Babi na Arba'in da Uku

941 135 5
                                    

Zaune take tareda Abida a parlorn dake gidan Mommy suna kallon chopped challenge, mommy ce ta fito cikin shigar alfarma ta wata expensive lace kalar jaa, kayan ya karbe ta domin ko daman mommy fara ce kuma dai jan kala daman na ma farare kyau. Sagale jikinta yake da mayafi blue Wanda ya shiga da tufafin nata. Kamshin turarenta kam mild ne don sai mutum ma ya matsu dap da jikinta zai jishi, kuma ba ma mai irin tashinan bane.

Wuyanta da kunenta duk sakale suke da dan kunen gold masu kyau da tsada, gakuma wasu zuben gold guda biyu da ta saka a fingers inta sai kuma bangle dan babba da ta sa a hannunta na dama. MashaaAllah Mommy tayi kyau sosai.

" Mommy har kin fito " Abida ta tambayeta bayan da suka ji shigowar mommyn.

" eh fa, yanzu nake son tafiya ma don naga har na danyi letti " ta fada tana mai gyara golden wrist watch inta na micheal kors dake sagale a hannunta na hagu. Dinner bikin yar kawarta Hajiya Safiya zata Wanda matar ta gayyace ta even though ba wai kawar ta kut da kut bace amma dai suna mutunci da ita sosai.

" mommy mashaa Allah kinyi kyau " Afra ta yaba tana mai sakar ma Mommy murmushi.

Murmushi mommyn itama tayi tace. "nagode daughter, kinga da mun sami Omar a waya ai da kin raka ni ".

" wallahi ai banji dadi ba " tace tana mai pouting. Tun dazu suke neman Omar a waya amma basu samishi ba sai suke tunani ko ya shiga meeting ne, domin daa mommy tayi niyar fita da Afra amma ai bata dauki yarinya ta fita batareda izinin mijinta ba, don itama sai da ta tambayi nata ya bata izini kafin ta fita. Abida kam sakin baki tayi tana kallon ikon Allah.

" toh su daughter manya, ni ko tayin ma ba ammin ba ".

" toh ai ke kintashi daga daughter na, wannan hurumin Ammin ki ne, ince jiya da zata fita ba tare kuka fita ba ". Mommy ta ambata tareda kara cewa.

" don haka ni ma sai ki barni da daughter na " ta karasa da dariya ganin yanda Abida tayi kicin kicin da fuska. Itama Afra dariyan tayi tana ma Abida gwalo.

" lalle ya Faruq ya kamata ya dawo in bahaka ba mommy zata ce bata ma san shi ba ".

" ai ko ya dawo ko bai dawo ba ni na sami sabuwar ya sai dai fa Kuyi hakuri " Mommy ta karasa a sigar wasa.

Duka dariya suka sa mata kafin sukayi mata rakiya waje. Komawa sukayi ciki suna ta hira kala kala kamar Wanda ba abinda ke damin su. Toh zance Abida ba abinda ke damunta, Amma Afra wannan case daban ce domin tun jiya tunani suka bi sukayi mata yawa. Abinda bafa ta saba ba kenan, shine yawan tunani. Amma gashi Omar yayi abinda ya sata kwanan tunani. Ita ta rasa ma ya zata danganta maganan shi na karshe, mai yake nufi da haka, agreement in su ina ya tsaya. Ya kasa kama Salim ne yasa yake maganar nan ko kuma me, domin dai tasan tunda yayi mata alkawarin yana kama Salim zai rabuda ita. Toh ya kasa Kama Salim ne, in toh hakan ne yana nufi bai shirya rabuwa da ita ba kenan anytime soon.

Amma da tayi bakin ciki, don ita a rayuwarta bata son taga ba ta cimma abinda ta sa wa ranta son sai tayi ba. Don dai ma bata son karya alkawarine da tuni tace ya sawake mata. Tasan auran su ba mai dorewa bane, da ba agreement inan ita mai iya hakuri ne ta zauna da Omar, ko da dai ba auran soyayya sukayi ba, amma tasan watarana they might feel something for each other.

Jin an tabo ta ne ya dawo da ita  hayyacinta.

" lafiyan ki kallau kuwa " Abida wace taga Afra ta lula cikin duniyar tunani ne ta tabo ta.

" eh"  ta amsa mata amma kamar hanyanzu hankalin nata bai wajan.

" ko dai, ko dai " Abida ta kara fada, tareda daga girar ta tana yar dariya.

" ko dai me " Afra ta tambayeta tana dan hade rai domin ta so gano abinda Abida ke nufi.

" ke banza ce toh tsoranki zanji don kin hada rai da bazan fada ba. Mai ya hanaki bin mijin naki, in kisan zaki zo Kiyi ta lulawa duniyar tunanin shi ne. Murmushi Afra tayi batare da ta bata amsa ba, tareda shrugging shouldern ta in a kya tayi way.

 AFRA Where stories live. Discover now