💖💫RUDANI💖💫 2

359 64 9
                                    



This page is dedicated to Fatimah, my one and only Teeeee🌚🦋

Wata classy babe ce ta shigo ta samu waje ta hakimce, glasses in dake idonta ta cire sannan ta dau waya ta shiga dannawa, fara ce sol dan kuwa da ganinta kaga Shuwa, tanada kyau so Masha'Allah komai yaji, ganin takai 2mins wajen ba wanda ya fito yasa ta mike saidai kafin ta haura sama taga Aameer "Morning Aameer" ta fada sannan ta karasa ta basa hanu alaman su gaisa "Ahh Teemerh kece anan, Morning" ya amsa sannan ya bata hanu suka gaisa kaman yanda ta bukata "Bai dawo ba?" Ta tambaya
"Eh sunyi landing, yanzu shi zanje daukowa ae" ya fada yana mey cigaba da tafiya "Toh muje tare mana"
"Kije ina?" Ashphert ta amsa ta daga balcony tana kokarin saukowa tana gyara veil in ta "Ashphert morning" Teemerh ta fada tana wani shu'umin murmushi "Kinga let's get going kar kumun tashin hankali anan" Aameer ya fada sannan yayi waje ya barsu ah wajen "Da kin kwantar da hankalin ki very soon za.." Teemerh bata karasa ba Ashphert tayi waje dan sam bata shiri da yarinyan, dariya Teemerh tayi sannan ta bisu "Aameer tun wuri kar ka dau yarinyan nan dan ba daidaitawa zamuyi ba" Ashphert ta fada ganin Teemerh na karasowa wajen su "Yarinya tana sanku amma sam kun hating nata" ya fada sannan ya bude mota ya shiga, shiga Ashphert tayi dan tasan dole zai dauki Teemerh, saida kuwa ya dauketan

