Babi d'aya

2K 220 5
                                    

Tsaye take gab da rail d'in balcony in da yake ta wajen d'akin ta, ta d'ora hanayenta biyu a akan rail in yayin da tayi k'asa da kanta. Iska ce mai dad'i take bugowa, wanda take kunshe ta k'ananan droplets na ruwa da ake yi. Garin a lumshe ya ke ya yi bak'i kirin yayin da ake doka tsawa da walkiya.

Hakan bai sata komawa cikin lafiyayyan d'akin ta ba. D'ago da kyakyawar fuskar ta tayi ta kali yayyafin ruwan da ake, hannunta na dama tamika wajen, ruwan na sauka akan shi.

Tunani take yi akan abinda ya auku makon da ya wuce, ta kasa samun natsuwa, domin ba yanda taso ya faru  bane ya faru,  taso ace an fasa komai. Ta hanyan nan ne zata samu peace of mind kuma ta cika alkawarin da ta daukar mata, amma haka baiyu ba.

Afra ta tsaya a wajen har kimanin mintuna shida ba tare da tace komai ba, kawai dai tana tunanin hanyar da zata bi wanda zata cimma burinta ta yanda babu loophole a ciki da zai kara iya kub'u ta daga kaidin ta.

Ta sha Alwashin ruguza rayuwar shi kamar yadda yayi wa abin mafi so yuwa a gare ta, sai ta sa ya zama abin kwatance a duniyar nan, sai ya yi na damar da sai ya gwammaci da baya raye a doran k'asan nan. Wata tsawar aka k'ara yi ne ya sata dawo wa hayyacin ta. A hankili ta mayar da hannunta gefan ta yayin da ta juwa don kumawa cikin d'akin ta.

Kulle french doors in tayi, ta zage fararren curtains in da suke mak'alle a gaban kofar. Dumi taji duk ya mamaye jikin ta wanda da yake sanyi kalau, ta ku take kamar batasan yi ta je har cikin bathroom in ta, wanda ya tsaru iya tsaruwa. Komai na ciki silver ne daga kan Jacuzzi zuwa ga wash hand basin in, bathroom din mai girma ne wanda yake kunshe da part in da all birth necessities in ta ke wajen. Daga kan bathrobe ne zuwa ga towels.

Wajen wani kofa ta je, ta jawo handle in, tana bud'ewa ta shige ciki. Dako wani silky bathrobe tayi ma kunshe da sunan victoria's secret, a baya bathrobe in kuma sign in fiffike ( wings ) ne. D'auka taiyi ta fito kafin ta karzaya zuwa ga jaccuzin ta domin ta yi wanka.

****

Sakkowa take yi daga matattakalen bene, wanda yake in a curved shape, sanye take ciki riga Abaya milk colour mai faffad'ar hanu, jakar micheal kors ce mak'alle a hannun damanta yayin da ta kara iPhone x din ta kune wanda yake nuni da waya take yi.

Fuskar nan tatta fau ba makeup in banda powder da ta saka, sannan qwalin da ta zazzara a idanun ta, sai kuma nude lip gloss in da ke bakin ta.

K'afan ta na kai karshen stairs in, ta juwa zuwa hagun ta, masu aikin da ke share share da goge goge sukayi ta d'iban gaisuwa yayin da take maida musu da martani fuskan ta a sake.

Afra kenan ya ga Alhaji Muhammad safana wanda yake asalin dan katsina. Baban ta hamshakin mai kud'i ne wanda ya ake dama wa da shi a dunniyar. Ita ka dai Allah ya albarkace shi da wanda a hakan bai daina  gode ma Allah da kyautar da ya bashi ba.

Matar shi d'aya Hajiya Nabila al ansari wadda take yar jihar mali, amma zama ya dawo da iyayenta Nigeria, a inda tahad'u da mijin ta har sukayi aure. Hajiya Nabila itama babbar yar kasuwa ce wadda take zuwa irinsu china, turkey ,Germany da dai sauransu saran kaya. Tana da shaguna manya manya a garin kaduna. Shaguna da ake ji da su a fadin Nigeria.

Iyayen Afra sun bata tarbiyya dai dai gwargwado, tana da ilimin both a na boko da islama. Duk da sake wan kudin da take samun a wajen iyayenta bai sa ta watsar da tarbiyyar da suke mata ba , dan ita akwai ta da son taimakon bayin Allah, ga ta da tausayi da nuna so ga duk wani na k'asa da ita. Wannan kenan.  

*****

Ta wani dogon hallway wanda akayi painting in shi in white and milk ta wuce kafin ta k'araso wata double door kalar bak'i, turawa tayi tare da yin salama. Wata farar matace wanda takai kimanin shekara arba'in da uku zaune akan d'aya daga cikin kujerun da suka zagaye long dining din. Zaune ta ke da alama jiran yar ta take yi ta iso suci abinci tun da damar al'adasu tun tana k'arama tare suke cin abinci da Ummin ta.

" Morning Ummi " tace yayin da ta d'an rank'wafa ta manna wa Ummi peck a goshinta.

Ummi murmushi tayi irin na su na manya yayin da ta d'ago idanunta takale ta with tenderness kafin ta amsa mata tare da tambayan ya take.

" kalau Ummi,  where is Abbi " ta tambayi uwar tata yayin da take shirin zama kusa da ita.

" ya tafi office,  yau suna da meeting ".

D'an gajeran murmushi tayi yayin da tafara serving din abincin a plate d'aya. In da sabo to ta saba tashi da kwana ba tare da ta sa mahaifinta kuma mafi soyiwa a gareta a idanun ta ba. Ita har mamaki hakurin Ummin take yi. Sabida ace mijin ka inya fita tun safe bai kara dawowa sai dare, kai kud'i ma wani sa'in baiyi ba.

Haka dai suka zauna suka ci abinci without talking don daman haka iyayen ta suka sabar mata in dai ana ci abinci toh ba a magana. Wanan kenan. 

************************************************************************

Assalamu alaikum.
This is all I have for today.

To ayi karatu Lafiya but don't forget to vote , comment and like .

Smiling bay.

 
            

 AFRA Where stories live. Discover now