Babi na Arba'in da takwas.

1K 125 9
                                    

" baabaa kana fa cin amarcin ka kaga yanda kayi wani fresh " Abdullah ya ambata yana mai kai wai Omar hannu su gaisa, musabaha sukayi da shi kafin ya zaune a daya kujerar da ke cikin parlor gidan sa.

Dan murmusawa Omar yayi amma ba wai yana da niyar bude cikin shi ba ne ya furta ma aminin nashi abinda ke faruwa da shi. Ba wai kuma don be yi trusting in Abdullahin bane sai don kar yaje ya fada mishi, shikuma Abdullahin yayi subul da baka ya fada wa Aisha, don yasan in dai Aisha tasan zancen nan kamar Mommy ta sani ne domin ba abunda zata rage a zancen nan, kuma shi zata sa a uku.

" toh ya Amaryar tamu "

" tana nan Lafiya, ina Aisha ne da Yaya na naga ban gansu ba " Omar ya fada yana mai waige ko zega shigowar su.

" Suna kai ma Ummanta ziyara ".

Jinjina kanshi Omar yayi amma bai kara furta ko da wata kalmar ce ba. Daman ya aka kare mutumin da ba wani damuwa yayi da magana ba gashi kuma wannan damuwar da tayi mishi cinkus a kwakwalwarshi, ta hana shi sukuni ko na second daya ne, alhini yake dan ko bacci gagaras sa yake yi, yana tunani wani amsa zai samu daga wajan Afra. Inda wata ce yanda yaga ta koma mishi faram faram zai iya hasashin kila ta sako ne, amma wannan Afra ce, kwata kwata bazai iya cewa ga abinda zai faru ba.

So many scenarios ne a kanshi akan abunda zata iya yi, she's unpredictable. Jin an tabo shouldern shi ne ya bashi daman dawowa daga tunanin da ya jefa kanshi ciki.

" ya kayi shiru, ko wani abu ne ke damin ka " Abdullahin ya furta yana me kara kallon shi tsaba, sai kuma yanzu da ya kalle shi ne yaga kamar akwai wani abu da ke damun shi domin yaga ya dan rame, ga kuma idanun shi da suke nuna gajiya da kuma wani abunda ba zai iya ganewa ba.

Murmusawa yayi yana mai jinjin kanshi domin kauda wani kokwanta da zai iya ziyartar abokin nashi.
" lafiyata kalau, kawai dai wani case ne na wasu da muka kamo yake sani tunani " be karasa zancen ba sabida it's confidential, kuma su duk amintakan su ba Wanda yake disclosing confidential issues wa dan uwanshi, shi yasa ma in dai suna tare basu cika magana akan aikin su ba.

" toh Allah ya kawo sauki, ya sa kuyi galaba a kansu " ya fada sanin cewa wannan ne kawai amsar da zai samu daga wajan abokin nashi.

Labarin dunyi suka dako suka fara yi, duk da dai Omar wani sa'in sai dai yace eh ko A'a, domin shi fa surutu ba wai ya damu da yi bane. Amma kuma abunda yake daure mishi kai shine yanda yake iya zama yayi ta surutu da Afra, kai in wani ma Wanda be sanshi ze zata hakan yake ko da mutane ne.

*****
Two days later.

Murna ce da fargaba suka mamaye zuciyarta. A barin murnar yinta take sabida jin labarin za a mika su Salim kotu domin yanke musu hukunci and ta barin fargabar kuma tana fargabane kar a zo a basu wani sentence Wanda ba shi take so ba, don anata in an basu rai da rai shine zatayi farin ciki, ko da yake Omar yace mata suna da kwararun evidence da zai iya kaisu da zaman gidan yari na duk rayuwarsu.

Ina ma Samha na raye, tazo taga fansan da ta mata alqawarin dauka tayi shi, da yanzu tasan irin dadin da zata shiga ciki, da yanzu ta wanke duk wani bakin cikin dake ranta amma ina ta rigasu gidan gaskiya, amma addu'arta a ko yaushe shine Allah ya hada su a Aljannah. Jin wani abu me dumi na bin kuncin ta ne yasa saka finger ta ta goge ta ga hawaye ne, damana ta san tatsuniyar giza bata wuce ta koki.

Kullum in dai ta tuna da Samha sai ta zub da hawayen, she holds her so close to her heart, tana jin har ta mutu bazata taba mantawa da yar uwarta ba, ba jini daya suke da ita ba amma shakuwar da sukayi ko wani Wanda suke jini dayan ma ba suyi ba.

" Yaushe ne za'a shiga kotun "

Dauke idonshi yayi daga kan wayar da yake daddanawa, yana me kallonta da  tambayar da me take son sanin date in da za a shiga.

 AFRA Where stories live. Discover now