Babi na Hamsin da biyu.

978 106 2
                                    

MASKA ESTATE.
Shirye shirye tun yanzu mama Zalikha takeyi, duk mutanan cikin estate in su ba Wanda be sami labarin akwatin har uku da aka kawo wa maryam ba, kuma wai na nagani ina so. don haka mutane da yawa suna sintiri part in mama zalikha suna me bawa idonsu abinci.

Akwatinan ne guda uku aka ajiye su a tsakar parlor an bude su, a akwati daya atamfofine masu tsada, su exclusive super wax, sai kuma dayan akwatin kuma laces ne da materials sai kuma akwatin na karshi Veils ne da jakankuna tareda yan kunaye da sarkoki.

Duk matan yan uwa sai da sukaje domin sa albarka amma wasun su fa basu bar wajan nan ba sai da aka cika su da bakar magana barin ma mommy, ita kam ko a jikinta ma. A haka dai akayi ta Sama ma kayan albarka, daman kuma da suka zo an rigda an sa ranar bikin nan da watani biyu. Don haka shirye shirye suke ba kama hannun yaro, mama zalikha har  turkey suka je da yar tata domin sayo mata kayan daki, kama da su kujeru da gadaje.

An kashe makudan kudi a kayanan domin mama zalikha cewa tayi sai Sunyi kayan dakin da ku na Afra ba'ayi ba, ita dai ala dole da Omar take kishi, domin tana iya tuna lokutan da suka shude bayan an kai Afra Wato wa'enda sukaje kallon gida harda daukan hotuna, toh itama tana ai ayi wa yar tata haka.

Ba laifi kam tasiyo kaya masu bala'in kyau da tsada, bayan sun gama kuma sai da suka kara kwana a garin dumin bude ido kafin suka dawo da akwatin kamar guda goma, kum duk kayan sawan maryam ne, na Wanda intayi aure tayi amfani da shi, Wanda ake kira da hana gori kenan.

***
Bayan abunda ya faru tsakinin su wani soyayya suke sha ba kama hannun yaro, barin ma Omar kwata kwata son Afra ya chanja mishi lisafi, bawai kuma ya chanja halin na shi ne na rashin dariya ba, A'a kawai dai in yana tareda ita ne, sai ka rantsi ba shine me jijjida kan nan da izza ba.

Tsaye take jikin mirror na dakinta, sanye take cikin wani yardi na material Wanda akayi ma sinking bou bou, ta daure gashin kanta ata kasan keyanta, ta bar jelan na reto a tsakiyan bayanta Kusa da kugunta. Sunkuye take tana saka dan kune don haka hankalinta be kan ko ina sai abinda dake, hakan ne kuma ya bashi daman shigowa cikin dakin nata bada saninta ba.

Takowa yayi har inda take amma bata sani ba, sagala hannun shi yayi around her waist, dumin hannun mutum da taji a kan cikinta ya fargar da ita da zuwan nashi. Juyawa tayi da Murmushi a kan fuskarta tareda furta.

" good morning".

"morning " yace yana me leaning yayi capturing lips inta for a second kafin ya kara cewa.

" har kin shirya ne "ya tambaye yana mai dan plucking lower lip inshi.

" as you can see na ma bagama " tace mishi tana me futa daga rikon da yayi mata tareda zuwan kan gadon ta inda ta ajeye wani gajeran baki hijab da zai kai mata iya gwiwa ta saka shi, aikam ya zauna a fuskar nata ya kara ma fuskar kyau ma.

" wai dole sai kin je ne " ya kara jefo mata tambayan yana mai matsawa Kusa da ita.

Dan dariya tayi tana me girgiza kanta.
" makaranta fa zanje ba wani waje ba, taya zakace ko dole sai naje" ta fada mishi tana me har hada jakan da zata da ita makaranta, tun last suka koma toh ita bata koma ma sabida sai da ta gama registration da komai, don haka yau ita da Abida za su koma tare, domin sun ma ji labarin wani mayen lecturing har ya fara lecturing.

Dan shiru yayi fuskar shi de bai nuna yana son tafiyanta ba amma haka ya hakura, ko da ike shima fa yana da wajan zuwa, tun yanzu ma a haka ita yake jira ta shirya sai ya kaisu daganan kuma yaje wajan aikinsa. Rike mata jakanta yayi suka fito daga dakin. Sauka kasa sukayi suka nufi wajan dinning domin karyawa. Sai da cikinsu ya dauka kamin su fito daga cikin gidan.

Yau beyi niyar barin driver ya tuna shiga don haka karba key yayi daga driver yana me umartashi da ya bi motar su Faruq. Shiga motarshi kirar audi yayi itama tashiga while yaran shi kuma suka hau motocin da suke bin shi da shi.

