Babi na Ashirin da daya.

957 135 4
                                    

Jingine take jikin Ummi, kanta na dore akan cinyarta. Tsiyar da su suhaila da wasu suke mata ne ya cika dakin amma ita ko a jikin ta, gyarama kwanciyar ta tayi tana mai kar shiga jikin mahaifiyar tata.

" chab wayaga Ummi za a rabu da yar tilon yarta " suhail ta fadi tana mai dan musu kallon tausayi.

Murmushi ummi tayi tace . " sai hakuri ai kuma kowace mace ai hakan ne ke faruwa da ita ".

Shafa gashin Afra takeyi Wanda yasha mayuka masu kyau sai kyalli yake yi. Siraran hawaye ne suke trailing down kumatun Afra, tana mai jin zafin rabuwa da Ummi.

Ba a dade da kawo musu rahoton daurin auren ta ba taji duk duniyar ta tsaya mata, taresa jin dadi zatayi ko akasin haka. Ai batama jira jin wani congratulations da mutane suke tayi mata ba ta je dakin Ummi ta ci sa'a ta ganta ita kadai aikam hugging in Ummi tayi tafara kuka. Hakuri ummi ta fara bata even though itama sauran kiris ta zubda nata hawayi, Kawai dai bata su ta sa yarta a damuwane shiyasa ta rike nata.

Ahaka su suhaila suka zo suka same su, ko abinci ma a cikin dakin ummin taci kuma Kawai abinda ke tashin ta, sallah ne. Yanzu ma haka an sanar musu masu zuwa daukanta suna hanya ne shine ake neman taje ta shirya kafin su iso.

" kyale su habibty, tashi kije kiyi wanka kinji yar Albarka. " 

Nodding kanta tayi tana mai mikewa daga kwanciyar da tayi. Share mata hawayen da suka kwararo kan cheeks inta Ummi tayi tana mai tayata tashi tsaye.

Shiga cikin bathroom in tayi domin tayi wanka don a shiryata.

****
Zaman tayi a gaban Abbin ta, nasiha yake mata mai ratsa jiki da zuciyoyin mai sauraro. Yan daukan amaryan iso kuma harma angama mata fada Kawai na Abbinta ne ya rage kafin su tafi da ita.

" Allah yayi wa aureki albarka ya baku zaman Lafiya" 

" Amin " aka amsa mishi.

Ahaka aka tashi da Afra na kuka, hugging in ummi tayi tana kuka kamar ranta zai fita. Kowa na wajen sai da suka bashi tausayi domin ummin ita kanta sai da ta zubda hawaye.

Ahaka dai aka bambareta daga jikin Ummi aka yi waje da ita. Wata motace baka wuluk qirar audi aka sanyata a ciki. aunties in ta sai cousins inta da kuma wasu tsofafi su ne suka biyo ta.

Tafiya suka mai dan nisa kafin su isa estate in Maska. Ba a fi mintuna ba suka iso gidan su Umar. Fito da ita akayi, guda ne yafara tashi yayin da aka duguma ta zuwa cikin gidan.

Kaita akayi inda maman Umar take tare da kawayenta da Yan uwanta suke. Zama da ita akayi a kasan gefan ummi wace ta tari su da raha da murmushi.

" toh hajiya mun kawo muku yar mu amana, don Allah a rike ta da amana, in tayi wani laifi a hukutanta kamar yanda zaki hukunta yayan ki. ".

" ahh ai ni yata bata laifi don haka karkuji komai, kamar yar da na haifa a cikin na haka nake jin Afra " . maman Umar tafada tana me dago da afra daga kasa tana ajiye ta a kan kujerar Kusa da ita.

" ai kinsan karamin yarinyar ce sai da kwaba " daya daga cikin aunties in ta suka fada.

Yan zama sukayi, maman Omar sai nan da nan take da surukartata. Har ga Allah Umman Omar jin som Afra take har a cikin zuciyar ta. Basu wani dade ba ta ba da Umarnin kaita gidan ta Wanda shima a cikin estate in yake. Fita sukayi tare da wasu daga cikin yan uwan Omar aka wace zuwa gida nata. Gidan manshion ne babba, Wanda aka kawata shi da flowers masu kyau da grass. Gidan irin shi kalar hudu ne duk kuma na sabin angowane, duk kuma wajen gidan na kama Kawai dai ciki ne za a samu banbanci.

Gidan na dauka da parlors guda hudu, daki shida tare da bathrooms bakwai, sai kuma kitchen da laundry room Wanda yake a ta baya. Sojojine suke gadin gidan, bude musu gate akayi suka shiga.

