu tattauna akan issue in, to tell you the truth barazana kawai nake wa Omar, banda hankaline aure ko wata uku ba muyi ba ace har an rabu, rufa min asiri ince da su Ummi me ".

Dariya Abida tayi jin a sigan da Afra ta karashe maganar.

" toh dakike wannan maganar, da ya sake ki fa ".

Murmushi Afra tayi tace.

" kamar baki san wace ni ba, sai da na karance shi nasan abinda ze iya da wanda ba zai iya ba ".

Daga gira daya Abida tayi, tana me gyara zaman ta tareda cewa.

" ina jin ki, taya kika san haka ".

Murmushi ta kara yi kafin tace.

" ai kafin nayi hakan sai da nasan ya fara sona".

" taya kika san haka ".

" just take a look at me " tace tana nuna kanta .

" akwai Wanda zai ganni yace bai so "ta daga giran ta daya. Shewa sukayi suka tafa, Abida tace.

"amma ba kida kirkir. Taya kikayi haka ".

"  with my charms " tace tana fluttering lashes inta.

" kawai dai ina so ya gane kuskuransa ne".

" ai kin min dai dai. Ni dadi ma nake ji kina gwara shi, daman yayi mana mugunta kinga hakkin mu ne ya hau kanshi " Abida ta fada tana ta dariyar qeta.

Hararan wasa Afra ta jefe Abida dashi.  " dena ma mijina dariya. "

"toh masu mijin manya Allah ya so dai Muma Muna da mijin ".

Haka dai suka karasa labarin su cikin raha da annashuwa . Wannan kenan.

*****   

Zama yayi Kusa da ita yana me amsa gaisuwar ta, tunda ya fita da safe sai yanzu bayan isha ya dawo gida.  Kama su Salim da sukayi da kuma wasu yan ta'adda da sojojin da suka tura katsina suka kamo toh duk abin ya cude, domin investigating in yan ta'addan suke, ba ji ba gani, a wani barin kuma cukucuku sukeyi na shigar da su Salim kotu don a yanke musu hukunci domin suna da enough evidence da zai iya sa ayi musu daurin rai da rai.

" how was your day " ya tambaye ta yana me kallon gefan ta.

" Lafiya"  ta amsa mishi da dan murmushi. Nodding yayi ya mayar da kanshi kan kallon da takeyi, come dine with me ne da ake a tashar BBC food ta ke kalla. Tana son show in domin suna sata nishadi in dai ta kalla, shi yasa yawanci take kallon shi.

" what are you craving for " ya jefo mata tambaya.

" me " ta juyo da hankalinta kanshi tana me mamakin wannan sudden question in nashi, toh me yake nufi da haka.

Dan mirginar da kanshi yayi gefe kafin ya bata amsa.

" ace kizabi inda kike son zuwa kuma wani abu kike craving, what would it be" ya saka mata tambayar amma wannan a dala dala yanda zata gane.

" ummm " tace tana me tunanin amsartata sai da ta dauko kusan second uku kafin tace.

" if I say pizza would you take me to Italy to taste their famous cuisine"

Murmushi yayi jin abinda ta gama fada.

" I mean in Nigeria, kaduna state ma ".

Dan pouting tayi kafin kuma daga bisani tace.

" I am also craving for ice cream, so how about smart kids ?".

Tashi yayi daga zaunen da yake, yana me cusa hannun shi cikin aljihun wandon shi.

" jeki shirya mu fita, kuma five minutes kawai na baki. " ya fada tareda tafiya dakin sa. yasan in ba bata time yayi ba Afra zata iya shara hour daya tana shiri kamar wace zata canza wani abun nata. Itama jin time in da ya bata sai da tayi murmushi domin tasan halinta na nawa. Don haka tashi tayi ta wuce dakinta, amma kuma a kasan zuciyarta tana tunanin me dalilin shi na haka, ko duk wai don yayi wooing inta ne ta yarda ta zauna da shi. Abin ma dariya ya bata, amma in ko haka ne zata bi ta takun shi kuma sai ta bashi mamaki, hmm tana ganin be san wace Afra bane. Smirking tayi tana me nemo kayan da zata sa, wani black palazo pant ta dauko tayi pairing in shi da wata dark blue blouse, sai ta dako mayafinta blue tayi rolling head inta da shi. Mayafin na da girma domin ya rufe saman riganta gabaki daya. Mild perfume ta dan fesa Wanda sai ka matso kusa da ita za kaji kamshin turaren ma.

" sai da kika haura five minutes in nan " yace domin ya ji karan takon takalmin ta, yana me kallon agogan hannun shi.

"well mu mata ai Muna needing time domin mu shirya"

" please don't generalise, kice dai ke kadai domin duk nawan Abida ta fiki sauri ".

Murmushi tayi tana me rolling eyes inta. Tasan gaskiya yake fada, domin Ummi ta sha mata fada akan nawan nan nata amma ba yanda zata iya abin a jinin ta yake.

" kinyi kyau " yace mata yanzu da ya dawo da hankalinshi kanta. Kallon shi tayi taga shima sanye yake cikin wani black sweat pants tareda pairing dark blue tshirt shima.

" thank you. Surprisingly mun sa matching outfits, anya baka ga abinda zan sa ba ku " tace. Tsaye take hannun ta sagale da dan uwan shi, tana mishi kallon tuhuma.

Yar dariya yayi yana me shaking kanshi. Fita sukayi, ya shiga wajen driver, da har su Ozo za su karaso inda yake amma ya hanna hakan ne ya basu daman koma wa inda suke bayan da suka gaisa da Afra wacce ta amsa musu faram faram kamar ba abinda ya faru. Shiga cikin motan tayi , ya tuka su zuwa Smart kids, siyan ice cream sukayi da pizza wajan kafin ya fara yawo da ita cikin garin, sai da suka kai goma a waje kafin su dawo gida. Wannan kenan

______________________________________

Vote, share, and comment.

 AFRA Where stories live. Discover now