Babi na talatin da shida

1K 111 14
                                    

Bayan yan sakoni suka isa. Parking yayi a gaban gidan, duk suka fito. Mikawa daya daga cikin kurtun dake gadin gidan nashi yayi key domin ya sa motar a gareji, shi kuma yayi gaba , su Afra suna mai bin shi a baya. Bude kofar yayi da key, ya zare ki din tareda shigewa ciki ko barin musu kofar abude ma baiyi ba, sai Afra ce ta bude suka shiga tareda kulle kofar ta ciki da lock in da ke jiki.

Sama sukayi don yariga da ya yi sama abinsa. Tabe baki Afra tayi tana mai mamakin wannan sudden coldness in da yayi marring features in shi, amma bata tsaya wani pondering ba suka haura sama suma.

Dakinta suka shiga, Alwala sukayi domin an fara kiran sallar maghrib. Sallah sukayi kafin kowanen su ta hau yin su zikr a haka har aka kira sallah isha'i, shima suka gabarta tareda shafa'i da witr. Afra ce ta fara shiga ta watsa ruwa kafin Abida tayi, duk suka shirya cikin kayan barcin su. Ita Afra wata silk in riga da gajeran wando tasaka colorn pink, while ita kuma Abida tasaka rigar cotton baka da ta kaimata wurin gwiwa.

Daman basu wani dade da cin abinci ba, don haka ba mai jin yunwa a cikinsu, dan haka sai suka zauna a kan carpet, Abida ta fito da card na whot suka fara playing. Sallamar shi ce ta kara katse musu wasan.

" Afra kizo dakina ina jiranki" ya fada fuskar nan tashi a hade, yana kuma gama fadar haka ya fita daga dakin nata.

Duka da kallo na mamaki suka bishi. Ita Afra tunani take toh mai zata yi mishi da yake wani nemanta, ita tunda aka kawoto gidan ma bata taba taka kafarta taje dakinshi ba.

" kije kar ya gaji da jira, domin naga alama yau a Yaya Faruq inshi yake " Abida ta fada. Kalamanta ne ya dawo da Afra daga tunani da take. Itama ta lura yau kwata-kwata a wani sukwane yake ba wani annuri a fuskarshi. Tashi tayi taje cikin closet inta ta dauko wata bakar abaya ta saka tareda yane kanta da mayafi.

" barin je yanzu zan dawo, don haka kar ki kallamin cards ina ".

" In Shaa Allah bazan kalla ba" Abida tace tana mai dan dariya. Afra tana niyar yin magana aka kira wayar Abida jin tone of kiran ne ya nuna Affan ne ke kira sabida shikadai ne yake da different ringing tone a wayar Abida don haka sai ta fita batareda ta kara cewa komai ba. Wannan kenan

****
Bude dakin tayi wani iska mai sanyi, da kamshin daddadan turaren Omar ya bugi hancin ta. Ido tasa tana karema barin Omar kallon, part in shi na dauke da Palor ne sai daki da bathroom. Parlor kalar farine, da wasu fararen kujeru, jikin baton anyi hanging wani katon frame na black and white wanda ya bada wani aesthetic feel. Sai kuma wani shelve in golden colour wace aka jera original Chanel books, da su flower vases akai.

A ta bayan doguwar kujera kuma wani desk ne na glass da aka shimfida wani white fur rug a kai tareda dora wani golden tray wanda aka dora Hermes book tareda diffuser a kan shi. Parlor is looking pristine and elegant. Sallama ta yi amma taji shiru don haka sai ta karasa wata farar kofa da take zaton shine bedroom, knocking tayi taji shiru, kara knocking tayi amma kamar ba mutum sai da akayi yan sakoni kafin ya bude baki ya mata iso.

Shiga tayi da sallam a bakinta, amsa mata yayi a ta kasan makoshin shi.

" gani" tace tana mai tsayuwa a bakin kofa. Dakin shi take karema kallo. Ita mamaki take yanda mutum zai so painti baki. Dakinshi kwata kwata ba wani abu da za agani ace zai haskakashi sai dai farin popn da ke a ceiling, amma apart from that komai na dakin bakin ne, daga matte wall in zuwa ga bed in nashi harda bedding in ma silky black ne.

Dago idonshi yayi daga kan wayar da yake latsa wa yace.

" dodone ni da baza ki iya karasuwa ciki ba ".

Jim tayi na dan sakoni kafin ta karaso, kan stool in vanity in shi ta zauna batareda ta kara cewa komai ba, domin taga kamar rainin wayo yake son mata kuma tana jin ya fara mantawa da ita wacece, ya manta da Afra bata daukan wargi kuma ita kwata kwata isar shi bata wani daddarata da kasa, abu dayane ma yake dan sa ta sassauta mishi, abun kuwa shine yana dan mata kwarijin in ba haka ba da ta yaga mishi rigar mutunci.

 AFRA Where stories live. Discover now