Babi na takwas

1.1K 193 4
                                    

Qarar Alarm in ta ne ya tashe ta duba time in phone din ta tayi taga tara ta gauta kuma lecturen su goma ne. mika tayi yayin da take furta addu'ar tashi daga bacci. Tashi tayi tashiga bathroom domin kimtsa jikin ta.

Yau sati daya kenan bayan dawowar ta gida, tunda ta dawo kam Ummi ta sa mata ido bata barinta tafita ita kadai, dama kuma suna mid semester break so batada excuse in da zata samu da zai sa tana fita ko dan samo wata hanyar da zata cima burinta. In ma fitan ya kama sai dai tayi da drivern ta Wanda aka samo mata zai rinka kai ta ko ina.

Bata ji dadin wannan abin ba, sabida Abin da takeyi tana yin shi ne in secret batason saka wani aciki balle kuma yanda Abin ya zama kar a dalilin ta wani ya rasa ransa.

Bata wani dade ba ta fito fully dressed, abaya ce a jikin ta ruwan kasa mai wide sleeves, tayi rolling head in ta da veil in abayan, hannun ta dauke da brown bag na Gucci tare da brown gucci shoes in bag a kafarta. Fita tayi bayan ta gama shafe jikinta da bakhoor.

****
Ta fito kenan daga lecture hall ta hangi Asad zaune a kan bench in da ke kasan bishiyar mangoro. Tafiya ta farayi da dan saurin domin ta cinmashi, tana isa kusa da shi ta zauna a gefen shi bayan tayi mishi salam, ta gefen ido ya kaleta tare da amsa sallamar a zuciyar shi. Kallon tuhuma take mishi jin bai amsa sallamar ta ba, kuma daman tana cike da shi, through out last week tana kiran shi bai picking kuma gashi ita ba halin fita balle taje gidansu da dubu shi.

"Asad have I done something wrong " ta tambaye shi yayin da take kallon yanayin fuskar shi. Fuskar ba yabo ba fallasa amma ko dago idonshi bai yi ya kalleta ba bale ma tasamu damar ya amsata.

Sighing tayi tarasa mai yake damunshi domin ita dai tasan ba suyi fada ba balle tace killa shiyasa yaki mata magana, toh mai ya ke damunshi.

Ta bude bakinta daniyar yin magana dayar kawartata da isso wurin, daman tun daga nesa ta hangosu shiyasa mata karaso in da suke.

" Assalamu alaikum " tace yayin da ta zauna a kan bench in.

Amsa mata sallam sukayi a tare Wanda ya ba Afra mamakin tayanda akayi Asad yayi magana, wato dai wannan yana nuna fushi yake da ita ko me.

" wai meke faruwa ne naga duk faces in ku a cikume ". Rolling eyes in ta Afra tayi kafin tace.

" hmm sai dai kitambaye shi Abida, dan ni kam ba abin dake damuna "

Wace aka kira da Abida ne tajuya kallonta izzuwa ga Asad wanda fuskar shi take a murtuke kamar bai taba dariya ba.

" Asad wai meke faruwane " Abida ta tambaye shi.

Tsaki yayi tare da tashi daga bench din da yake ya ba su wuri sabida shi ganin Afra ma kara bata mishi rai yake yi, balle kuma in ya tuno da abinda ya faru last week. Shi bai san maiyasa Afra take da taurin kai ba, akan wani alkawarin da ta dauka take son kai kanta ga halaka. 

Da dai shima yana supporting din ta tunda alqawari ne amma kuma tunda abin ya kai ga taba lafiyarta ai ya kamata ta hakura ba tanace sai ta iddar ba.

Tsaki ya kara ja yayin da ya furzar da isar bakin shi kafin ya karasa zuwa hall in da zasuyi lecture, daman sauran yan mintuna lecturer ya shigo, so sai kawai ya shiga ya zauna a row in da ya saba zama watou a tsakiya shi ba a baya ba kuma ba gaba ba, amma yau sai ya shiga cikin wasu maza abinda bai saba ba don kullin tare yake zaman dasu Afra da Abida, jim kadan su Afra suka kara so ko kallon inda suka bai yi ba ya dai maida hankalinshi kan abinda mazan dake kusa da shi ke cewa.

Girgiza kai Afra tayi tadan murmusa sabida ita abin na shi ma dariya yake bata. Kawai sai mutum ya dau fushi batare an san mai akayi mishi ba.
Samun wani wurin sukayi ita da Abida, suka zauna aikam dai da zaman su da shigowar lecturern bai wuce yan sakoniba.