Sai da ya tsaya a gidan Abida domin daukanta don ita ma su za ta bi, sabida Affan be gari yayi tafiya wani seminar don haka sai ya roki Omar ya kai ta don da ba wai yayi niyar kaitan bane. Ba su wani jima ba suka fito tareda Afra daman kuma suna isa Afra ta fita domin yi mata magana. Sanye Abidar take cikin wani bakin abaya da akayi mishi ado a ta gaban da kuma hannun. Ta dan kara kirba kadan ta dalilin shigar cikin da take da shi na wata hudu yanzu, cikin be wani fito ba dan haka kawai dai haske ta kara da kuma kyau da yayi mata.

Shiga ciki sukayi tana e gaida Omar. Ya amsa mata faram faram har yana me tambayar ta ya babyn su yake, ta dai amsa mishi da Lafiya sabida ita har yanzu in aka tambaye ya lafiyar dan cikin nata kunya yake sata. Wannan kenan.

***
Haka rayuwa tayi ta tafiya da dadi ba dadi haka dai har aka shiga sati bikin maryam, mama zalikha tayi rawan gani bikin nan domin ta gyara yarta gyara na musamman domin in ka ga maryam yanzu ma za ka ga ta canja ma, tayi dan qiba ga hasken da ta kara kamar ka taba jini ya fito. Haka dai sai shirye shirye akeyi, yaune ma ake kamun ta Wanda za suyi a side resort. Ta kowani bari a gidan shirye shirye akayi domin zuwa wajan kamu kar suyi african time domin a invitation in an sa no African time ma sabida prominent mutanen da suka gaiyata.

Gida aka ware daban aka bama maryam da kawayenta abin mamaki kuma har da su Afra ta saka as bride'smaid inta ba wai don har yanzu tana son Afra ba, A'a sai dai wai ta nuna itama Allah yayi zata auri mai kudi Wanda ma kudin baban yaron ya so fin na daddyn su Omar. Toh shine itawai as let by gones in nan. Da Omar ya ma su hana Afra amma sai da mommy ta sa baki ya barta, don shi har yanzu ba wai yayi trusting insu bane.

Yanzu haka ma su Afra suna shiryawa ne, sanyi take cikin wani yadi na kampala black mai ratsin pink a jiki da aka mishi dinkin boubou irin na yan nijar inan. Duka haka maryam ta sa kawayenta yin dinkin domin tela dayane ma yayi musu dinki.

" ki bar gashinki a wajan mana sai ya fi kyau " wata kawar maryam me suna Sara ta fada a lokacin da taga Afra na kara ninke gashinta domin in ta zo dauri kar ya fito.

" rufa mata asiri Kina so ya Omar ya hanata tafiya kenan " maryam wace ake ma makeup ta abanta ba wai kuma abinda ta fada har ya kai har cikin zuciyarta bane, A'a wai ita dai kawai kar ace batayi magana ba. Haka zalika mutanen cikin dakin sun yi mamaki wannan furucin nata, domin Wanda suka sani sun san har yanzu ba wai tana sonta bane.

Dan waro idanu ta Sarah tayi tasan ko ba a fada ba wannan ce matar ya Omar in da kawarta ta mutu akai. Dan murmusawa tayi wa Afra tana jin son Afran a cikin ranta, a zuciyan ta ko ganin wautan maryam da maman ta suke a lokacin da suka so Omar ya auri maryam, ai da ta kade in dai wai kishi taso yi da Afra, ba don komai ba domin taji labarai da yawa akan Afra daman dai kawai ganinta ne bata taba yi ba.

Haka dai suka gama shiryawa, sai da aka dauki pictures in su, sai da aka dauki video wellwishers daga yan tsiraru kawayenta kafin su dunguma zuwa wajan, Wanda ya cika makila da yan uwa da abokanan arziki. Shiga sukayi ciki suna dan tana rawa, wasu dai a cikin kawayen ba su yarda ba domin irin taken rawan nasu sai da ya burge mutane, ita kanta amarya sai da ta taka daman gsta yar san rawa. Haka dai suka shiga suka zauna, sai kuma aka bude taro da addu'a bayan an gama ne aka zo yin ciniki da yan uwan ango. Aikam sai da suka chabki kudi kafin su bari a bude fuskar amarya, haka dai sukayi ta rawa suka gama, ango ma daga karshe ya shiga da tawagar abokan sa, aka dauki hotuna da dai sauran su.

Daga karshe su Omar da su Affan suma suka dau hoto da Amarya da ango kaman su dauki matayen su suyi gida da su, don sun ga mutane ba suyi niyar barin wajan ba. Wannan kenan.

____________________________________________________________________________

Kuyi hakuri da rashin samin update, uzurine yayi min yawa.

Vote, comment and share.

 AFRA Where stories live. Discover now