Babi na talatin da biyar

988 111 1
                                    

" yau zaka koma kenan " NaAbba yayi magana yana mai karasowa inda Omar ke tsaye. Daga kanshi Omar yayi tareda ce ma NaAbba.

" yau na ke son komawa, cause na baro wani pending work kuma ma akwai wani group da za'a tura katsina so ina so inje inga yanda training din nasu yake. "

Jinjina kanshi NaAbba yayi tareda mika hannunshi suka gaisa da Omar.

" toh shikenan, Allah ya kiyaye hanya, nidai akwai pending work in da ban gama ba amma In Shaa Allah, in na shigo cikin gari, zan biyo in gaida Amarya. "

" amin amin. Nagode sai na ganka"  Omar ya fada.

Kowa kama gabanshi yayi. Shi Omar wajen da motocin su yake yayi, Ozo ya bude mishi ya shiga ciki. Tafiya sukayi mai dan nisa sabida daga cikin gari zuwa jaji akwai tafiya. Yau ma kamar jiyan sun kunna jiniyar hakan kuma ya basu daman ratsawa ta cikin motoci, suna wucesu. Suna isowa kaduna straight bariki ya wuce domin pending aikin da yake da a office.

" welcome sir " Faruq ya sara mishi.

Jinjina kanshi yayi ba tare da ya amsa mishi ba yayi hanyar da zata sada shi da wajen field in. Ozo ne tareda su Faruq suka mara mishi baya, kowanen su rike da gun a hannu su.

Isarsu wajen field in duk sojojin da sukayi layi, wajen su hamsin duk cikin khaki, suka fara sara mishi. Jinjina musu kai yayi, a lokacin ne kuma captain in su mai suna Captain Ammar Uthman ya bar inda ya tsaya a gaban sojojin ya matso Kusa da Omar yana mai sara mishi.

" good morning  sir ". Ammar ya gaida shi.

" morning, how is the training going so far " Omar yayi tambayar da  muryashin nan dai mai taushi amma kuma kwata kwata ba alalum wasa a fuskar shi, domin ko a hade take tamkar Wanda bai taba dariya ba.

Duk sojojin wajen kallonsa suke, domin kamar wani celebrity yake a wajen su, daga Wanda suka sanshi har Wanda yaune suka fara ganin shi even though suna yawan jin ana ambatan sunan shi. Duk kuma ya burge su domin suna ganin kokarin da yake yi wa yan division in shi. They all admire him.

" it's going well"  Ammar ya fada tareda yiwa sojojin alamun da su fara rehearsal. Tsayawa yayi yana kallo, inda yaga akwai wani mistake, ya gyara musu. Wannan kenan.

*****
Sakowa suke daga kan staircase. Dariya ne ke tashi a wajen. Daga gani labarin abin dariya Abida take ba ma Afra domin sai dariya suke turka. Sanye Abida ta ke a cikin wani red atampha exclusive peplum mai mermaid skirt, tayi irin daurin zahra buhari. Ita kuma Afra wata embellished exclusive ce brown colour, ita ma dinki peplum da straight skirt ne. Itama daurin zahra buhari tayi ta fito da jelar gashin ta data daure a ta keyanta.

Duk Sunyi kyau cikin simple makeup in da sukayi. Hanya parlor sukayi, suna tafiya suna raha, daman an dade ba'a hadu ba.  Mommy dake tareda Daddy a parlor jin maganar su ne yasata dagowa ta kalle su. MashaaAllah abinda ta furta kenan domin yaran nata ba dai kyau ba.

Suma su Afra turus sukayi ganin Wanda ke parlor, ita Afra wani kunya ne ta ji ya mamayeta ganin irin dariyan da suka, ita bata zaci Daddy na gidan ba. Gwanda gwanda in da Mommy ne ma ita kadai, domi ta saba da Mommy wace ta dan saba da domin dan zamanan da tayi har sun saba da ita, domin Afra dai daman tana da saurin sabo sai dai in bata ga fuska ba.

Ihu Abida ta sake tareda da gudu taje tayi hugging in Daddyn. Dariya daddy yayi yana hugging inta baya. Abin sai ya ba Afra sha'awa, tana mai tuno da iyayenta domin itama haka take wa iyayenta.

" amma ke kam anyi girman kawai. Afra shigo ciki kin tsaya a bakin kofa " Mommy tace wa Abida tareda maida kallonta kan Afra.

Shigowa Afra tayi ta zauna a kasa Kusa da inda Mommy ke zaune.

 AFRA Where stories live. Discover now