💖💫RUDANI💖💫 25

185 36 18
                                    



Borno, Maiduguri.

Abbaas ne zaune shida wata, da gani itace Asmah matan da Najeeb ya aura, sai Bilqis dake gefe rike da littafi, shi yake bata labarin tana dan murmushi dai haka "So marriage plans?" Ta tambayesa dan kuwa duk cikin zancen nasa bey ambato mata aure ba "Yea for sure akwae randa zanyi aure but haryanzu bansamu wacce ta kwanta mun ah rai bafa" ya bata amsa ah takaice "Toh Allah ya kawo ta gari" da Amiin ya amsa nan yaga Leemerh ta sauko ita kadai sai kumbura takeyi "Ke kuma fa?" Asma'u ta tambayeta dan kuwa bakinta bayi gani yayi shiru "Ita wai wannan tanada wani damuwan da ya wuce na wancan Barrister'n ne?" Bilqis tayi saurin fada "Nifa indai haka ne, toh ina rokon Allah karya samun san wani ah raina" ta sake fada "Toh ke banda abunki Leemerh, ke da bakin ki kika ce mun yayi aure right?" Asmah ta tambaye ta "Eh yayi, kuma ni abunda nafi damuwa dashi is that ban ganin interviews nasa these days" Leemerh ta amsa ah nitse, Abbas dai kallonta kawai yakeyi bece komai ba dan bayison shirita wani lokacin "Toh wlh Allah yasa Yaa Najeeb yaji labarin wannan zance dan kuwa kin kade, banda shirme wai mutumin da bey san dakai ba kake wannan haukan akan sa" Bilqis ta fada cike da takaici "Wai hayaniyan mey nake ji ne haka?" Mum da shigowan ta kenan ta tambaya "Erm.. dama wai Leemerh kesan zama Barrister shine take bin cases na wani Barrister, wai Aameer Albaaz, Mum kin sanshi ma fa, that one da Yaa Najeeb ke kawai magazines nasa" Bilqis ta hade ma Mummy karya dan kuwa tasan inta ji labarin haukan da Leemerh keyi akan Aameer zata mata ba dadi, wai dan ma ah haka Mum nada sanyi "Kai Haleemah dai akwae shiririta, Toh shi kuma karatun naki kiyi yaya dashi?" Shiru tayi tana tunanin ajiye duk wani karatu ta sake sabo, kuma ita yanzu ta yanke shawaran Law zata karanta "No Mum, dama akwai particular case in da nakeso nasan ina ya samu evidence nasa" Leemerh ma tayi karya "Kuma sai aka ce miki bude sirrin su suke koh?" Abbas da sai yanzu yayi magana ya fada da takaici "Toh kadai barmun Haleemah da shirme, kwana ki kuwa ae na gansa nan Maiduguri, gashi da hankali kuwa" Mum ta fada harda dan murmushi "Mum, kinga Aameerrrrr?" Leemerh tayi saurin tambaya jin abunda Mum tace har tana kokarin fadi wajen karasowa "Ke da lafiyan ki kuwa?" Mum ta tambaya da mamaki ganin abunda Leemerh tayi, itama dai Bilqis jira takeyi taji ah ina Mum ta gansa "Im fine Mum, dan Allah ah ina kika gansa?" Ta sake tambaya, eager to know "Ah nan neighbor ne fa, gidan Ammaah, he is one of her grandsons" Mummy ta b'ata amsa sannan ta wuce abunta "Shikenan" abunda Leemerh ta furta kenan sannan ta bage musu a k'asa "So yana zuwa nan kenan" Asmah ta tambaya "Toh suna zuwan kenan ae tunda ta gansa, girl just chill zaki gansa someday" Abbas ya fada sannan ya mike "Allah indai ban zama Barrister ba ae fa ban huce takaici ba, like in gansa ne? So calm and gentle yanda yake abubuwa" Leemerh ke ba Asmah labari, kallonta Asmah tayi kawae dan batada kirki sosai gani take duk cikin su ba sa'anta shiyasa bata tab'a tad'i dasu saidai Abbas, yanzu ma ganin ya tashi ne tayi shiru "Just like a sparkling star" Leemerh ta fada a nitse "Toh kuwa kin samu aiki" Asma'u ta fada sannan ta tashi tayi sama "Haleemah kinsan dai already da karatun da kike koh?" Billy ta tuna mata "Toh ke kinga ina miki maganan komawa makaranta ne? Ae karatu ya kare sabo zan fara" kallonta Bilqis kawae tayi without saying a word

                   Abuja.