*******       

Dalibai nai wasu na cikin ajin suna shirin fitowa whilst wasu na jikin kofar suna jira abude kofar su shigo duk don su sami seats a ta gaba. Fitowa su Afra sukayi hannunta time da na Abida suna dan taba hira. Dauko wayarta Afra tayi domin ta jira drivern ta ya zo ya dauke ta tunda sun gama lectures.

Daman da niyanta ta bi Asad bayan an tashi amma sai ta neme shi sama da qasa ta rasa, har ya tafi sabida bai son wani confrontation daga wajen ta.

Dan matsawa tayi gefe domin ta ji maganar drivern nata domin wajen a cike yake da surutun students din. Bayan tagama wayar da Salisu driver ne ta koma gun da ta bar Abida.

" Ya har Yanzu baki tafi ba " Afra ta tambayi. Domin Abida dai zuwa take da motarta ba kawota ake ba.

Dan numfasawa Abida tayi na nuna gajiyawa don sun wahala yau Sabida tun 8 suke school sai yanzu four suka gama.

" kin San ya Faruq ya dawo, so yau shiya kawo ni "

Bude idonta Afra tayi in a surprised way kafin ta furta.

" Daman Famous ya Faruq ya dawo ban saniba balle in je in mika gaisuwa ".

Dalillin da Afra ta kira shi da Famous shine because kullin Abida sai tayi musu maganan shi amma har yau basu taba ganinshi ba. Dariya Abida tasa ganin expression in da ke fuskar Afra.   

Ta bude baki zatayi magana ne wayarta ta fara ringing, dubawa tayi taga favorite bro a rubuce, dan matsawa tayi domin tajishi da kyau da ba laifi wajen akwai dan hayaniya.

*****
" kinga zo muje, ya faruq ya zo " Abida  tace ma Afra yayin da take mikewa.

Tashi itama Afra tayi tana mai cewa cike da annashuwa.  " wa yaga yau zanga famous Ya faruq" 

Dariya Abida tayi tana mamakin zumudin Afra, ko da yake ita ta jawo Sabida kullin sai ta basu labarin ya faruq wanda ba tada hoton shi balle ta nuna musu, don ya faruq wani irin mutum ne da shi taking pictures bai dameshi ba kwata kwata, ita har mamakin yayan ta yake bata na rashin son daukar hoto.

Jan Afra tayi suka je wajen da tace mishi tana nan a lokacin da yakirata. Mota ce kirar rolls royce phantom ta 2020 baka ce wulik sai kyali take parke a karkashin wani shade dake wajen parking lot, kowa yazo wicewa ta wurin sai ya juya ya kara kallonta kai wasu ma har zuwa suke a dauke su hoto a kusa.  Although basu San da mutum aciki ba.     

Itama kanta Afra sai da motar ta burge ta duba da tsari da kyan ta ke da shi, hanyar wajen motar Afra taga Abida tayi ita tabita a baya tana aiyana ko dai motar yaya faruq ne domin Abida ta taba ce musu yana da bala'in son motaci. Aikuwa tana cikin tunanin ta ne Abida taje ta kwankwasa windown motar ta barin driver's seat, sai da ya dauki wajen seconi biyar kafin ya zuge glass in motar, bawai kuma don bai jita bane Kawai dai ra'ayinshi ne da tsabar jiji da kai da isa dake daminshi.

Kallon kanwar tashi yayi yana daga mata gira daya in a questioning way. Dan rankwafowa tayi kafin tace.

" ina yini ya Faruq ".

Daga mata kai yayi batare da ya amsa mata ba. Dan pouting tayi kafin tace

" Yauwa ya F kasan Wannan friend in nawa danake baka labari akanta, to itace ta zo gaishe ka ".

Zuba mata idanu yayi yana son tuno da wace kawace tataba bashi labari akan ta. Nodding Kawai yayi mata don bazai iya tuno da wata kawarta ba kuma bai shirin sa wa kanshi ciwon kai.

Wuja wa Abida tayi ta jawo Afra wace ta dan tsaya dan nesa da su matsowa tayi kusa da motar, a kunyance tace.

" ina yini ya faruq ".

Muryar ta yaji ta doke kunan shine ya sa shi dagowa daga danna wayar da yake yi. Itama a lokacin da dago idanun ta ta sanya su akan nashi, ai sai jin kirjinta tayi ya bada wani sauti mai karfin tsiya, mamaki da al ajabi ne suka bayan a fuskar ta , yayin da shima gogan namu yake kallonta da tsantsar mamaki, da kuma familiarity  domin kuwa ba jin zai taba mantawa da mai fuskar nan.

************************************
Don Allah kuringa voting da commenting. Rashi commenting in kun yana sani jin kamar ba kwa jin dadin litafin nawa ne. Koma yana sace min gwiwa inji duk banji yin rubutun ma . Please vote, comment and share

 AFRA Where stories live. Discover now