Babi na Ashirin da biyar

1K 175 5
                                    

parking motar yayi a gaban habil cafe.  Wajen bai wani cika ba domin ko tsirarun motacine ma a parke a wajen. Kashe motar yayi, tareda cire key in motar. Kallon gefan shi yayi yaga har Afra ta bude kofa domin fita, dauko wayoyin shi yayi yasa a cikin aljihun shi kafin shima ya fita. Kule motar yayi kafin su jera su shiga cikin cafen.

Iska mai sanyi ce ta bugosu a yayin da suka shiga ciki, wurin kamar dai yanda yake a wajen haka ma cikin ba wasu mutane, daga wasu family of four, sai wasu yanmata guda hudu sai kuma su Omar. Wani secluded waje ya samar musu suka zauna kafin wani waiter yazo wajen su.

" good morning sir, ma'am " ya gaishe da su tareda mika musu menu.

" morning, "  Afra ce ta amsa musu tana mai mishi murmushi.

Kallonta Omar yayi ya dan hada rai kafin ya kai kallonshi kan waitern

" we will call you when we are ready to order " ya fada in a dismissive tone.

Dan murmushi waitern yayi kafin ya barsu. Kallon menu ta fara yi, tana duba abinda ya bata sha'awa, yan sakoni ta dauka kafin ta aje menu in.

" are you ready to order " ya tambaye ta yana mai kallon cikin kwayan idonta.

Nodding tayi, kafin ta kai duban ta ga wajen tana dan kale kale, tana yawan wuce restaurant din amma bata taba tunani tsayawa ta ci abincin wajen ba, she just hopes that yana da dadi. Daga hannun shi Omar yayi, yayi snapping fingers in shi wa waitern.

Zuwa yayi ya karbi ordern su kafin ya tafi. Dora right hand in ta tayi a kan table while using her left tana dan duba Instagram in ta. Kallon hannun ta yayi da yasha bakin lalle, ga kuma jan lalle da ya zagaye dogayen fingers in ta. Abin ya bashi sha'awa, domin shi a rayuwarshi yana son ganin mace da lalle.

Yana cikin admiring lallen tane suka ji salama akansu. Dago kanshi yayi ya kale yammatan, mata biyu ne Wanda suke tareda kawayen su amma ganin shi ne ya sa su zuwa wajen shi. Suna daga cikin matan da ke bibbiyar shi. Kallo daya yayi musu ya watsar.

Afra ce ma ta dan musu murmushi tareda amsa sallamar tasu.

" Gen. Omar how are you " daya daga cikin yammatan ta fada.

" Lafiya"  ya fada a kasan makoshin shi ya na mai mamakin yanda suka san sunan shi, amma kuma ai bai kamata yayi mamaki ba tunda dai haryanzu yammatan da suke bibiyarshi basu dai na ba.

Kallon Afra yayi yaga mai zatayi sai yaga ma ko kallo matan basu isheta ba.

" wannan sistern kace ". Wannan tambayar ce ta kawo da hankali Afra kan matan.

Kallo take musu na mamaki da iya jure rashin mutunci. Su yanzu suna a matsayin su na mata in ba namiji bane yayi musu magana ai ba sayi degrading kansu a wajen na miji ba.

Shaking kanshi Omar yayi, sannan ya daga kanshi ya kalle su. Still shi suke kallo suna jiran amsar sa. Hannun Afra dake kan tabirin ya damka. Haka ko ba karamin bata mamaki yayi ba, kafin kuma ya kai shi kusa da shi, tafin hannunta yayi ma short chaste kiss, yan mai kallon yanayin yammata.

" matatace, " ya basu amsa with finality. Aikam sumsum suka wuce domin ba karamin haushi ya ba su ba, Wato su duk wahalar son nashi da suke shi bai ma damu ba, sabida kuma ya raina musu yawo shine har da wani kissing mata hannun ta, toh dadin abindai suma ba masoya suka rasa ba.

Ita Afra abin ma dariya yabata, tunowa kuma da abinda yayi sai ya sa ta damke fuskar ta tareda cewa.

" ewww " ta fara goge tafin hannun ta a jikin sleeve in rigarshi. Shi abin ma dariya ya bashi, aikam sai gani tayi ya fara dariya. Ita a kullun tana mamakin yanda Omar yake finding wasu abubuwan funny, ita fa bata ga wani abin dariya a abinda take ba, hasalima haushi taji. Don mai zai samata yawun shi a hannun ta.

 AFRA Where stories live. Discover now