Wani charming handsome nagani ya fito, zan iya rantsewa ba indigene na Nigeria bane saboda tsantsar kyau'n da Allah ya masa, tsayawa fadan kyanshi ma bata lokaci ne saboda shi'in real definition of dream boy ne, saukowa yayi sannan ya fara duba motacin dake gabanshi koh zaiga sunan dake jikin plate no. na motan saidai duk babu na Aameer a ciki, kasancewan yasan Aameer ne zaizo daukan shi yasa yake dubawa dan koh sama da kasa zasu hade bazai dauki motan gida ba, saboda ba'a fiye ajiye Jeep cars gidan ba, shi kuma hankalin sa bayi kan kowani mota sai Jeep, waje ya samu ya zauna saida motochi suka fara watse wa kaman ance ya dago kai yaga Aameer a gabanshi "Doctor I've been waiting" cewan Aameer "Koh ni ka barni ina jira ba, c'mon zuwa da wuri ya gagari mutum" ya fada yana wani bata rai "Daka samu nazo daukan naka ne zaka fada mun magana?"
"Oh Barrister namu koh nace Young Jugde mai ya kawo wannan magana kuma?" Ya fada still ba wani murmushin kirki fuskan sa "Toh nasani? ae kai ba'a maka mutunci shiyasa"
"Whatever muje dai"
"Anwaarrrrr" Teemerh ta fada sannan ta karaso da sauri tayi hugging nasa, wani kallon banza Ashphert dake tsaye gefe ta bita dashi "Missed you" tayi saurin fada, shi ah duniya ya rasa gane wata irin yarinya ce Teemerh amma yasan duk abunda takeyi it's for the good "Missed you too" ya fada sannan yayi breaking hug in "Ke kuma fa?" Ya tambayi Ashphert ganin ta maqale ah gefe kaman zatayi kuka, shiru ta masa batace komai ba sai dirty look da take watsa wa Teemerh, gane hakan da yayi yasa shi sakin murmushi baiyi niyya ba, hakan ya kara fito da kyan da Allah ya masa "C'mon Ashphert don't be silly..." bai karasa ba ta tsaidashi "Muje koh" ta kalli Aameer ta fada, Teemerh kuwa na gefe sai murmushi takeyi dan bata fiye san zaman lafiya ba, wani daga cikin masu aiki a airport suka samu ya dauki suitcase nashi zuwa mota "Wait guys" Ashphert tayi saurin tsaidasu ganin sun kusa shiga mota "What again?" Anwaar ya amsa "Is that not Ilhaam and Munnirah beside her?" Ta fada tana musu nuni da wajen dasu Ilhaam ke zaune, tunda Anwaar ya daga ido ya kalli wajen sau daya ya tabbatar itace bai sake ba, Aameer ne yace "Ilhaam ce mana, amma yaushe flight nasu ya sauka?" Ya fada sannan suka karasa wajen shida Ashphert suka bar Anwaar da Teemerh tsaye, ganin haka Anwaar ya shige mota abunsa "Ilhaam" ya kira sunanta calmly, koh ba'a fada ba tasan waye saboda kamshin turaren sa kawai ya isar da sakon, tare suka dago ita da Munnirah nan Munnirah tayi saurin cewa "Ina kwana Yaa Aameer?"
"Lafiya" ya amsa "Yaushe kukayi landing?" Ashphert ta tambayi Ilhaam "Dazu fa" ta fada sannan ta mike tayi hugging Ashphert, hugging nata back tayi kafin suka breaking hug in "Ina kwana?" Ta gaishe da Aameer, maimakon ya amsa sai cewa yayi "Muje koh?"
"Muje ina? daman ni kazo dauka?"
"No I came to pick on Anwaar bansan kun sauka ba"
"Toh ku tafi kawae za'a zo daukana"
"Aameer wai fa kuna batawa Anwaar lokaci" Teemerh ta fada tana kallon Ilhaam da tunda ta mata kallo daya ta kauda kai "Ilhaam kun dawo lafiya?" Teemerh ta fada saboda ita ta kurba munafurci "Lafiya qlau" Ilhaam ta amsa, ciro key Aameer yayi ya mikawa Teemerh "Aameer me zanyi dashi?"
"Baya ce na bata masa lokaci ba? he should take you home" kin karba tayi tace "ni baza'ayi haka dani ba" ta fada sannan ta juya dama abunda ya kawota daban ne "Aameer don't worry, driver'n Ummi wil be here"
"You sure?" Ya tambaye ta "Yea sure"
"Toh mu tafi" ya fadawa Ashphert
"No kuje zan taho tare da Ilhaam"
"Okay" kadai yace yayi gaba "Toh nikam bari na bisu" Munnirah ta mike tabi bayan Aameer nan Ashphert da Ilhaam suka zauna "Wai haka zaki zauna kina kallon su?" Ashphert ta tambayi Ilhaam "Mai kikeso nayi Ash?"
"I can't say amma abun nata yayi yawa"
"Nifa banda damuwa da ita, tashi muje gashi ya karaso" Ilhaam ta mike ganin Driver'n Ummi "Amma gidan Ummi zamu koh?" Ashphert ta tambaya
"Dole fa, mai zanje na musu can"
"Amma Ummi bata dawo ba, koh jiya da mukaje Mami kadai muka samu"
"Toh muje wajen Mamin mana" suna shiga Ilhaam tace masa wajen Mami nan ya shaida mata Mami jiya tayi tafiya, ba yanda suka iya akayi gidan Baa dasu. Tafiyan 53mins ne ya kaisu gidan nasu dake Maitama kasancewar daga Nnamdi Azikiwe International Airport zuwa cikin Abuja akwae nisa, koh da sukaje already su Aameer sun dade da isa abunsu. Ah palo ta same su duka, Xeenerh na ganinsu ta mike da sauri taje huggin nata "Ahh 'yar uwata kuma qawata, indai kyau ne ba wanda zai nuna miki" Xeenerh ta fada saboda neman magana ganin Teemerh wajen, janta zuwa main palo tayi saidai tana zama Anwaar ya tashi, ganin haka ma Teemerh ta tashi zata bisa "Amma anyi asaran haihuwa, nifa namiji bai bini ba banga dalilin da zaisa na bisa ba" Ashphert tayi mocking Teemerh
"Worth it, nah?" Teemerh ta tambaye ta sannan ta kashe idon dayasha lashes tayi sama, tashi Ilhaam tayi dan in ta cigaba da zama ah wajen kuka zatayi, tana shiga daki tayi wanka

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now