Addu'a akasata yi kafin ta shiga ciki da right leg in ta. Cikin gidan ya kawatu iya kawatuwa kamar ma ba a Nigeria ba, daman dai Lerouge interior ce aka kira tayi mata decorating komai na gidan. Tsayawa ma fada irin kyau da yayi ma bata lokacin ne.

Dakin ta aka kaita Wanda yake a sama. Dakin babban ne mai silver coloured queen sized bed. Bedding in nata in silky ash ne da throw pillows a jere a wajen. Ottoman coloured bed in ne agaban gadon, sai kuma wani chest shima same color. Kofina hudu ne a dakin. Da wanda zai sada mutum da bathroom, sai na balcony, sai kuma wace zata kai mutu zuwa ga walk in closet, sai kuma kofar fita.

Nasiha sukayi mata sosai kafin su tafi su barta tare da kawayen ta. Yaye mayafin da ke kanta tayi domin ta samu damar shakan numfashi. Su suhaila sun fita daga dakin domin su karasa kallon gida. Duk inda suka leqa sai sunyi santin shi.

Sai da suka dau mintuna kafin sugama kale kalen su, jin qaran door bell ne yasa suhaila zuwa ta bude tana mai tunani ko mai makeup ce tazo. Ai kuwa ita ce tare da masu aiki sun kawo musu abinci. Basu wajen shiga tayi yayinda tayi ma makeup artist in iso cikin dakin Afra.

"Afra a zubu miki abinci ne, ankawo " ta tambaya Afra.

Shaking head inta tayi tace.
" A'a akoshe nake. ".

" mai kika ci, ko da yake ai kazar amarci na jiran ki. Ni dai barinji in ci sai mushirya. " 

Harara Afra ta shifeta da shi, itakuma tayi dariya kafin ta barta tare da make up artist in.

Fara mata makeup in makeup artist in tayi sai da suka dauki hour daya da rabi donma anyi salah isha. Saka kayanta tayi lokacin ma kawayenta sun shirya suma cikin shiga emerald green material tareda head in shi. Ita kuma wata red detachable gown ta saka. Tail in gown in ya rufe medium carpet in da ke shimfide a cikin dakin nata. Daukan hoton su madugu yayi kafin ta fita, aroosa da suhail suna mai rike mata rigar ta baya.

Gaskiya Afra ko makiyi ne ya ganta sai ya yaba, sai dai in bazai fada bane. Fita sukayi daga cikin gidan inda motoci ne na abokan ango suka zo daukar amarya da kawayenta.

Wata mota kirar audi r8 v10 ta 2020 kalar ash ce a parke, nan kuma su suhaila suka yi da ita. Suna isa wajen motar, aka bude motar ta wajen driver. Omar ya fito cikin wata dakakiyar shadda baka  wadda akayi wa aiki mai kyau da bakin zare, hular kanshi bakace wadda ta qara fito da kyaun shi. Shima dai ba karya yayi kyau MashaaAllah.

Dan murmushi yayi wa su suhaila Wanda suka gaishe da shi. Mai da kallonshi kan Afra yayi wadda itama shi take kallon. Sai da ya dauki minti daya yan karemata kallo. Wai yaushi Omar shine mai mata, wai shine mijin wata. Shi har yanzu abin ma mamaki yake ba shi.

Itama a wajen Afran haka abin yake, wai itace yau matar wani. Wai itace take da aure. Kara sowa yayi zuwa inda ta tsaya, su dama su suhaila sun bar wajen tunda suka gaisa. Tsayawa yayi a gabanta, height in shi yayi mata rumfa domin mashaaAllah Omar ba dai tsawoba.

Bazato ba tsamani Kawai tajita a jiki shi, hugging in ta yayi ya jawota kan faffadar kirjin shi. Abokan nasu su dai Kawai kallon ikon Allah suke, wai yau umar ne ke rike da wata mace. Chab amma Afra ta taki sa'a.

Itama Afra abinda yayi ya bata mamaki domin batayi tsamanin haka daga gareshi ba. Ba ma abinda ya kara bata mamaki sai kissing forehead inta da yayi tareda whispering out.

" welcome zawjati "

Murmushi ya mata. Murmushin da sai da yasata pausing for a bit. It tunda take da Omar bai ma taba mata irin murmushin nan ba, kuma ma wai mai yake nufi da haka, ta zata agreement insu ba hada jiki in a sense of rike hannunta and so on to mai yasa ya karya.

" ba haka mukayi da kai ba ". Ta ce mishi.

Ya jita amma yayi banza da ita ya nuna kamar bai san mai ta ke nufi ba, ya kuma sani amma kuma ya take sanin nashi. Ai ba haramun yakeyi ba, matar sa ce ta sunna so shi bai ga wani abu a wajen ba . Wannan kenan.

*************************************
Two updates in one day, huh na fa yi kokari,

Please vote, share and comment.

 AFRA Where stories live. Discover now