Babi na sha takwas.

972 150 7
                                    

" wai ina zaka ne " Uncle H yayi masa tambayar.

Tunda suka fito daga gidan sukayi ta yauwo, gashi haryanzu ten pm ma yayi, amma bai ga sun zo destination in da zasu ba. Yin shiru Umar yayi batareda da bashi amsa ba, yana dai tukin nan nashi a hankali kamar Wanda baida wani damuwa a zuciyarshi.

Amma kuma damuwace tayi mai fal azuciya. Yarasa abinda yake masa dadi. Wai shine yau babanshi zai bude baki yayi tunani hadashi da yar witch in nan. Shi a rayuwar shi ba macen da yaki jini irin mama zalikha kokuma muce witch inji shi. Tun ba yau ba shi ya lura da yanda matar take, kwata kwata akwai ayar tambaya akan ta. He does not even trust her, tana mishi kamada munafukai, ko kuma yace tana da sufan munafukai.

Tsanar da yayi wa uwar ne ya koma kan yar daman kuma itama yar ta gado halin Uwarta ta ciki da wajen. Huro iska mai zafi yayi daga bakinshi, yana mai jin bakin ciki na nukurkusowa a cikin shi. Kwata kwata natsuwar shi ta kaura, ya rasa gane mai ke mishi dadi ma.

Toh ko dan sabida shi auren ma ba a gaban shi yake bane, ya sa yake jin zafin kara tattabo mishi wani karin aure da ake niyar yi. Amma ai ko lokacin da aka je mishi tambayar Afra bai ji bakin cikinan ba, hasali ma wani farinciki marar misaltuwa yashiga ciki da yaji faruwar haka. Amma na maryam kam, ko da ma dai an watsar da zanci, still abin na mishi zafi. Bai kaga yin auran farko bama balle a kawo mishi talan wata.  

Tafiya yayi mai nisa, har ya iso bridge in da taraba old kaduna da new kaduna, haurawa yai yayi tafiya mai nisa, sai da ya iso millennium city kafin ya karya kwana ya shiga ta ciki.
Shidai Uncle H nashi kalo ne kurum bai sake magana ba tunda ya lura mutumin nashi bai jin yin zance.

Shiga sukayi ta gidajen, har sai da suka wuce su , suka shiga cikin daji.

Shi bai ma jin tsoro kidnappers Uncle H ya ambata a cikin zuciyarshi.

Ahaka dai a cikin gargadar nan yayi ta driving har suka iso gaban wani black metal gate, wanda akayi shi mai stripe, control ya dauko daga pocket nashi yayi dailing wani number. 

Uncle H shi dai Kawai kallon mamaki yake bin Omar da, yana mai tunani inda Omar ya kawo su. Wani blue light ne ya hasko su, kafin gate in ya bude. Cusa kan motar yayi cikin log house in shi Wanda banda mahaifiyar shi da Abdullah ba Wanda yasan yana da shi. Shima Abdullahi adalili kade Afra da yayi shi ya jawo ya sani.

" wai Omar ina ne nan " Uncle H ya ambata yana mai kare wa gidan kallo, yana sha'awar yanda aka ginashi.

" my house " Omar ya fada a takaici. Kashe injin motar yayi bayan ya sata a parking lot. Fita yayi daga motar, da Uncle H following suit. Tafiya sukayi ta kan cobble stone in da aka jera akan kasan gidan.

Tawani hanya da aka kawata wajen da manya manyan bishiyu Omar yanufa, tare da Uncle H mai bi masa. Tafiya sukayi kafin su iso, glass kofar da zata sada mutum cikin gidan. Gaban gidan a kawace yake da shrubs da flowers yayin da half gaban da glass akayi shi dayan half din kuma da log.

Danna thumb in shi yayi a wani wajen da ke needing thumb print, wanda ya bawa black wooden kofar daman bude wa. Shiga yayi ciki, uncle H shima ya shiga yana mai kullo kofar.

" kai Umar wani irin iskanci ne wannan, yaushe kayi wannan gidan " Uncle H yafada in amazement yana bin gidan da kallon mamaki da awe a fuskar shi. Gidan yayi mishi kyau ba karya. Wasu parts na gidan duk black colour ne, kama daga painting in zuwa kujerun da wasu appliances, Kawai palone all white. 

Shaking head in shi Umar yayi kafin yace " ban wani dade ba,  kasan da ga kai sai Ummu da Abdullah ne suka san da gidan nan. ".

" toh mai ya sa hakan " Uncle H ya tambaya yayin da yake takawa zuwa ga all white sitting room dake jone Kusa da front door in. Zama yayi akan kujera yana mai jiran amsar Omar.

 AFRA Where stories live. Discover now