6:45 am ne amma still tana kwance dan bata sa ran tashi bama, hasken ranan daya haska idonta ne ya sata bude idon ah hankali, hanu tasa daga kan nightstand ta dau sleeping mask nata sannan ta juya ta sake gyara kwanciya abunta, kaman ta tuna da wani abu kuma ta tashi da sauri ta zauna, sleeping mask in ta cire ta jefa a gefe abunta, dan bata rai tayi kafin ta mike ta cire cute cartoon nightgown in da take yawo a ciki, towel ta dauka tayi toilet, bada jimawa ba sai gata cikin wani pink bathrobe, alamu dai wanka tayi, mai ta shafa da sauran abubuwa sannan ta feshe turare ta shirya tsaf cikin blouse da skirt na atampa sannan tayi k'asa, ganin ba Ummi yasa tayi dakinta, tana zaune rike da Qur'ani tana karanta shi ah nitse, samun waje Ilhaam tayi ta zauna tanajin yanda Ummi ke karatu ya burgeta sosai, tasan matan akwae addini, Ummi nayi itama tanayi ah hankali har saida ta karasa karanta Suratul Maryam tunda dama a shafin karshe take, kafin ta rufe cike da nutsuwa ta juyo "Kin tashi?" Ummi ta tambaye ta "Eh dama-" sai kuma tayi shiru "Dama mey?" Ummi ta tambaya tana bata full attention nata "Ummi dama nace tunda dama Baa ne ya hana karatun kuma yanzu bayi nan basai ah cigaba ba?" Ta fada kanta ah k'asa dan kuwa zama ita kadai ba karamin damunta yakeyi ba, dan kallonta Ummi tayi saidai bata ce komai ba hakan yasa Ilhaam dagowa ta kalleta "Kiyi haquri in na fadi abunda ba dai-dai ba" ta fada cikin sanyin murya "Baki fadi abunda ba dai-dai ba Aya, amma ke baza kiyi tunanin yin aure kaman yanda shi Baa ke so ba?" Shiru Ilhaam tayi kawai batace komai ba "Akwae wanda kikeso ne?" Taji Ummi ta jeho mata tamabya batayi tunani ba, da sauri ta kalleta sai kuma ta fara girgiza kai "Idan har kin tabbatar ba wani ah ranki, inaso ki bani dama na sama miki miji wanda zai kula mun dake sannan kiyi karatun naki cikin mutunci" kallonta kawae Ilhaam takeyi ta kasa ce komai dan batada plan na aure yanzu kam "Ina tamabyan ki kin mun shiru" Ummi ta dawo da ita daga duniyan tunanin daya tafi "Ba kowa" ta amsa ah nitse "Wai mey ke damunki ne?" Ummi ta tambaya ganin yanayin ta "Bakomai Ummi" ta fada murya na rawa kaman mey shirin kuka "Kinga kar kiyi kuka, koh auren ne bakiso?" Shiru Ilhaam tayi sai chan tace "Inaso zanje wajen Aunty Aisha" ta fada still kanta ah k'asa "Ki bari zuwa gobe, yau zaki taimakawa su Suhaila ah kitchen" dan kallonta Ilhaam tayi hakan yasa tace "Anwaar zai dawo, nace ya dawo dan na gaji da zaman shi chan ba aure" hawayen da take kokarin boyewa ne ya sauko dan batasan Anwaar kusa da ita, gashi yanzu Ummi ta dawo dashi, saurin tashi tayi gudun kar Ummi tayi tunanin wani abu ta fice ah dakin, wanke fuska tayi sannan ta wuce dinning area, ah nitse ta fara cin abinci harta gama, bayan ta gama ta samu su Suhaila ah kitchen kaman yanda Ummi tace saidai ta kasa yin abun kirki, ita ke zuwa tana jerawa akan dinning har suka kammala, bayan sun gama ta wuce daki danyin sallah'n Zuhr




💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now